Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

YAREEMA KHALEED CHAPTER 4

YAREEMA KHALEED

CHAPTER 4





••••• firgigit Raihana ta dawo daga dogon tinanin data tafi wanda tayi tin a lokacin data ga mutuwar Khulaid a TV.

yanda ta haΙ—a zufa kace damben gaske tayi ba tinani ba, Khalid dake gefenta ta kalla wanda ke cikin tsantsar mamaki,al’ajabi da kuma Ι—arsuwar firgici a zuciyarsa.

dogon numfashi ta sauke wanda ya sanya Khalid dawowa daga tinaninsa yana kallonta.

hannunta ta maΖ™ale da nasa, zufa kawai take haΙ—awa domin tabbas idan har asiri ya tonu ayanzu to kashinta ya bushe.

duk da jarumtar da yake tare da ita amma hakan bai sashi jin tsoro a cikin zuciyarsa ba domin gani yake tamkar aljanu ne suka buΙ—e masa ido.

ta gefen ido guda Raihana ke kallon Rahinat dake duban tv tana goge hawaye.

itama sai yanzu ta maida baki Ι—ayan hankalinta kan Tv Ι—in dan sake tabbatar da mutuwar Khulaid shin gaske ce.

ganin gaskiyar lamari duk sai jikinta ya mutu, take tausayin bawan Allahn ya kamata saboda sadaukarwar da yay akanta.

amma taya akai hakan ta kasance? amsar da bata da wanda zai bata ita sai dai kuma idan har ta gano cewan su Sultana Yasmeen ne sila to itama sai taga bayansu.

jitai Khaleed ya kama hannunta ita da Nimrah sun wuce zuwa room Ι—insu, suna tafe Rahinat na bin bayansu da kallo har sukai cikim Ι—akin.

baki Ι—aya Rahinat acikin tashin hanΖ™ali take, ita bata damu da baΖ™in mugun mijin da ƘADDARAR SO ta haΙ—asu ba, babban burinta wannan baΖ™ar azzalumar da take basaja matsayin ita ta fitar da ita daga wannan mawuyacin halin data jefata.

ko yanzu a wanna hali mahaifanta ke ciki oho gashi bata da wayar kiransu idanma ta samu to da wannan bakin zatai masu magana bayan azzaluma mai kmaa da ita sun nakasa ta.

Ammi,Abbi da Hajiyanta kawai ta tina ta sake fashewa da kuka.yanzu taya zata koma garesu bayan bata da kuΙ—in jirgi bata da hanyar komawa nigeria tinda bata san ko’ina ba.

jin saukar hannun Raihan tayi akan nata, da sauri ta zame tana kaΙ—a masa kai.

yatsunsa ya sanya ga kumatunsa ya motsa wanda yay mata nuni datai murmushi.

tana kallonsa ta Ι—an murmusa sannan ta haΙ—a hannayenta biyu tai masa godia, ta juya zata tafi yasha gabanta yace,

“dan nabiyurrahmati ki tsaya”dakatawa tayi da tafi ta Ι—aga masa hannu alaman mi zaka mani

“kince baki san inda kike ba, to yanzu idan kin tafi ina zaki?”

murmushin tai wanda ya taho tare da hawaye ta kuma bashi amsa da hannu “nima ban sani ba”

ya juya ya kalla room Ι—in dasu Raihana suka shiga, “kin san wadda naga kina nunawa Ι—azu ne ,wannan mai kama dake Ι—in?”

tai saurin kaΙ—a masa kai alaman a’a saboda bata son ya shigo rayuwarta ya rasa ransa shima kaman yanda Khulaid ya rasa nasa a garin taimakonta.

“cikin su ukun duk ba wanda kika sani?”

ta sake Ι—aga masa kai. yace, “oak to shikenan, amma idan ba damuwa kizo muje gidana mana ki zauna kamin Allah ya baki lafiya”

ta girgiza masa gami da haΙ—a hannayenta mai nuna alamun godia sannan tasa Ζ™afa ta wuce.

tsaye yayi yabi bayan poor girl Ι—in da kallo cike da tausayawa, shin ko mike damunta oho?

kai bazai iya barinta ta tafi haka ba dan haka da sauri yabita, gabanta yasha ya dinΖ™a mata magiyan dan Allah ta barshi ya sami ladan taimakon wallahi bazai cutar da ita ba in kuma hakan ta kasance Allah yay mata sakayya tin aduniya kamin aje ga lahira.

