WATA FUSKA CHAPTER 3

WATA FUSKA CHAPTER 3
WATA FUSKA CHAPTER 3 Zaman makarantar haka ya kasance cikeda wata iriyar shaquwa tsananin maheer damuka islam, kullum suna tare kokuma idan basa tare to kuwa suna nan maqale a waya amma Maheer betab’a furtawa Islam kalmar so ba….yayinda Nancy ke matuqar shan wahalar soyayyar datake wa Maheer wacce ta tabbatar koda babu Islam baze so er qauye irin taba, kullum setayi kukan rashin sa da soyayyar sa datake neman illatar da ita, yauma kamar kullum tana zaune yana zuba lecture yana musu sallama akan se sun dawo hutu tunda sun kammala exams dinsu yau, ji tae wani zazzafan zazzab’i ya mata dirar mikiya, koyaya zata iya jure rashin Maheer na watanni uku? Koyaya zataji bayan rabuwar da zasuyi? Ganinsa kawai yakan saukar mata da nutsuwa sosai azuciyarta mesa zuciyarta da gangar jiknta basu mata adalci ba akan soyayyar Maheer? Ina ita ina shi? Ko bayan talauci batada wani gata a duniyar nan se Allah…..haka aka watse kowa ya fashe hannunta Islam taja1 “Muje office d’in sir maheer yace n…