WATA BAKWAI CHAPTER 5

WATA BAKWAI CHAPTER 5
WATA BAKWAI CHAPTER 5 Da tunani barkatai a zuciyarshi harya tashi da safe. Tun wajen karfe bakwai daya koma bacci bai tashi ba sai yanzun nan. Yana duba agogo har sha daya tayi. Dakyar ya rabu da katifar yaje yai wanka. Ya shirya cikin wani kaya na karan miski brown. Yayi kyau matuka. Har ya wuce zaiyi dining room din ya tuna da yar mutane da take karkashin kulawar sa bata da lafiya fa. Yaja wani gajeran tsaki sam sam baya son matsala a rayuwar shi. Bangaren husna ya wuce yaga ko taji sauki. Dan bai niyyar daga tafiyar shi ba saboda ita. Yanda aka lika masa aurenta haka aka lika masa tafiya abuja da ita. * Husna kam dayake ba sallah take ba. Tunda ta tashi tai wanka ta shirya cikin wata doguwar riga simple. Suka sha wayarsu da ammar harya shirya zuwa aiki. Dan ya ce mata ya samu aiki a wani gidan mai. Suna gama wayar ta kwanta shiru abinda ya faru tsakaninta da prince ishaq yana mata yawo. Sai taji kaman tanajin kam shi har yanzun kan gadonta. Taja tsaki. Bakin natacce …