Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

YAREEMA KHALEED CHAPTER 9 THEND KARSHE

YAREEMA KHALEED






CHAPTER 9 THEND KARSHE








*__________?* yanda ya tsamke ta ajikin sa tsam tini ta kuma yunΖ™ura wa domin Ζ™wace wa daga jikin sa sakamakon abinda taji ya tsarga mata.
+

“uhm-uhm ni ka rabu dani dan Allah”.

Ζ™aramin bakin ta ya kafe da idanun sa da suka gama sauya yanayi saboda sha’awa.

“ki faΙ—i mani mi zan yi ki huce fishin da kike dani wanda yake azabtar dani”.

“to ni ban yi niyya ba sai ka rabu dani, ni dan Allah ma ka sake ni na huta….”.

Ι“acin rai ne ya bayyana a fuskar sa saboda jin furucin ta, yatsan sa ya Ι—ora saman laΙ“Ι“an ta ya danne,

“kar na sake jin kin mani wannan mummunan furucin idan ba haka ba ranki zai Ι“aci”.

“to baka na da wata matar ba miye naka idan ka rabu dani”.

tai maganar tana shagwaΙ“ar da fuska.

Ζ™aramar dariya yayi, Ι—ayan hannun sa ya Ι—auke daga bayan ta ya dawo dashi fuskar ta ya Ι—ago, cikin Ζ™wayar idon ya kafe da ido yana kallo, ita Ι—in ma shi take kallo da wani irin yana yi, jin baza ta iya jure ma kallon nasa ba ya sanya ta saurin sadda idanuwan ta Ζ™asa tana kallon Ζ™irjin sa.

sakamakon hango kishin sa Ζ™arara cikin idanuwan ta da kuma fuskar ta da yake a shimefiΙ—e yasa shi sakin murmushin leΙ“e wanda ya fitar da sauti.

kanta ya kwatar bisa faffaΙ—an Ζ™irjin sa yana shafa gashin kan ta.

ta gefen kunnen ta ya raΙ—a mata, “mi yasa kike zaluntar zuciyar ki akan haramta mata abinda take so take kishin sa”.

“ni ba kishin ka nike ba, kawai dai na faΙ—i maka ne ka rabu dani ka koma can wurin matar ka ku Ζ™ara ta”.

“ni banda wata mata sama dake, ke Ι—aya nasan zuciya ta na so na Ζ™auna, kece kawai mai maΖ™ullin zuciya ta”.

ya Ι—ago kanta tare da mata nuni da saitin zuciyar sa yace, “kinga nan, mallakin ki ne ke Ι—aya”. sannan ya mata nuni dashi kan sa yace, “ni kai na naki ne, ke Ι—aya kike da wannan jikin ta ko’ina, ruwan ki ki bari kuyi shairing da wata ruwan ki ki hana wata kusantar shi”.

Ι—ago idanu tayi karab nata ya sauka cikin nasa,wani murmushi ya sakar mata haΙ—i da kashe mata ido guda, baki ta turo gaba tasa hannu ta bugi gefen Ζ™irjin sa tana tsuke fuska.

“ni ka daina mani wannan kallon”.

cikin sigar kwai-kwayon ta shima yace, “ni ka daina mani wannan kallon”.bata san lokacin da dariya ta subce mata ba dan yanda ya kwai-kwaye ta yasa ta dariya, wani sabon abune ya sake tsarga hudojin jikin sa sakamakon muskuta jikin ta data yi anasa, ido ya lumshe for second kana ya buΙ—e yana sake kallon asalin kyawun dake tattare da ita, manuniyar yatsan sa ya dora ta gefen dogon hancin ta yace, +

“Angel na ke kyakykyawa ce sose, haka duk lokacin da kika Ζ™awata wannan fuskar taki da dariya har sai kifi kyau kyau, plsss Ι—ago ki kalla cikin ido na ki sake min dariyan ki mai kyau kin ji”.

“taya zan maka dariya bayan ina fishi da kai ko ka manta ne”.

langwaΙ“ar da kansa yayi cikin shagwaΙ“a tamkar Ζ™aramin yaro yace, “umhmmmm wai har yanzu baki haΖ™ura ba?”.

kai ta Ι—aga masa alamun ehh, miΖ™ewa tayi a jikinsa tana gyara Ι—aurin towel Ι—in ta, zaune tayi kan gadon tana so ta miΖ™e taje ta Ι—auko kaya amma yanda ya kafe ta da mayatattun idanun sa yasa ta kasa.

“kaga ka tashi ka fitar mani a Ι—aki zan saka kaya, bazai yiwu nida Ι—aki na ba kazo ka hanani sukuni ba, kaje idan na dai na fushin da kai zan neme ka amma ba yanzu ba”.

ko motsawa bai yi baranta ne tasa ran zai fita sai ma kyawawan eyes Ι—in sa daya lumshe, Ζ™un-Ζ™uni take cikin ranta, ajiyar zuciya ta sauke ta yunΖ™ura zata miΖ™e taji ya kamo hannun ta ya dawo da ita ta zauna, zaune shima ya miΖ™e kusa da ita, murza tafin hannun ta ya shiga yi tare da ranΖ™wafo da kansa ya cusa cikin Ζ™irjin ta yana goga fuskar sa, gaba Ι—aya nema yake yasa jikin ta yin weak, dan haka da sauri tasa hannu ta Ι—auke kansa.

shagwaΙ“a da rigima ya hau yi mata kaman Ζ™aramin yaron dake neman nono, ganin ba sauraron sa za tayi ba ya sakko Ζ™asa yay kneeling a gaban ta.

in a cool and slow motion voice yace da ita, “plsss my Angel”.

da hannu biyu ta katse sa, “naji ya isa, oya hold your lips”.

magana zai yi tai nodding kan ta tace, “shikenan ashe baka so na haΖ™ura”.

saurin kama bakin sa yayi wanda hakan ya sa ta Ζ™yal-Ζ™yale da dariya sose, dariyar shima yaso yi dan akaran kansa ya bawa kansa dariya da yanda ya jawo laΙ“Ι“an sa gaba ya damΖ™e.

“kana yin dariya punishment Ι—in ka zai sauya better hold on”.

marai-rai ce fuska yayi yana “unhm”.

kunnen sa Ι—aya ta kama ta murΙ—a da zafi sannan tace, “aha take promise”.

kansa ya Ι—aga alamun ya Ι—auka.

lakuce masa hanci tayi tace, “magana zakai ba Ι—aga kai ba”.

da ido yay mata nunin kama baki data sashi.
binsa tayi da sexy eyes nata tana kallon sa kamin ita ma ta sakko zuwa gaban sa da yay kneeling.

hannayen sa ta sauke daga bakin nasa daya kama, haΙ—awa da nata tayi gam tace dashi,

“idan har kana so naci gaba da kasance wa matsayin matar ka to kayi min alΖ™awarin zaka daina mu’amalantar dukkanin abinda yake haramunne shan sa a musulunci, zaka kaucewa shan duk wani abu da yake sanya maye gudun saΙ“awa mahallicin ka, zaka nisan ci duk abinda zai illata lafiyar jikin ka”.”i promise you my lady, bazan sake ba, nima ba son kai na yasa nake sha ba, halin da aka jefa ni shi ya jawo na kasance cikin masu shan kayan maye domin na samu sukuni acikin zuciya ta na Ζ™azafin da akai mani, sai kuma azabar da kike mani na nuna cewan baki sona, amma na maki alΖ™awari daga shan Ι—azu da nayi ba zan kuma sha ba in har zaki barni na rayu cikin Ι—umin jikin ki”.

ya Ζ™arasa maganar ya matsowa tare dasa hannu ta weast Ι—in ta ya janyo ta zuwa jikin sa.
harar sa ta Ι—anyi tare da Ι—auke hannayen nasa tace, “to ai baka ce min ka yafe ma Ya Raihana ba”.

