WATA BAKWAI CHAPTER 1

WATA BAKWAI CHAPTER 1
WATA BAKWAI CHAPTER 1 Tunda abokansa suka rakoshi suka gama surutunsu da kawayen amarya bai ce uffan ba. + Asalima bazai iya maimaita magana daya da suka fada ba dan hankalinsa ba akansu yake ba. Kallan yarinyar da take zaune kan gadon ya keyi baima san me zai soma fada mata ba.Ko kalar fuskarta bai sani ba tana zaune kan gadon lullube da mayafin da bashi da niyyar bude mata. A hankali kaman mai koyon magana yace mata. “Sannunki” Tafi mintina biyar a zatansa ma bataji ba sannan cikin rawar murya tace masa. “Nagode” Hannunta tasa tana sake gyara mayafinta dai-dai lokacin da idanuwansa suka sauka kan hannayen nata da suka sha kunshi. A gefe guda kuma zuciyarsa ta dauke shi ta watsa shi wani lokaci can baya. *** *** Da gudunta ta karaso inda yake. “Yayana kaga kunshina yayi kyau?” ta fadi da murmushi a fuskarta. Shima murmushin yai mata yana fadin. “Kai kai gaskiya baiyi kyau ba” Fito masa da idanuwanta tayi lokaci daya ta tabare fuska tana shirin yin kuka. Yana…