WATA BAKWAI CHAPTER 3
WATA BAKWAI CHAPTER 3 rince ishaq kam hannunta yabi da kallo da wani yanayi a fuskar shi.+ Gani yai da gaske takeyi cikin alamar tsoro yace mata “ke meya hakan wai?” Ta ma kasa magana kawai wayyoo mami take kira ta dafe ciki da hannu daya. Dayan kuma ya rike da na prince ishaq dam. Baya son ganin wani cikin yanayi. Hakan na tuna mishi abubuwa da yawa. Tsugunnawa yai Allah ya zuba masa tausayi musamman ma mata. Cikin damuwa yace “Are you okay? wai meke damunki?” Daqyar tace masa “cikina…” Wani abu da ya dade bai motsa ba a jikinsa yaji. Koma menene yafi karfin zuciyarshi. Baisan lokacin daya kai hannun shi kan cikinta ba. “Dai-dai ina yake ciwo? Murdawa yake? Zafi?” Kaman bata masan yanayi ba. Pillow din kujera ya dauko ya ajiye kasa ya samu ya zame hannunshi daga nata. Kamata yai ya kwantar. “Stay right here” ya fada ya mike da gudu har kafarshi ta taka step din farko na benen zai hau sama kawai kamar wanda aka dokawa guduma akai. Ya tuna da alkawarin dayai ma kanshi…