“ni bani ke da kaina ba, umarnin ki nake jira abar Ζ™aunata”.
ya faΙ—i yana shafa gefen fuskar ta da bayan hannunsa.

“ka zama mai yafiya domin Allah ma muna masa laifi kuma mu roΖ™e sa ya yafe mana, dan haka ka yafe mata har abada, kace ka yafe wa duk wani wanda ya zalunce ka a rayuwa, kayi masa fatan shiriya”.

” ehhh nayi , har wanda ma zasu yi min laifi nan gaba duka na yafe masu”.

yayi maganar yana Ζ™oΖ™arin cicciΙ“ar ta.

“a’a ka Ζ™yale ni mana ,kace so kake na haΖ™ura to na haΖ™ura komi ya wuce, ka barni naje nasa kaya kaga ko mai ban shafa kasa duk na bushe”.

bai saurare ta ba ya Ι—auke ta tana masa zillo, a kan gado ya kwantar da ita shima ya kwanta kusa da ita tare da Ι—ora kanta saman hannunsa.

karkato ta yayi sukai facing juna, Ζ™ayataccen murmushi ya sakar mata ya zagaye weast Ι—in ta da Ι—ayan hannun sa yana murza mazaunan ta.

“um-um ni ka bari”.
ta faΙ—i a shagwaΙ“e.

“hmm to na daina, oya tell me about my love”.

fari tayi da ido tare da juya Ζ™war idon ta, hira ta fara masa wadda ta sanya sa ya nutsu yana sauraron ta, tin daga farkon faΙ—awar ta tarkon son sa har kawo ya yau, ji tayi yay shiru kamar babu shi a wurin, ta Ι—ago ta dube sa, hankalin ta ne yaso tashi ganin yanda launin idon sa ya sauya yayi jawur, gashi yay mata Ζ™uri ko Ζ™iftawa bai yi ba.

hannu ta aza bisa kumatun sa tana shafawa tace, “Husby whats wrong?”.
ta faΙ—i da damuwa.

ajiyar zuciya ya sauke with pity face yace mata, “am so sorry for all my wrong deed to you”.

“no worry Husby nah, ya zama past”.
kansa ya gayaΙ—a tare da ce mata, “all thanks to you Angel”.

murmushi ta sakar masa tare dayi masa kiss a cheeks nasa
“nima tell me about my love”.

leΙ“ensa ya motsa ya lumshe idon sa tare da jan dogon numfashi ya sauke sannan ya buΙ—e idon sa ya ware su akan ta, hannun ta ya jawo ya Ι—ora a saitin zuciyar sa, yanda taji zuciyar na harbawa sai data Ι—an tsora ta.

“haka son ki yake a kowanne bugu na zuciya ta tare da fitar numfashi na”.

motsa fuska tayi cike da jin daΙ—i cikin zuciyar ta, tinawa da Nadeeyah yasa farin cikin ta ya tsaya annushuwar ta ta Ι—auke, ido ta Ι—ago tana duban cikin Ζ™wayar idon sa da Ι“acin rai a maganar ta tare da faΙ—a take kora masa bayanin,

“kaja wa waccan lusarar matar taka kunne akan shiga hurumina in ba haka walla sai na maida wannan dogon goshin nata ciki, ta bar ganin ina mata shiru ina Ζ™yale ta tayi tinanin ko tsoron ta nike ji, ina raga mata ne kawai saboda ni ba mai son tashin hankali bace amma idan bata saita hankalin ta ba to ni zan koya mata hankali…….”.

shiru yay yana sauraron masifar tata, sai dai ta nisa har tana Ζ™ulle ido kawai ya rufe bakin sa da nata da kisses, kasancewar kowa a desire yake so she was enjoying abinda yake mata.*__________?* Khaleed sam baya fahimtar abinda Rahinat take faΙ—i masa, baki Ι—aya ya Ι—imauce da jin sa a wata duniya ta daban, lokaci guda zazzaΙ“i ya rufe mata jiki sai kuka take ta na basa haΖ™urin ya Ζ™yale ta da zafi, bai bar ta ba sai daya tabbatar daya maida ta cikakkiyar mace tukunna shima kuma ya dawo hayyacin sa
+

gefe ya koma yana maida nunfashi idon sa a lumshe, wani sanyin daΙ—i ke ratsa ilahirin jikin sa, ita kam banda shashsheΖ™ar kuka babu abinda take, sai daya gama maida nunfashi kan hankalin sa ya dawo kan kukan da take yi, jikin sa ya jawo ta ya shiga lallashin ta yana bata haΖ™uri, Ζ™in sauraron sa tayi tana ture sa, shi ko kukan da take gaba Ι—aya ya Ι—aga masa hankali duk ya duburbuce, tsam ya matse ta jikin sa yana shafa gashin kanta yana afkin lallashi har bacci ya Ι—auke ta.

kwantar da ita yay ya shiga yayi wanka sannan ita ma ya haΙ—a mata ruwa kana yazo ya cicciΙ“eta ya kaita toilet Ι—in ya dire ta cikin bath-tub, take kuwa ta farka a baccin ta fashe masa da sabon kukan shagwaΙ“a.

murmushi yayi ya mata raΙ—a a kunnen sannan ya fice ya bar toilet Ι—in domin ta samu tayi wanka, sai data gama kukan ta sannan ta gasa jikin ta ta samu tayi wanka.

shi ko tini ya gyara kan gadon ya kimtsa wurin, tsabar rashin kunya ta Khaleed har Mami ya kira ya sanar mata cewar yau ya maida Ζ΄ar’ta mace dan haka tayi adu’an samun jika a wannan rana.

murmusawa kawai Mami tayi tace da shi, “Allahumma yahidika mara kunyan yaro kawai, ina fatan baka wahalar mani da ita ba?”.

tamkar yana gaban ta ya Ι—an sosa Ζ™eya yace, “ehh Mami sai dai raguwa ce Ζ΄ar’taki, sai kuka take yi”.

“tana ina bani ita”.

“tana toilet”.
“oak to ka tabbatar ta gasa jikin ta yanda ya kamata kamin na shigo anjima”.
“tom Mami”.

koda ta fito sai Ι“ata fuska take yi, shi ko yana ganin fitowar tata ya miΖ™e ya nufo gare ta, kauda fuskar ta gefe tayi tana ce masa,

“ni kar ka taΙ“a ni”.
tayi maganar a shagwaΙ“an ce.

hannu yasa ya Ι—auke ta yana faΙ—in, “haba Angel nah, am sorry kin ji, daΙ—in nan fa bani Ι—aya naji sa ba kema kan ki kin ji
.

kanta ta Ι“oye cikin Ζ™irjin sa, dariya yayi ya sauke ta kan stool ya Ι—auka mai ya shiga shafa mata, ita kam kunyar sa duk ta gama cikata, sam ta kasa kallon sa, dan haka yana gama sanya mata kaya ta masa wayo ta turasa parlo ta rufe Ζ™ofan ta dawo gado tana murmushi.

