WATA FUSKA CHAPTER 2 WATA FUSKA CHAPTER 2 A qofar office d’insa ta tsaya tana danna er qaramar wayar ta ta android qirar kamfanin techno bugu na y2 er qaramar alhakin data jima da fita yayi, wannan ya sanya sam batasan da zuwan suba har suka qaraso wurin, gayan murya Dr. Shema yae yayinda Maheer ya qurawa wayar dake hannunta ido sosai takesha maintenance wannan ya sanya sam bazakace tsohuwar bugu bace,a ninke take da leda me kauri duk jikinta gashi an had’ata da screen protector wannan wane irin maleji ne da tattali d’an tsiya? Sam wannan be dace mace ba koda yake wataqil laifin matsiyacin mijinta ne banda haka wannan tun yaushe ta fita a yayi? Gyaran muryanshi yae dan kanshi ya saisaita nutsuwar sa yabi bayan Dr. Shema ganin harya qure cikin office d’in…..da sallamar sa shima ya shiga yayinda Hafsat ta mara masa baya tana me duqar da kanta wannan sabon malamin nasu yana santa gwiwowinta yin sanyi matuqa, wannan idan nasa suna neman razanar da ita gashi da kallo sekace maye, seya qura mata wannan gwal…