YAR MAKIYAYA CHAPTER 16

YAR MAKIYAYA CHAPTER 16
YAR MAKIYAYA CHAPTER 16 Cikin nutsuwa yake tuk’i idanuwan sa na kan titi yana ganin yanayin hark’allan mutane wasu su bashi dariya wasu kuma su bashi haushi. Wayar sa ce tayi k’ara don haka ya yi parking a gefe sannan ya d’aga wayar + “Habeeb bro! I can see you are already missing me, ai na fad’a maka you can’t do without me!” Suraj ya fad’a cikin yanayin zolaya. Daga d’ayan b’angaren Habeeb yace “Hah! As if kai ma zaka iya rayuwa ba ni! Anyways ina gari fa yanzun haka amma ina da wasu y’an ayyukan da zan yi , but gaskiya you will pick me up when am done coz ba mota a waje na”. “Ok toh ba matsala yanzun haka ina kan hanya I’ll take care of some business ,let me know in ka gama sai in d’auko ka”. Daga nan suka yi sallama kowanne ya ajiye waya Suraj ya tada mota yaci gaba da tuk’i….. Hirar su suke mai dad’i ita da umma hauwa k’ararrawar k’ofa ta yi k’ara hakan ya sa Layla ta mik’e cikin sauri ta nufi k’ofa a zaton ta Suraj ne ya dawo amma wanda idanuwan ta suka nuna mata mutum ne…