_BAYAN WUYA SAI DAƊI._

shine abinda ta faΙ—i cikin ranta.


*3 MONTHS LETTER.*

Nadeeya ce zaune akan gadon ta ta cika tayi fam kawa zata fashe.

Jakadiya tazo gaban ta ta duΖ™a tace,

“ranki ya daΙ—e ina fatan dai lafiya ko?”.

a hasale Nadeeya tace mata, “ina fa lafiya Jakadiya wannan matsiyaciyar yarinyar ta rabani ta Sultan, kwata-kwata hankalin sa bai kaina gaba Ι—aya ma mantawa yake da cewar ni matar sa ce, har kawo tsawon yanzu fa babu abinda ya shiga tsakanina da shi, ya bar ni da tsananin son sa d sha’awar sa”.


Jakadiya ta gyara zama ta numfasa, cikin murya ta magulmata tace mata,

“hmmm ai ranki ya daΙ—e ba haka Ι—aya ta bar sa ba, buzaye ai zama da su haΙ—ari ne, mugwaye ne da kike ganin su, na tabbata ta asirice Yarima ne”.


“haka kike gani Jakadiya”.”Ζ™warai kuwa ranki ya daΙ—e, amma ai na banzar tayi domin muma baza mu barta haka ba taci gaba da yin nasara akan mu, dole mu miΖ™e tsaye musan abin yi”.

+

“tau yanzu me kike ganin zamu yi?”.

Jakadiya tayi shiru tana nazari can tace, “tana da ciki ne?”.

Nadeeya ta Ι—anyi tunani tace, “da kamar wuya, domin da tana da ciki da kinji a fada yanda Mai martaba keji da ita Ι—in nan, kuma shi kan sa Yarima da zan gani daga gare sa”.

“to masha’Allahu, dama da tana ciki abin farko da zamu fara shine zubar da cikin saboda kar tazo ta haife mana baΖ™ar kadarar da zai gaji kujera, amma yanzu matso da kunnen ki kiji”.

nan Nadeeya ta bata kunnenta ta guntsa mata magana, dariya sukai tare sannan suka tafa, ran ta fari Ζ™al, nan take kuwa suka shirya yanda zasu je wurin boka.

****
“Aayan abinda yasa na kira ka shine, ina so na tinatar da kai cewar kamar yanda Rahinatu take matar ka haka Nadeeyah take mata a wurin ka, yanda kake fita hakkin waccan haka ya kamata kake fitta hakkin wannan ma domin dukan su matan ka ne kuma ko wacce nada hakki akan ka, kar ka bari Allah ya kama da tauye hakkin Ι—aya daga cikin su, ka zama adalin namiji a wajen matan ka kaman yanda muke fata ka zama adalin shugaba a wannan masarauta”.

“Mami nifa bana son wannan yarinyar kin fi kowa sanin haka tun muna yara jinin mu bai zo Ι—aya ba, kuma ni mace ne da Jad zai ce ya aura min ita ba tare da sani na ba bare neman izini, ni na yanke shawarar kawai zan sallame ta domin bazan iya zama da ita ba, totally ba ta Ι—aya daga cikin irin matan da nike ra’ayi, Angel kawai ta ishe ni nayi rayuwa ta cikin jin daΙ—i”.

duk yanda Mommy taso ta nusar dashi sam ya burki ce yace mata ba haka ba, ransa a Ι“ace ya miΖ™e ya fita daga Ι—akin ta, kai tsaye sashin mai martaba ya nufa, shi Ι—aya mai martaba ya yarda da shigowar sa ba tare da neman izini ba.

a kishingiΙ—e ya sami mai martaba hadimai na masa firfita yana kuma cin kayan itaciya, gefe da shi ya zauna ya gaida shi cikin girmamawa, fuskar mai martaba sake yana mai murmushi ya amsa masa.

sunkwi da kai Ζ™asa Khaleed yayi yay shiru har sai da Mai martaba yace dashi,

“ya dai sarkin gobe, da wata matsala ne naga ranka a Ι“ace haka, ina fatan ba acikin masauratar nan aka Ι“ata maka ba domin ko wane bazan raga masa ba, duk cikin jikoki na kai nafi so kaine wanda bana Ζ™aunar ganin Ι“acin ransa ko kaΙ—an, zan kuma iya aiwatar da komi domin ganin ranka ya faran tu na kuma ci zarafin duk wanda ya nuna cewar baya son ka”.

“Jad kai ne ba kowa ba”.

jin haka mai martaba ya miΖ™e zaune yana mai kallonsa, yana kuma mamaki da jin cewar shine ma yayi laifin ,kodai har yanzu bai daina fushi dashi ba a game da abind aya faru a baya.
“matso kusa dani nan Aayan”.
ya faΙ—i yana mai masa nuni da kusa da shi.

ya taso ya dawo inda ya umarce shi, fuskar mai martaba Ι—auke da damuwa yasa hannu ya dafa kafaΙ—un sa yace da shi


“laifin mina maka Aayan, mi kake so na maka wanda zai gusar da laifi na daga zuciyar ka?”.

“ina so kamar yanda ka haΙ—a aure na da Nadeeyah, a yau ka raba wannan aure domin bana son ta kuma bazan iya zama da ita ba”.

“haba Aayan, kar kayi haka mana, Nadeeyah fa Ζ΄ar’uwar ka ce duk da a baya baka son ta ayanzu ya kamata ka sota kodan matsayi na zama matar ka data samu, ka tausaya wa maraicin ta ka zauna da ita”.

“bana son yin jayayya dakai,bana son yin musu da maganar ka, Jad idan har ka tursasa mani zama da ita to lalle zan bar maka masarautar ka da Ζ™asar ka kaman yanda ka umarce ni dayi a baya”.

hankalin Mai martaba ya tashi da sauri ya tari numfashin sa yace, “baza ayi haka ba Aayan, kai da zaka amshi ragamar mulki nan bada jimawa ba, a wannan karon idan kayi nesa dani lalle zan shiga mawuyacin hali, dan haka domin kasancewar ka farinciki na yarda da abinda kake so”.

nan take Mai martaba yasa a kira masa maga-takarda yace yana buΖ™atar takarda da biro, ana kawo masa ya miΖ™awa Khaleed yace ya rubuta duk iya adadin sakin da yake so yay mata, nan take kuwa Khaleed ya rubuta mata cika biyu yace idan ta gama idda ta dawo zai zai cika mata sauran Ι—ayan ta. +

koda Mai martaba ya kirayi Nadeeyah ya bata takardar ta ta buΙ—a taga maike ciki, take a wurin ta yanke jiki ta faΙ—i, amma yayin data farfaΙ—o ba Khaleed kaΙ—ai ba shi kansa Mai martaban zagin sa take, uwa uba kuma Rahinatu.

zuciyar ta a hasale ta miΖ™e tana huci tayi turakar Mami tace ayau bata ga mai hanata kashe Rahinatu ba, da Ζ™ayar aka samu Ζ™artan fadawa suka rirriΖ™e ta aka kaita Ι—akin horo aka kulle.

Ɓangaren Rahinatu kuwa tunda ta labari yaje mata ta Ι—auka fushi da Khaleed saboda ya mata alΖ™awarin zai yi haΖ™uri ya zauna da Nadeeya kuma bazai taΙ“a sakin ta ba kamar yanda yake faΙ—i amma yau sai ya saΙ“a mata wannan alΖ™awari.

sose ta Ι—auka dokin fushi da shi ,tin Khaleed na Ι—aukan abin da wasa har yazo ya fara damun sa ganin da gasken-gaske dai fushi take sose.

takai yanzu gaba Ι—aya ta kulle sashen ta duk sanda yaje a rufe yake samun sa, idan kuma yaje Ι“angaren Mami domin ya ganta tana jin sa zata miΖ™e ta bar wurin, ta kulle duk wata hanya da zata sada su ta juna, shi kuwa baya ganin zai iya dawo da Nadeeyah sam.

