YAREEMA KHALEED CHAPTER 8
2 YAREEMA KHALEED CHAPTER 8 ________?* *2MONTHS LETTER.* + Yau ne aka fito da Raihana daga cikin kurkukun da aka aika da ita, kuma ayau ne dai-dai wannan lokaci su Ammi da suka koma nigeria suka dawo domin tafiya da ɗiyar tasu. Allah sarki baiwar Allah Raihana abar tausayi,duk ta rame ta ƙanjame tamkar ba ita ba, ga wani baƙi da tayi duk kuwa da tafi Rahinatu haske amma ayanzu kam Rahinatu madara ce akanta. dukansu a zaune suke acikin fada kowa yana jiran isowar su, zumuɗi duk ya hana Rahinatu nutsuwa so take kawai taga shigowar ƴar’uwar tata. sai da aka sanar ma da mai martaba kana ya bada izinin shigowar tasu. hannayenta da ƙafafuwanta duka ɗaure suke da ankwa, kana kallonta kaga wadda ta azabtu, tsabagen wuyar da tasha da ƙyar ma take ɗaga murfayen idonta. da gudu Ammi ta taso ta rungume ɗiyar tata ajikinta tana kuka, itama kukan ne ya suɓuce mata dama a maƙoshinta yake. dukansu farinciki suke sose, tin ma Rahinatu data ƙan-ƙameta ta kasa sakinta har sai da mai martaba yay sallama kowa ya w…