WATA BAKWAI CHAPTCHAPTER 15

WATA BAKWAI CHAPTCHAPTER 15
WATA BAKWAI CHAPTER 15 A hankali komai yake tafiyar musu. Sauqi kam ya samu wajen nas watanshi biyu kenan cif a asibiti. Dan harya soma musu korafin ya gaji shi kam. Saidai likitanshi yace ba zasu sallame shi ba sai sun tabbatar internal injury din daya samu a kanshi bazai bada wata matsala ba. * Prince ishaq da husna kam da duk ranakun da suke wucewa wani irin shakuwa me karfi ce take kara shiga tsakaninsu. Yanzun kam sai tai kwanaki ma bata tuna da wani ammar ba. Zasu kwana waje daya da prince ishaq. Dan tama saba da duk rikicinsa yanzun. Suje unguwa tare, wasu lokuttan in yasan zai fita ya jima saiya dauketa ya sauketa asibiti wajen Nas suyita hirarsu in ya dawo ya biya ya dauketa su koma gida. * Yauma kaman kullum tana zaune falo tana kallon mbc 3 ya fito jikinshi sanye da farar shadda. Da kyanshi da shaddar suka shigar mata ido. Murmushi tai. Ya daga mata gira hadi da fadin Say it hussy” Ta kalle shi cikin ido tace “mezan fada?” Ya sake fadada murmushinsa. “Kice…