****
tashin yau yana dawo daga masallacin asuba ya nufa sashen ta dan yasan da wuya idan ta rufe Ζ™ofa, saboda tana idda sallar asuba take zuwa gaida Mami da Mai martaba da Kakar sa.

yana ko zuwa ya tadda Ζ™ofar parlon ta a buΙ—e, har dakawan da ke tsaye zasu isar da saΖ™on shigowar sa ya dakatar dasu nan yace duk su tafi

ita kam data dawo daga gaida su Mami baki Ι—aya ta manta da batun rufe Ζ™ofa ta koma ta kwanta sai dai ta rufe Ζ™ofan Ι—akin ta, daya murΙ—a handle yaji a rufe kamar zai kuka, ya dawo ya nemi cushion ya kwanta.

sai 8 ta farka ta shiga wanka, yana kwance yaji motsin buΙ—e key, da hanzari kuwa ya miΖ™e ya nufa Ζ™ofan, yana zuwa ya murΙ—a handle a hankali ya tura Ζ™ofan ya shiga, hamdala yayi da godema Allah daya sanya har ya shiga bata san ya shigo ba.

kai tsaye ya nufa inda take yana takawa saΙ—af-saΙ—af, tana tsaye a gaban tangamamen closet tana ciro kaya, jikin ta Ι—aure da Ζ™aramin towel fari iya ka cinyar ta, baki Ι—aya jikin jiΖ™e yake da ruwa da alamu daga wanka ta fito, sam bata ji motsi na alaman mutum a bayan ta ba dan hankalin ta baki Ι—aya na kan zaΙ“ar kayan da zata sanya.

lumshe idon sa yayi tare da furta Alhamdulillahi a cikin ransa, duk wata nustuwa da samun farin ciki nasa tana tare da Rahinatu, buΙ—e idanuwan sa yayi ya sauke su kan santala-santalan cinyoyin ta masu Ι—aukar hankali, maida Ζ™wayar idon sa yayi daga saman kyakykyawar sumar kanta yana sauko da idon sa har zuwa tudun Ζ™afar ta.
gaba Ι—aya suran jikin ta sura ce mai firgita sha’awar duk wani lafiyayyan Ι—a namiji, cikin sanΙ—a ya Ζ™arasa takawa har ya kai gab da ita, dai-dai lokacin ita kuma ta zuge closet Ι—in ta juyo, a firgice ta waro ido taja da baya zata kurma ihu nan take towel Ι—in jikin ta ya zame ya faΙ—i Ζ™asa, saurin jawota yay jikin sa ya manne ta da Ζ™irjin sa yasa hannu ya rufe bakin ta.

“shiiiii!”. ya faΙ—i yana tsurawa Ζ™wayar idoon ta kallo, “matsoraciya nine to ba wani ba zaki mani ihu yanzu kisa azo a rufe ni da duka, mai martaba yasa a kulle ni”.

hararsa tayi ta shiga sauke ajiyar zuciya haΙ—e da runtse ido, ba Ζ™aramin tsoro ya bata saboda tasan ita Ι—aya ce a Ι—akin kuma babu wani mai shigo mata, ko hadiman ta iyakar su parlon ta da Ι—ayan Ι—akin ta amma ko Ζ™ofar wannan Ι—akin basa zuwa, shi kuma data san yana shigowar yanzu fushi take da shi tasan koya zo zai ga wurin a kulle ya koma.

shi kam wani sanyayyan murmushi ya saki mai sauti yana bin kyawun fuskarta da kallo, a iya ka kwanakin nan da suka Ι—auka tana hora sa ba Ζ™aramin kewar ta yayi ba, Ζ™ugunta ya kamo da kyau haΙ—e da kai bakin sa saman kumatun ta yay mata light kiss.

gaba Ι—aya hudojin ilahirin jikin ta sai da suka amsa, ji tayi wani abu ya tsirga mata zuwa tsakiyar kan ta, ita kanta tasan tayi kewar sa sai dai tana so ta hora shi domin ya dawo da Nadeeyah Ι—akin ta, sam sakin bai mata daΙ—i ba duk da ba zaman lafiya suke da ita ba.

Ι“ata fuska tayi haΙ—e da Ι—auke idon ta daga gare shi, hankalin sa ya tashi ganin har yanzu dai fushi take da shi, tace da shi, +

“ka rabu dani tunda dai ka koyi saΙ“a alΖ™awari”.

murmushi yayi yace da ita, “ban koya ba kaman yanda kike tunani, kawai dai bazan iya sirka soyayyar ki data wata Ζ΄a mace ba, Angel ki fahimce ni wallahi bazan iya haΙ—aki da wata ba, jikina iya mallakin ki ne anyi shi domin kene kawai”.

lumshe idon sa yayi ya fara yawo da yatsan sa guda a Ζ™ashin bayan ta, ita ma lumshe nata idon tayi taja numfashi ta sauke kamin nan ta buΙ—e ta sauke su a kan nasa da suka sauya kala, sun rune sun yi jawur ,ga kallon da yake mata jin sa take har zuciyar ta, baki Ι—aya zallar soyayyar ta data hango cikin Ζ™wayar idon sa ta kulle bakin ta, ga shi ita kuma a gaskiya bata shirya saukowa ba a yanzu.

“My Heart Beat”.
ya kira sunan ta cikin muryan raΙ—a, hannun ta ya kamo ya Ι—ora a saitin zuciyar sa tana mai jin yanda take harbawa, ganin bata amsa masa ba ya shiga yawo da tafin hannun sa a jikin ta yana ma gadon bayan ta shafa mai tafiyar da hankali, nan take taji tsayuwar da take ajikin sa na neman gagar ta, yunΖ™urin Ζ™wacewa tayi, take ya maida kansa saman wuyan ta ya shiga sumbatar ta sumba mai tada duk wata sha’awa.

yana yi yana goga gashin sajen sa a gefen fuskar ta yana kuma yawo da halshen sa cikin kunnen ta, take ta soma fita hayyacin ta, daga ita har shi jikin su ne ya Ι—au rawa lokacin daya maido da hannun sa ga Ζ™irjin ta, wata iriyar ajiyar zuciya ta sauke tare tasa hannayen ta ta kewaye shi, kanta ta Ι—ago sama tare da haΙ—a lips Ι—in ta da nasa kamin ta buΙ—e baki ta kama nasa laΙ“Ι“an duka ta shiga tsotsa kawa ta sami sweet, gaba Ι—aya babu wani kuzari ko Ζ™arfi a tare da su, sauran guntun kuzarin daya rage masa ya Ι—auke ta ya aza saman gado nan suka shiga romancing juna, abubuwan da suke ma juna tuni Rahinatu ta mance da wani fushi da take da Khaleed, har suka lula babban birin maji daΙ—i.

