WATA BAKWAI CHAPTER 4
WATA BAKWAI CHAPTER 4 Yaji shigowarta sarai ya ci gaba da game dinsa. Ya kuma ki abinda tace. Dame take ji da ba zata dauke shi da muhimmanci ba.+ Dan shi bata gabansa bashi zai bata damar jin hakan game dasji ba. Ba ai macen da zata nuna masa iyakarsa ba. Ko da huddy ce kuwa. Dole ta bashi girma ko bata so. In tana son magana dashi ta zagayo ta kalli fuskarsa. Husna kamar zata saka ihu don takaici. “Magana fa nake maka kazo kasa a budemin gate.” Ta sake fadi cikin alamar qulewa. System dinsa ya rufe ya miqe yana shirin nufar dakinsa…..tasha gabansa shade din idonta ta cire ta kalle shi cikin fuska sosai. Tunda yake bai taba ganin kiyayya irin wadda yagani a cikin idanuwanta ba. “Don na tambayeka abu zaka nemi wulaqantani?” Da mamaki sosai yake kallonta. A. Lokaci daya kuma yana tambayar kanshi akan me zata aure shi. Ta tsane shi!!! Yagani cikin idanuwanta bata son shi. Ko da zaka auri mutum dan kudin shi da kalar tsanar datai masa kam zata hakura. Sai dai duk wannan bai …