TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 1

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 1
TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 1 Kashim Ibrahim library (KIL) babban ɗakin karatu ne cikin Jami’ar Ahmadu Bello da ke birnin Zariya. Kamar kullum yauma ɗakin karatun cike ya ke fal da ɗalibai maza da mata kasancewar lokacin jarabawar zango na farko na shekarar (first semester) ya matso. Ɓangaren da ta san ya fi kowanne rashin hayaniya ta samu ta raɓe. Sanye ta ke cikin shuɗin hijab dogo har kasa. Sam ba ta damu da ta shafa ko hoda ba bare a kai ga jambaki, irin bakaken matan nan ne da su ka amsa sunan “black beauty”. Duk yadda ta so ta mayar da hankali ta gane karatun da ke gaban ta, hakan ya gagara ba dan komai ba sai dan zaman da wani ya yi kusa da ita. Zuwan ta be fi da awa daya ba sai gashi shi ma ya zo, kuma ya rasa in da zai zauna sai kusa da ita duk girman library din, mitar da ta ke yi cikin ran ta kenan tana mai jan tsaki ɗaya na bi ma ɗaya. Tana cikin wannan halin ne ta ji kamar an gogi kafar ta wanda hakan ya sa ta saurin janye kafar da sauri, a fusace cike da alama…