biro da takarda daya miΖ™o mata ta rubuta masa, _bawai taimakonka ne bana so ba saboda fuskanka bai kama dana mugwayen mutane ba, da zaka cutar dani bama zaka kawo ni a asibiti ba domin aceci raina ba…kawai dai ina guje maka shiga wani hali ne ata dalilina saboda duk wanda ya kasance tare dani da sunan taimako mutuwa yake, kayi haΖ™uri na gode da iyaka taimakon da kayi mani Allah ya biyaka da gidan aljanna._

sose kalamanta suka Ζ™ara sawa yaji wani mugun tausayinta ya sake kamashi, har Ζ™asa ya zube Ζ™afafunsa ya hau mata magiya har saida ta amince.

sanyi yaji ya ratsa zuciyarsa saboda bayan taimakonta da yake sonyi kuma akwai sonta tin na wasu watanni a zuciyarsa wanda yake ganin idan har babu ita a rayuwarsa to ba lallai yaci gaba da rayuwa cikin jin daΙ—i ba.

“na gode sose da kika amince kuma ina roΖ™on Allah ya fitar dake daga cikin Ζ™angin rayuwar nan da kike ciki…yanzu mu koma ciki mu amsa magunguna dan likita yace akwai drugs Ι—in da zai Ι—oraki akai”

binsa tayi suka koma ciki duk data dameshi daya faΙ—a mata me akace yana damunta amma yaΖ™i, ahi kansa bazai iya ba saboda in har ya faΙ—a mata zai kuma iya haifar mata da wata matsala

murmushi Rahinat taΖ΄i cikin ranta take cewan, _nasan dai bazai wuce hawan jini ba ko ciwon zuciya…ni kaina in akace banda Ι—aya daga ciki to akwai ayar tambaya akaina dan ko kewan mahaifana ma kaΙ—ai ya isa ya haddasa min wani ciwo bare wannan Ζ™angin rayuwan dana shiga_.

****

kan gado ya zaunar da ita yana shafa bayanta a hankali.

bazata can Ζ™asa da mura taji yace da ita, ” are you 2wins?”

bum gabanta ya faΙ—i, _na shiga uku kar asiri na ya tonu, idan Yarima ya gane wace ni wallahi na gama kaΙ—ewa._

ganin tai tsiru tana kallon gaban rigarsa da alamu na tsoro ya talbi fuskanta tare da cewan,

“what happen Angel?”

fashewa tayi da kuka ta faΙ—a jikinsa ta Ζ™an-Ζ™amesa.

sumar gashin kanta yake shafawa yana lallashinta, “minene kuma?”

“ban santa ba tsoronta nike ji”

“to is oak daina kukan”

ta girgiza kai, “nidai kasa a Ι—auketa ko kuma mu tafi mu bar garin..kullum fa saita bani tsoro a mafarkina”

kai ya Ι—aga mata kawai sannan ya miΖ™e ya fita a Ι—akin tare da cema Nimrah ta kula da ita.

fitowansa ya dinΖ™a waigen ko zaiga su Rahinat amma baiga ko Ζ™yallinsu ba.ba.

+

tambayar Dr incharge yay yake sanar masa yanzu aka sallamesu sun tafi.

da sauri Khaleed ya fice, dai² da Ζ™arasawan fitansa dai² da zagayowan Raihan daga rufema Rahinat Ζ™ofa.

a dabarance ya Ι—aga cameran wayan dake hannunsa ya Ι—auki Raihan hoto, har lokacin da Raihan ya fice daga asibitin bai bar kallon numbar motan ba daga nan ya fuskanci ta nigeria ce..

zooming pix Ι—in yayi ya kalla sose sannan yay backward yay zooming Ι—in gefen fuskan Rahinat daya Ι—auka ta cikin window wanda bai fito clearly ba.

zuwa ga wata numba ya tura komi sannan ya nemi da akawo masa kujera.

zama yayi ya shiga online Libya TV talk,abinda ya fahimta a Ι—azun ya Ι—auke hankalin mutum biyun shi ya shiga yay search.

