YAREEMA KHALEED CHAPTER 9 THEND KARSHE

YAREEMA KHALEED CHAPTER 9 THEND KARSHE
YAREEMA KHALEED CHAPTER 9 THEND KARSHE *__________?* yanda ya tsamke ta ajikin sa tsam tini ta kuma yunƙura wa domin ƙwace wa daga jikin sa sakamakon abinda taji ya tsarga mata. + “uhm-uhm ni ka rabu dani dan Allah”. ƙaramin bakin ta ya kafe da idanun sa da suka gama sauya yanayi saboda sha’awa. “ki faɗi mani mi zan yi ki huce fishin da kike dani wanda yake azabtar dani”. “to ni ban yi niyya ba sai ka rabu dani, ni dan Allah ma ka sake ni na huta….”. ɓacin rai ne ya bayyana a fuskar sa saboda jin furucin ta, yatsan sa ya ɗora saman laɓɓan ta ya danne, “kar na sake jin kin mani wannan mummunan furucin idan ba haka ba ranki zai ɓaci”. “to baka na da wata matar ba miye naka idan ka rabu dani”. tai maganar tana shagwaɓar da fuska. ƙaramar dariya yayi, ɗayan hannun sa ya ɗauke daga bayan ta ya dawo dashi fuskar ta ya ɗago, cikin ƙwayar idon ya kafe da ido yana kallo, ita ɗin ma shi take kallo da wani irin yana yi, jin baza ta iya jure ma kallon nasa ba ya sanya ta saurin sadda idanuwan ta ƙasa tana ka…