SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 21

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 21
SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 21 Falon suka wuce, Iyayanshi zaune suke kan kujera shi kuma yana kasa yana wasa da yatsunshi, gabanshi se dukan uku uku yakeyi+ Dad dinshine ya kalleshi yace” Mansur meke tafe dakai? Fadamun da sauri dant Zan fitane M.T ne ya gyara zama yace dad Dan Allah neman alfarma nakeyi a wajenku, Ku amince na aura Nazeefa inasonta! Dad dinshi Ya cire Glass din dake fuskarshi ya karemai kallo, tuni murmushin dake fuskarshi ya gushe, yace Ashe bakada hankali? What are you saying? Yarinyar data gama bin gidajen mutane zaka cemun ita zaka aura? Sam bazaiyuwaba! Karma in Kara jin wannan maganar a bakinka, Mansur ka sake tinani! amma banace akwai yarinyar da Zan hadaka da itaba? Kenan Allah kadai yasan abun da kuka aikata lokacin da ka kawota gidan nan! Zaka zo ka dameni kace wani zaka aureta ka shiga taitayinka Mansur turaki tsabagen rikicewa kasa motsi yayi, Dan kallon abun yake kamar a film? Mum dinshi kuma na zaune tana ba Alhaji hakuri Alhaji yace Sam bazaiyuba…