shiru yay bayan daya gama kalla,tinaninsa ya tafi akan to mine alaΖ™ar Angel Ι—insa da wannan mutumin har fuskarta ta bayyanar da tashin haΖ™ali da ganin gawarsa.

tinani na biyu daya fara wancen mai kama da Angel daya gani ita kuma wace daga ina take kuma itama mine alaΖ™anta da mutumin da yaga har ta zubda hawaye akan gawansa?

ya jima sose yana ta nazarin abubuwa da dama har tinkararsa da Raihan yay da neman faΙ—a that means kenan ya taΙ“a saninsa amma shi bai sansa ba.

lalle ya zama dole yay bincike akan yarinyar nan dake neman firgitar masa da Angel,in har ba aljana bace to haΖ™Ζ™un bazasu rasa nasaba da juna ba domin kallon da ya Ζ™are masu tsab ya nuna masa da kama ta jini a tsakaninsu tinda baiga Ι—aya daga cikinsu da kofato ba.

kansa ya jingina akan rocking chair Ι—in da yake zaune akai.idonsa a lumshe yake tinanin kamin wani baΖ™on al’amari ya danno kai ya kamata ya san asalin Angel Ι—insa kan su Abie suyi nasarar cin wasan da yake ganin kaman tsarawarsu ne akan halitta biyun da yagani a yanzu.

dan yana da tabbacin dan su rabashi da ita suka haΙ—a wannan plastic surgery Ι—in.

ya jima nan zaune har lokacin idonsa a lumshe kiran da Nimrah ta masa ya sanya sa buΙ—e ido ya saukesu akanta.

“Khoyaa Sister inlaw na son ganinka”

a saraucensa ya Ι—aga mata kai da nuna alaman he is coming.

shigansa Ι—akin a zaune ya tadda Raihana kishingiΙ—e da pillow fuskanta Ι—auke da damuwa.

gefenta ya zauna yana dubanta kamin ya miΖ™a hannu ya kama nata ya sanya nasa ciki.

a hankali ta buΙ—e ido ta zubesu kan halittarsa da kullum ke daΙ—a rikita mata lissafi wanda take adu’an kullum ya zama mallakinta.

kukan shagwaΙ“a zata fara ya tsaidata da faΙ—in, “mu bar nan ko?”

kai da Ι—aga masa na alaman, “ehhh”

“zamu tafi amma ki fara bani amsan tambayan da zan maki kinji”

ta gyaΙ—a masa kai kawai.

“Angel taya akai kika shigo cikin bayin masarautarmu?”

“Yarima na ka manta da tarihina plss bana son tina baya”…..

“just tell me”

ya katseta cikin tsawa.

ido tap da hawayen dake neman gangarowa take kallonsa, duk da tarihinta abin atausaya mata ne amma bazai yiwu ta bashi asalin tarihin rayuwarta ba in har ba iyayenta ne suka nemeta ba to babu wanda zai sna asalinta.

kan tayi wata magana aka buΙ—e Ζ™ofa wanda sallamar da sukaji ya Ι—auki hankalinsu.

Khaleed bai miΖ™e ba yaci gaba da zamansa amm akansa sunkuye a Ζ™asa.

Mami ta Ζ™araso inda yake zaunen tace dashi, “Aayan lalle so ya rufe maka ido ka manta wace ni a wurinka tinda har ina kiranka kaΖ™i amsa kirana saboda kana tare da azzaluma wadda ta jefa rayuwarka acikin Ζ™unci ko”ba haka bane Mami, plss you should just forget about the past, ta rigada tayi kuskure kuma ta tuba sannan nida tayiwa na yafe mata…..”

tas Mami ta sauke masa mari a fuska, “idan kai ka yafe mata toni ban yafe mata ba saboda itace silar rabani da mijina da muke matuΖ™ar sΖ™n junanmu, ta kuma gurΙ“anantar da rayuwr Ι—ana, ta rabasa da mahaifinsa…toni ban yafe mata kuma akan hakan ne zan Ι—aukaka Ζ™ararta”

taja numfashi kamin tace, “sannan idan har ka maida igiyar auren dake tsakaninka da ita Aayan to zan tsine maka kuma ni ba uwarka bace sai dai ka nemi wata uwar…..”

bata kai ga idda abinda zatace ba baiwar dake tare da ita ta Ι—aga wayanta da aka kira ta miΖ™o mata.

ganin sunan Abie tai saurin karawa a kunnenta tayi sallama wadda da kaji kasan tana Ι—auke da tsan-tsar Ι“acin rai.