*AFTER 1 WEEK.*

Bikin Raihana da Khulaid ya Ζ™ara to ,hakan yasa Rahinatu shirya wa domin tafiya Nigeria ita dasu Mami.

kamin tafiyar tasu Mami tace zasu fara zuwa gidan amarya Nimrah dake zaune a saudia, Khaleed yace da Mami ai Rahinatu ba yanzu zata tafi ba sai ana gobe biki sai su taho tare.

mangare sa Mami tayi tace, “ka isa ma ka bimu, ai anan zaka zauna har muje mu dawo, kai kenan baza ka barta zuwa wurin ba kullum kana naniΖ™e da ita”.

“Mami ita ma ki tambaye ta kiji”.
“bazan tambaye ta ba Ι—in, tafiya dai bazamu da kai ba”.

ranar da zasu tafi jin yake ina ma yana da abinda zai hana tafiyar, baya jin zai iya wata guda ba tare da Angel a tare da shi ba.

zama yay tana shiri yana mata kukan shagwaΙ“a, ita kam sam bata bi ta kansa ba don idan ta biye masa zai kuma ruguza tafiyar yaune kamar yanda yayi a jiya.

sai data haΙ—a komi nata ta bada akai mota kana ta juyo gare shi, zama tai bakin gado tana masa Ζ΄ar dariya tana tsokamar sa.

kansa ya kwantar saman cinyar ta yana neman mata kukan gaske.
“Angel kin fi kowa sanin wane ni, kin san bazan iya zama ba tare da ke ba har tsawon wata guda, dan Allah kice ma Mami kin fasa wannan tafiyar”.

ido ta zaro waje, sumar kansa ta shigar da yatsun ta ciki tana yamutsawa, “lalle Husby kana son kanka da yawa, bikin Yaya Raihana kake nufin baza ni ba, tabΙ—i kai ma kasan abinda ba zai yiwu ba kenan”.

“ni bamce ki haΖ™ira ba, kice kin haΖ™ira da zuwa gidan Nimrah, ita tayi tafiyan ta idan ya rage 2dayz bikin sai mu tafi tare, amma yanzu ace sai kinje saudia kin yi 2week kin kuma zuwa nigeria kinyi wweeks ,haba Angel nah ina kike so nasa raina”.

cike da tsokana tace da shi, “kaga amfanin mata da yawa kenan, da yanzu idna bana nan sai ka tafiayr ka wurin Nadeeyah”.

“ai dama ban sake ta gaba Ι—aya ba, kamn nasan da zuwan wannan ranar, kinga yanzu idan kika tafi saina dawo da abata musha amarcin mu kamin ku dawo”.

wani malolon takaici ne ya kamata, mugun kishi ya tokare mata maΖ™o shi, ture kan sa tayi a samna cinyar tata ta yunΖ™ura zata miΖ™e ya dawo da ita ya zaunar yana mata dariya ita kam ta bone fuska har tana neman fashewa da kuka.

“Allah ya huci ran gimbiya, nida wasa nike maki, ramawa nayi nima, amma kema kin san ai Ζ™aryar wata mace tace zatai gogayyar miji da ke”. +

da Ζ™yar ya shawo kan ta, Mami nata kiran wayar ta ta fito amma bai barta ta tafi ba sai daya lalata kwalliyar ta gaba Ι—aya, sai daya sha zumar ta ya Ζ™oshi kana ya barta ta tafi cike da kewar ta.*__________?* masha’Allahu anyi bikin amarya Raihana an gama lafiya sai fatan zaman lafiya da kuma zuri’a Ι—ayyi ba. +

duk waΙ—an da suka je biki suna zuwa su diba Anty Asma’u wadda ciwon paralize ya kamata, ta zama abar tausayi duk wanda ya ganta sai ya zubar mata da Ζ™walla, shi yasa aka ce a rayuwa ka shuka alkhairi, bada ban darajar Ζ΄aΖ΄an ta da taci ba Uncle Badamasi ce yay baya dawowa da ita.

ranar da su Rahinatu zasu baro nigeria harda kukan ta domin tasan yanzu kamin ta sake zuwa sai anjima, tunda tana komawa school zata ci gaba da zuwa.

wannan karan ma sai da suka fara zuwa saudiya gidan su Mami kana suka Ι—auko hanyar Libya.

tun suna can Mami ke lura da yanayin ta na kwana biyu da take fama da zazzaΙ“i, jikin ta duk yayi wani colaps ko abinci ma bata fiya ci ba.
sai dare suka sauka, lokacin da Rahinat da shiga Ι“angaren Khaleed bai nan sun fita wata gayyata shida mai martaba.

ji tayi ba zata iya komawa Ι—akin ta ba saboda rashin Ζ™arfin jiki da take ji,toilet Ι—insa ta shiga ta yi wanka ta fito, ko mai bata shafa ba ta Ι“ingile anan kan gado bacci yay awon gaba da ita.

koda ya dawo ya ganta murmushi kawai ya saki ya gyara mata kwanciyar yaja blanket ya rufe ta, stool ya janyo gaban sa ya Ι—auka system ya kunna ya hau aiki.

sai kusan 11 ya kammala ya turawa mai martaba saΖ™on sannan shima yayi shirin kwanciya, jikin sa ya jawo ta ya hugging nata very tightly, yasan duk gajiya ce ta sata wannan baccin banda haka da Angel sai ta jira dawowan sa, cikin zuciyar sa yake ta mitar an wahalar masa da ita, ahaka har bacci shima ya Ι—auke shi.

asuba nayi kusan tare suka farka, yay alola ya wuce masallacin fada ita kuma tai tata sallar a Ι—aki, sai dai fa wannan ma tana iddawa ta kife da bacci a wurin.

shi ko tun bayan daya idda suka zauna tattaunawa a game da Ι—aurin ratayar da za’ai ma Sultan Dameer, shi ba shi da matsalan komi sai da yace da mai martaba ayi komi kamin gari ya waye Angel Ι—in sa ta sani.

Raihan nata kuka lokacin da aka rataye mahaifin sa, yana ji yana gani aka zuge shi, duk da Dameer ba mutumin kirki bane kowa ya shaida hakan a masarautar ,amma da yawa sai da suka yi kukan mutuwar sa sai dai Khaleed ya jaddadi kowa daya ja bakin sa yay shiru, idan har suka bari matar sa ta sani to lalle zai masu hukuncin da bazai masu daΙ—i ba.

suna zazzaune anan fada Mami ta kira Khaleed take shaida masa yayi sauri yazo matar sa b….
lafiyar da bata Ζ™ara faΙ—i ba ya yanke wayar ya taso da sauri ya fito, a hanya sunkai kiciΙ“is da Abbas, tambayar sa ya shiga yi,
“ranka ya daΙ—e lafiya dai ko na ganka a hargitse haka”.

ba tare daya kalle shi ba yace, “maza tada mota”.

yana shiga yaga Rahinatu kwance saman cinyar Mami, gaban ta ya duΖ™a saitin fuskarta ya shafo wuyan ta nan yaji jikin ta zafi kawa garwashi.

