YAREEMA KHALEED CHAPTER 7

YAREEMA KHALEED CHAPTER 7
YAREEMA KHALEED CHAPTER 7 *__________?* ko bayan da Nawwara ta ɗaga abinda taji mahaifin nata ya faɗa ne ya ɗaga hankalinta, da sauri kuwa ta faɗa ɗakin Anty. + zaune gefen gado ta ganta ta rafaka uban tagumi, ta dafata tace, “mi Hajiya Saddiqa tace maki?”. ai gaban Anty sai daya faɗi jin ambatar sunan Hajiya Saddiqa, bata taɓa sanin da shaiɗaniyar mace take mu’amala ba sai data nuna mata halinta, to kome zai faru da ita ai sai dai ya faru da ita amma bazata taɓa iya mu’amala da mace ƴar uwarta ba. saɓo mai girma a wurin Allah, mai aikata shi Allah ya tsine masa, da sauri ta girgiza kanta tace da Nawwara, “babu komai tace dai zata je ta dawo”. Nawwara tace, “oak, to Anty Baba ne ya ƙirani yace wai mu shirya yanzu yasa Yaya ya gama booking zamu wuce ƙasar Libya”. a firgice Anty ta zaro ido dan zancen ba ƙaramin razana ta yayi ba, kamin tayi wani yunƙuri na magana suka jiyo ƙarar jiniya a harabar gidansu. da sauri suka miƙe su duka suka fita, suna isa parlo suka ci karo da Hajiya a tsaye fuska…