YAR MAKIYAYA CHAPTER 17 YAR MAKIYAYA CHAPTER 17 Dare yayi saboda haka Habeeb ya koma chan gida tare da umma Hauwa ya bar Suraj tare da Layla, ko da suka iso gida shigowar su living room duk suka yi turus ganin Mom da Dad zaune, as usual Dad yana zaune k’afa d’aya kan d’aya yana kallon news yayinda mom ke zaune tana danna waya. A tare suka d’ago suka aza idanuwan su kan Habeeb ita kuwa Umma Hauwa gaisuwa ta kwasa tayi ciki, shima Habeeb d’in k’arisa wa yayi inda suke ya gaida su cikin ladabi da rusuna wa kuma cikin sakin fuska suka amsa kafin Dad ya cire glass d’in shi yace “Habeeb my son whare is Suraj Ko ba tare kuka fita ba? Tun d’azu muka iso har dare yayi babu kowa sauran ma’aikatan ma basu san da fitan ku ba”. Habeeb cike da mamaki yace “daman bai sanar da ku ba? Amma naji Kamar d’azu yana waya da ke Mom”. Kai mom ta jinjina kafin tace “Bai fad’i komai ba kawai mun yi da shi a kan muna hanya, me yafaru Habeeb akwai wani abu ne?” Ta tambaya tana mai ajiye wayar ta a kan side table. “Mom abu…