“Heartbeat mike damun ki baki faΙ—i mani ba?”.

kasa ba shi amsa tayi ta bisa da idanun ta da suka kawo ruwa, saboda sose zazzaΙ“in da ke jikin ta ke shigar ta ga wani azababban ciwon kai na daban.

ai a ruΙ—e ya Ι—auke ta daga saman cinyar Mami ya fita da ita, ko tsayawa sauraron abinda Mami kece masa bai tsaya ji ba.

ita kuwa cike da shagwaΙ“a ta narke masa ajiki tare da fashe wa da kukan shagwaΙ“a wanda jinsa ya sake Ι—aga hankalin Aayan.

yana fita Abbas ya buΙ—e masa gidan baya ya shiga sannan shima ya shiga yaja su, direct asibiti suka wuce, suna zuwa likita ya mata gwaje-gwaje nan yay ma Khaleed congratulation ya sanar da shi Madam na Ι—auke da cikin wata 3.

ina ai musalta farinciki a wurin Khaleed ba zai faΙ—u ba, nan take ya kira Mami ya sanar mata ya kuma sanar ma da Mai martaba, kan kace wannan masarauta ta Ι—auka tun kamin su dawo.

tini mai martaba yasa aka soke raΖ™uma domin ai sadaΖ™a da su.

Ι“angaren Nadeeyah kuwa tunda Jakadiya taje mata da labarin ta nemi natsuwar ta ta rasa, hankalin ta ya ta shi, safa da marwa kawai ta shiga yi a duk ta haΙ—a zufa.ganin haka yasa Jakadiya kwantar mata da hankali akan cewar ta bar mata komi a hannun ta, ba zubda ciki ba ko ciwon hauka take so a Ι—ora mata sai anyi yanda take so.sai a lokacin zuciyar Nadeeyah ta sami nutsuwa nan ta cika Jakadiya da kuΙ—aΙ—e masu yawa tace ta aiwatar da duk abinda ya taga ya kamata.

Rahinatu kuwa tun samun cikin nan samun kulawa daga wurin Khaleed ya nin ka na da, riritata yake tamkar Ζ™wai, ko da za shi course itally ce yay da ita zai tafi sai da Mami tai masa da gaske sannan ya haΖ™ura amma ba don ya so ba, son samun sa ya tafi da abar sa shi zai fi kulawa da ita acan.

haka ya tafi bada son ransa ba, da sukai masa rakiya airprt kawa ya janyo ta su tafi, ga cikin ya wani Ζ™ara mata kyau Ζ™irjin ta ya ciko sose yayo sama, haka suka rabu da kewar juna, a system kam kullum suna cikin vedio calling shida ita.

a daddafe ya samu yayi 2weeks acan ya saito hanya dan sam ba zai iya wannan wata gudan ba babu Angel kusa da shi, jin sa yake tamkar ya shekara dubu bai gan ta ba, da murnar sa ya nufi Ι“angaren ta sai dai yana zuwa ya tadda bata nan hadiman ta suka ce masa tana Ι“angaren Kakar sa Jadda.

yana zuwa ya tarar da abinda yasa shi kurma ihu ta zubewa Ζ™asa yana jin zuciyar sa kamar zata fito, domin cikin da yake marari ya zube, Nadeeyah tayi nasara akan hakan, sai da su Jadda suka lallame shi da tasassun kalamai tukunna ya sami nutswa cikin ransa tare da roΖ™on Allah ya ba su wani mai albarka.

kwana biyu da faruwan hakan yay masu visa zuwa america domin a asibiti su sake kula masa da ita daga nan kuma su sha honeymoon Ι—in su.

cikin jirgi Rahinatu kwanciya tayi ajikin sa shi kuma yana aikin shafa bayan ta kamar yana lallashin yaron da zai bacci, a hankali a hankali take masa hira mai daΙ—i duk wanda ya Ι—aga ido ya kalle su yaga cikakkun masoya, a haka har tayi bacci.

har sanda suka isko america bata tashi ba, shima kuma bai tashe ta ba ya Ι—auke ta suka fito, koda ya fito tuni motoci har sun zo Ι—aukan su.

gidan da suka sauka mai kyau da tsari, tunda suka sauka wanka wannan baya barinta tayi da kanta, shi zai mata ya naΙ—o ta a towel ya shafa mata mai yasa mata kaya ya kuma bata abinci baya barin ta yin komi da kanta.
sai da sukai wata biyu cif sannan suka kamo hanya suka dawo, satika kaΙ—an da dawowar su Rahintau ta fara rashin lafiya sose.
a wujugace akai kaita asibiti, ana zuwa aka jona mata drip jikin ta sannan likita ya aunata nan ya tabbatar wa da Khaleed tana Ι—auke da juna biyu na tsawon wata biyu da sati guda.

ai wannan karon murnar har tafi ta farko, don take Khaleed ya durΖ™usa Ζ™asa yayi sujjada ga Allah yana mai nuna tsananin farincikin sa da godiya ga Allah.

yana miΖ™ewa ya zura hannu aljihun sa ya ciro damin kuΙ—i ya damΖ™a ma Dr Abid, kallon kuΙ—aΙ—en Dr Abid yayi ya kuma kalla Khaleed da alaman tambayan na minene.

“thank you so much Dr da wannan albishir Ι—in da kayi mani, wannan ita ce kyautar ka”.

murna sose Khaleed keyi baki yaΖ™i yaΖ™i rufuwa, waya ya Ι—auka ya kira Mai martaba ya sanar masa, yana fitowa ma ya sanar da Mami abinda likitan ya shiada masa, murmushi kawai tayi tace alhmdl Allah ya raba lafiya amma ita dama tuni tasan menene, haΖ™iΖ™a ita ma ba Ζ™aramin farinciki ta kasance ba aciki Allah yasa an sami tsayayyae shine abinda take roΖ™on Allah, dama ga Nimrah ma da ciki farincikin sai ya zame mata biyu.

room Ι—in da take kwance suka Ζ™arasa, cire mata drip kenan suka shiga, babu kunyan Mami bare ta nurses ya Ζ™arasa da azarΙ“aΙ“in sa ya rugumota jikin sa tsam yana faΙ—in,

“i rilly rilly love you Angel nah, another gift from God, na gode na gode, Allah ya sauke mani ke lafiya”.

ya Ζ™arashe maganar da bata sumba a kumatu, ita kanta nurses sai data ji kunyan abinda yayi kasancewar ta budurwa.

murmushin jin daΙ—i tayi ta ruΖ™o hannun sa, “da gaske Husby ina Ι—auke da wani sabon cikin?”.

“Ζ™warai kuwa, abinda Dr ya shaida mani kenan yanzun haka”.

ya faΙ—i yana mai shafo cikin ta.runguma ita ma ta kai masa tare da kwantar da kanta saman Ζ™irjin sa.

“kayi namijin Ζ™oΖ™ari Husby nah lalle kai ba Ζ™aramin gwarzo bane, cikin watanni uku ka sake saka Ζ™wai”.

fuskar sa ya kwanto saman gashin kanta da babu Ι—an kwali, “ai daga kene Heartbeat, kogin madara da zumar ki daΙ—in sa daban yake…..”.

