WATA FUSKA CHAPTER 6
WATA FUSKA CHAPTER 6 Sosai yasha mamakin yarinyar to ita kuwa menene da riqa ninke wannan fuskar ta d’aura *Wata Fuskar* akan kyakyawar fuska irin wannan? Dukda ya kula akwai makeup a kan fuskar amma ya tabbatar da cewar itace tawa makeup d’in kyau bawai makeup d’inne ya mata kyau ba, tana sanye da rantsattsen lace maroon color ta yafa mayafi fari dayake ratsin fari ne ajikin lace din, mayafinta asaman kafad’unta duka biyu ta zagoshi be sauka ba bare ya rufe mata jikinta wannan ya sanya duk a takure take, yakuma kula sosai da hakan murmushi ya sakarwa kanshi ya kula ya shagala sosai da kallon Nancy yana qoqarin kawarda dubanshi gareta ta juya masa baya nan take doguwar sumar kanta da aka linke kusan hudu aka mata daurin zara buhari ya bayyana, kafe idanshi yae akan sumar kanta ko shakka bayayi yanayin Nancy ya masa shi duk wannan qaton qugun nata be dameshi ba sam hankalinsa yatafine akan murmushin ta me qayatarwa daya tabbatar murmushin ne yake sada zuciyar sa da tata wuri…