YAREEMA KHALEED CHAPTER 4

YAREEMA KHALEED CHAPTER 4
YAREEMA KHALEED CHAPTER 4 ••••• firgigit Raihana ta dawo daga dogon tinanin data tafi wanda tayi tin a lokacin data ga mutuwar Khulaid a TV. yanda ta haɗa zufa kace damben gaske tayi ba tinani ba, Khalid dake gefenta ta kalla wanda ke cikin tsantsar mamaki,al’ajabi da kuma ɗarsuwar firgici a zuciyarsa. dogon numfashi ta sauke wanda ya sanya Khalid dawowa daga tinaninsa yana kallonta. hannunta ta maƙale da nasa, zufa kawai take haɗawa domin tabbas idan har asiri ya tonu ayanzu to kashinta ya bushe. duk da jarumtar da yake tare da ita amma hakan bai sashi jin tsoro a cikin zuciyarsa ba domin gani yake tamkar aljanu ne suka buɗe masa ido. ta gefen ido guda Raihana ke kallon Rahinat dake duban tv tana goge hawaye. itama sai yanzu ta maida baki ɗayan hankalinta kan Tv ɗin dan sake tabbatar da mutuwar Khulaid shin gaske ce. ganin gaskiyar lamari duk sai jikinta ya mutu, take tausayin bawan Allahn ya kamata saboda sadaukarwar da yay akanta. amma taya akai hakan ta kasance? amsar da bata da wanda zai …