Mami kam bazata juri ganin wannan rashin kunyar ba don haka ta saki gyaran murya, sam Rahinatu ta manta da cewan tana wurin, shi kam dama yana sane, wata uwar kunya ce ta lullΙ“ueta tana jin kawa ta nutse cikin Ζ™asa.

ita wata kunyar ma ta daban data kamata Mami fa tasan yanda ankai ta samu cikin, ai ina ji tai kaman tai tsuntsuwa nan ta Ι“oye fuskar ta a bayan Khaleed.
sai dare aka sallame su suka koma gida.

a wannan cikin kam zo kuwa ga sabuwar tarairaya, Lallami, So, Da kuma Ƙauna da Khaleed ke bawa Rahinatu, motsin ta ma sam bada son ranshi take ba don aganin sa motsawa ma wahalar ta yake, ita kuwa banda narkewa ba abinda take masa.

babu inda yake zuwa ko da yaushe tana maΖ™ale jikin sa ita ma tai ta zuba masa shagwaΙ“a.
haka Ι“angaren kowa ma samun kulawa take kowa Ζ™ara son ta yake.

sai dai fa shima wannan karan abin sam baima Nadeeyah daΙ—i ba, nan sun kai Ζ™ulla-Ζ™ullar su da Boka akan ai mata kurciya ko a haukatata.

yanda suka so haka akai, wata rana Rahinatu ta fito da tirtsitsin cikin ta don lokacin yana wata bakwai, tana gab da shiga turakar Jadda Nazneen Nadeeyah ta hange ta da sauri ta cilla mata layar dake hannun ta.

jikin ta har wani tsuma yake yana Ι“ari ,burin ta kawai tazo ta taka wannan layar ko ta wuce ta kusa da ita burin ta ya cika, sai dai tana gab da nufar wajen sai ga Khaleed ya sunkuce ta ta baya ya juya da ita saboda bai son ta fito ba, daga shigar sa toilet ta sarfo don ta gaji da zaman wuri Ι—aya.
wani malolon takaici da baΖ™in ciki ya turnuΖ™e maΖ™oshin Nadeeyah, ranta a Ι“ace ta nufi inda layar take zata Ι—auke kawai bata ankara ba ta zame ta faΙ—i akan ta, ba wata-wata asiri ya koma kanta tamkar yanda boka yace da ita, hauka tuburan sai ihu take tana faman tsalle-tsalle.

abin ya bawa kowa tsoro da mamaki, dake Jakadiya ita ma baΖ™ar munafukar kanta ce nan ta je ta sami mai martaba ta feΙ—e masa biri da wutsiyar sa akan Ζ™ulalliyar da Nadeeyah tai ta zame kanta.

hukuncin da Mai martaba ya Ι—auka akan Nadeeyah yaso ace lafiyar ta Ζ™alau da gobe aka ce ta kuma abinda tayi ba zata yi sa ba, sai can bayan gida aka mata wani Ι—aki aka sanya ta aciki, nan take kashi tai fitsari haka kuma taita wani irin kuka kamar na jaki, sai dai ana ta mata magani da kuma adu’oi.

cikin hukuncin ubangiji cikin Rahinatu ya shiga wata tara cif, zuwa wannan lokacin ta gama yin nauyi domin tashi da zama da Ζ™yar take yin su bare uwa uba tafiya, Ζ™afafun ta sunyi mugun kumbura ita kanta cikin ya kumbura ta, ba Ζ™aramin tausayin ta Khaleed keyi ba, motsi kaΙ—an zatai zai shiga jero mata tambayoyi wani bin ma har tsokanar sa take don taga yanda zai ruΙ—e.

daren alhamis ta tashi da tsananin ciwon mara ga bayan ta ma, jikin ta duk ciwo yake mata, dauriya da cijiya kawai take saboda kar ta Ι—aga hankalin Khaleed dake bacci, tun tana dauriyar har abin yafi Ζ™arfin ta, nan ta kamo Khaleed ta shiga girgiza shi, wani ikon Allah ya jima bai irin wannan baccin ba, duk baccin sa kuwa tana motsi zai buΙ—e ido ita har mamaki ma yake bata amma yau kam ta shin sa take yana sake gyara kwanciya.

yana farkawa ya ganta yaga yanayin da take, ai a kiΙ—ime ya sakko daga gadon ya nemi jallabiya ya zura, sannu yake ta faman jera mata ya sunkuce ta suka tafi asibiti ba tare da sanin kowa ba don lokacin Ζ™arfe 2 na dare.

suna zuwa likita yaga halin da take ciki yace a wuce da ita labour room, farko Ζ™i Aayan yayi yace shi ta haihu a gaban sa, ganin abu yaΖ™i ci yaΖ™i cinyewa haihuwa har akai asuba bata zo ba ya Ι—au waya ya kira Mami ya shaida mata hankalin sa duk a tashe.

nan da nan ko suka Ι—unguma mutan gidan suka taho asibitin, lokacin da suka iso yana daga tsaye kusa da labour room Ι—in ya kifa kansa, Abie ne ya taΙ“o sa, yana Ι—agowa ya rungume Abie tare da fashe da kuka, kukan sa yake sose babu Ζ™aΖ™Ζ™autawa tamkar Ζ™aramin yaro, babu abinda ya shalle sa da kallon da mutane ke masa, gani yake tamkar zai rasa Angel Ι—in sa, idan ya jiyo ihun kukan ta har zabura yake yay Ζ™ofan shiga labour roon Ι—in su Jad su ruΖ™osa.
+

da Ζ™yar suka lallashe shi Abie ya zaunar da shi kan kujera ya dafa kafaΙ—ar sa, yana mata adu’a yana zubar hawaye, iya jigata da wahaltuwa Rahinatu ta sha don bata haihu ba sai yammacin wannan rana awa goma sha biyar tana abu guda, 19:00 na dare ta haifo santalelen Baby boy Ι—in ta, yaro fari Ζ™al kyakykyawa da shi jinin labarabawa, kamar sa sak ta kakan sa sarkin Libya.

tunda Rahinatu ta yunΖ™ura ta fiddo da shi ta fitar da nishin Ζ™arshe bata kuma sanin a duniyar da take ba.
nan da nan ko aka shiga gyaran yaron aka tsabtace shi sannan ita ma aka shiga gyara ta, amsar yaron Dr yayi a hannun nurses Ι—in ya fita da shi.

yana fitowa kuwa suka yo kansa da tambaya Ι—auke a bakin su, sai dai abinda suka gani a hannu’n sa maganar kowannen su ta tsaya, farinciki duk ya lulluΙ“e su kowa murna fal a ransa.

murmushi yayi ya miΖ™a masu Baby’n yana taya su murna, duk abinda ke faruwa Khaleed bai san abinda ake ba yana can duniyar kuka ya kifa kai kansa a cinyar Abie.

jin kukan jariri yasa shi Ι—agowa, yana Ι—aga ido ya hango Mami riΖ™e da jariri a hannu, ai bai san lokacin da ya wani zabura ba ya miΖ™e yay wajen su, kallon kowa ya hau yi yaga babu ita, Dr Abid ya nufa yana kallon sa.

“Dr ina matata?”.
yayi tambayar a hargitse hankalin sa na neman barin jikin sa, don ganin jariri kaΙ—ai ba Ζ™aramin fargaba ya shiga ba.

sai da Dr yay murmushi sannan yace masa, “tana ciki”.
ai bai jira wata cewar ba ya matsar da Dr daga bakin Ζ™ofan yay ciki, yana zuwa ya tadda ita kwance kawa matatta, bacci take tana maida numfashin wahala, Ζ™arasawa yayi ya zauna gefen ta tare da ruΖ™o hannun ta cikin nasa, tsabar tausayin ta bai san sanda sabuwar Ζ™walla ta cika idon ba ta zubo.

dai-dai lokacin kuma su Jadda suka shigo suma, kowa hankalin sa ya tattara kan yaron ana ta yaba kyawun sa, Jadda kema Jad tsiyar ita ai ta sami sabon miji tunda dama shi ya tsufa.

Khaleed kam sam hankalin sa bai jikin sa saboda rashin farkawar Angel, bai sami natsuwa ba sai da Dr Abid ya shaida masa Ζ™alau take babu wata matsala an mata alluran bacci ne don ta huta.

cikin Ζ™anΖ™anen lokaci masarauta da gari ya Ι—auka, kafafen yaΙ—a labarai da ko’ina abinka da haihuwar Ι—an masu Ζ™asa.
tunda Rahinatu ta farka sabon farinciki ya lulluΙ“e Khaleed, Ζ™aunar ta da saoyayyar ta Ζ™ara ratsa cikin Ζ™ashi da Ι“argo na zuciyar sa.

kasancewar bata da wata matsala a daren aka sallame su suka koma gida.
hadimai da fadawa nata kai komo, tun kamin shigowar su busar serewa da algaitu ke ta shi duk da kasancewar dare ne, kowa Ζ™oΖ™arin sa so yake ya zama mutum na farko da zai fara taya Sultan Aayan murna domin samun babbar kyauta.

sose Rahinatu da Boy Ι—in ta ke samun kula daga Ι“angaren mijin ta da Ζ΄an’uwan sa, trolly set biyar yasa aka judo masa da kaya na jariri daga saudiya aka kawo masa a washe gari.

Ζ΄an’uwa da abokan arziΖ™i kuwa koda yaushe cikin tururuwar zuwa barka suke, kwana biyu da haihuwa Raihana ta diro garin itama lokacin Ι—auke da jaririn cikin ta, ana kwana huΙ—u kuwa sai ga su Hajiya da Ammi suma sunzo har Yaya Suwaiba.

kamin suna akwati set goma sha biyar Aayan ya dire ma yaron sa da Maman sa, yau ta kama ranar suna inda yaro yaci sunan Kakan mahaifin sa sarkin Libya wato Suhail suke kiran sa da Arman.

zo kuga ruwan kuΙ—i da kyauta a wannan rana, sai da Aayan ya Ζ΄anta bayi 100 banda waΙ—an da sarki shima ya Ζ΄anta, haka nairori suka dinΖ™a kuka a wajen taron shagalin suna, sama ta ka ake Ι“arin su, duk wanda yazo wurin nan sai an masa kyauta ta musamma mai tsoka, don mutane biyar Ι—in farko da suka fara halarta wajen da maΖ™ullin mota aka bisu ciki harda su Yaya Aisha tah da su Khaleesa, Nusy GidaΙ—o kuwa dama ita ce uwar buΙ—e taro don sallar asuba ma a wannan hall na cikin masarauta tayi ta saboda kar a rab tayi ta saboda kar a raba wani abun ba ita.
+

sha’ani ake ta gudanarwa namomi nata kuka a bakunan mutane, Maman Husnah na hango loko can ta kwashi nama cikin wata kula tasa agaba sai ci take tana suΙ—e hannu, data ga an kuma shigowa da abun rabo zata taso da gudu tazo ta shige gaba saboda kar ai rabo babu ita, Ζ™arshe ma mayafin ta cire shi tai ta dunΖ™ule a hannu, Ι—aurin Ι—ankwali kuwa tsabar zalamar nama ya kunce an maida shi irin na tsaffi.

su My Zee,SisNah,Precious,Maman Abdallah,Uwar biri Hanash, sai Ι—aga selfie ake ana Ι—asa hotuna a inda ba’a taΙ“a zuwa ba, a Ζ΄an gayyar soΙ—i kuwa harda Ζ΄an xumunt@ Novell@ suka yo ayari nida ko katin gayyata ban kai masu ba, duk sun zauna akan kujerun da aka jera na alfarma sai Ζ™walala ido suke suna jiran akawo masu nasu kason niko na rufe taro nace an ta shi, ina ta masu dariya ciki-ciki nace waya kawo ku gayyar soΙ—i gobe kwa kuma zuwa ba abinda zan bari a baku.

haka aka sha taro masha’Allahu taro tamkar naΙ—in sarauta, an tara jama’a babu Ζ™arya kuma duk wanda yazo sai yay hani’an yake tafiya.

Sultana Yasmeen dake prison a kulle ji take da zata sami damar fitowa da ba’abinda zai hanata banka ma gidan nan wuta shegu kowa ya rasa ran sa a banza, banda rashin adalci Ζ΄ar’ta na cikin wani hali amma su farinciki ma suke akan haihuwar shegen yaron nan da taso mutuwar sa aciki kamin ya fito.

tunda Khaleed yaji cewar Rahinatu wurin Jadda zata koma ransa ya matuΖ™ar Ι“aci, sam bai so hakan ba don wannan an Ζ™ware shi ne kawai, yana ta faman kumbure-kumbure ya miΖ™e daga Ι—akin nata ya wuce sa shin sa kamar zai kuka.
Mami nata masa dariya tace kuma kar ta sake ta dinga ganin Ζ™afar sa har sai anyi arba’in, a zuciyar sa kuwa yace da ku kanku sai kun gaji kun bani a bata, haka yake zuwa kullum babu ko kunya don ma in ya tashi wani abin Rahinatu bata bi ta kansa.

ranar kuwa data dawo ai Khaleed kawa zai tsaga Ζ™irjin sa ya sanya ta, tunda ya Ζ™ure ta da ido yana kallon ta kawa yau ya taΙ“a ganin ta, shi kam wani kyau ta daΙ—a masa na musamman tamkar an sake halittar ta da zallar madarar kyau, Ζ™irjin ta dake Ι—aukan hankalin sa duk sun daΙ—a cika.

Arman dake hannun ta ya amshe ya fita da shi ya kaima Jadda, yana dawowa ya tarar da ita tana Ζ™oΖ™arin zuge zip Ι—in rigar ta, daga zuwa taya ta kuma ai nan salo ya sauya, lokaci guda ya gama burkita mata tunani, shi kansa nemna fita hayyacin sa yake, burin sa kawai ya jisa cikin Ζ™oramar zumarta, shi sam baya gajiya da ita ko kaΙ—an, kullum sake zama masa sabuwa take ga uban daΙ—i da take Ζ™arawa, wannan dare kam an gwangwaji sabon amarci saboda Mami da Jadda gyara suka mata na musamman, Ζ™amshin ta duk ya susutar da shi bai sami nutsuwa ba sai daya ji sa a duniyar data fi komai daΙ—i… Rahinatu na ganin so da Ζ™auna a wurin mijin ta da bata taΙ“a zato ba.

wani bin har haushin kanta take ji da raΙ—awa soyayyar su ƘADDAR SO da tayi a baya.
haka rayuwa tai ta tafiya shaΖ™uwa na daΙ—a shiga tsakanin su, kullum tamkar ana Ζ™ara masu son juna.

shekarar Arman uku aka haifa masa Ζ™anne 2wins duk mata, shima wannan lokaci anyi bisha-sha, yara suka ci sunan Mami da Ammi ana ce masu Mahnoor da Maisha, Arman na son Ζ™annen sa, haka zai zo yake ta leΖ™en sj ta cikin cot nasu yana kaΙ—a masu abin wasa, wani lokacin ko in har akan gadon ta ta bar su to har Ζ™oΖ™arin Ι—aukan su ya ke, sai ta kore shi ya tafi wurin Abie yana kuka, in ya tambaye sa yace Ammi ce.

Ι“angaren Raihana ma nada yara uku a lokacin, mace Ι—aya Jannat sai tagwayen mazan ta biyu Fadil da Fahad.

haka Nimrah ma a lokacin tana da Ι—iyar ta Jasmeen.


*ALHAMDULILLAHI ANAN NA KAWO ƘARSHEN

Post a Comment for "YAREEMA KHALEED CHAPTER 9 THEND KARSHE"