“Su hana ki dawo yanzu ga yarinyar ta dawo sai dai basa tare da wuldi…shi ki Ζ™yalesa duk inda yake ma zai dawo ne indai yasan ta dawo garemu tinda ya fifitata akanmu”

tinda Abie ya fara maganar wai tazo ga yarinyar ta dawo Mami ta saki baki da ware idanuwa ne.

jin shirunta Abie ya katseta tinanin da take da faΙ—in, “Suhana bakiji nane”

“ina jinka Abu Aayan, sai dai zancen naka ne ke neman sani a ruΙ—ani”

“kaman ya kenan?”

“ehhh to aini na gama shiga ruΙ—u kuma, bari dai gamu nan zuwa in mun iso ma fahimtar da juna baki Ι—aya”

kashe wayan Mami tayi tabi Raihana da kanta ke sunye Ζ™asa da kallo, ta sanya hannunta ta damΖ™i kanta ta Ι—agota tana sake kallonta.

ita Ι—ince dai, to a’a ya Abu Aayan kuma zaice mata gata a wurinsu bayan gata ita data rayuwa da yarinya kusan shekara, toko dai yayi ne dan ya kwantar mata da hnakali ganin ta Ι—aga hankalinta na son dawo da Ι—anta da kuma hukunta shegiyar yarinyar,to amma bata yanda za’ai suyi mata irin wannan wasan.

ta shiga duhu sai kuma ta koma masarauta zata shiga haske.

dan haka da faΙ—a tace da Khaleed, “tashi kama hannun matarka mu tafi, in kaΖ™i kuma wallahi yanzu na maka baki”

ba shiri ya miΖ™e tsaye ya kama hannun Raihana ya sauko da ita daga gadon, suna gaba Mami na biye dasu a baya har suka Ζ™aras amota aka buΙ—e masu suka shiga.

koda suka riski can Ι—in Rahinat suka tarar a fada an saΖ™ale hannayenta a igiya an kuma Ι—aure Ζ™afafunta sai police huΙ—u a kewaye da ita, Abie da Papa kuma na zaune bisa kujeran saurauta.

Ζ™arasa shigowansu cikin kowa sai da yay shock saboda abinda suka gani, wanda suka tsorata duk suka miΖ™e.

shi kansa mar martaba miΖ™ewa yayi da ganin abin al’ajabi na halittar Ι—an adam guda biyu a gansa.

Abie yace da Mami, “wannan kuma fa?”

Mami tace dashi, “ina can asibitin ai ka kirani kuma muna tare da ita, to ita waccen Ι—in wace”?

Papa da Abbu suka miΖ™e, cikin faΙ—a suke ceda Khaleed, “Aayan karka rain amana hankali domin wannan shirinka ne ,wato kaje kasa anyi plastic surgery ko..to in har baso kake hukunci ya hau har kanka ba ka tantance mana asalin matarka”Abbu ban aikata plastic surgery ba kaman yanda kuke tinani, ni kaina i was shocked a time Ι—in dana gansu Ι—azu,sai dai na alaΖ™anta hakan da kamanni ne……” +

cikin doka tsawa Papa yace, “uskutt….”

sannan ya juya ga police yace, “shima ku kama minshi har ita data ke tare dashi ku wuce dasu prisone babu wani mai kawo min wasa cikin masarautata”•••••••ansa masu handcuff zasu tafi Nadiya ta taso da gudu ta zube gwiwowinta gaban Papa cikin kuka take roΖ™onsa,

“dan Allah Papa kai min rai kayi haΖ™uri ka Ζ™yalesa, kar a tafar min da miji dan Allah, tinda laifin bana sa bane ai hukunta su su kaΙ—ai, abarshi yaji da iyaka sharrinma kaΙ—ai da suka masa”

hauka tibirin Nadiya ta kama, kukanta ko kaman an kunna jiniya, koda ta shiga gaban Khaleed ta riΖ™o hannunsa tana masa surutai ya bata kyakykyawar harara ba shiri ta kauce. +

umarni Papa ya bada da a Ι—auketa a wurin, in har kuma ta musa to su haΙ—a har ita.

kowa na wurin ya nutsu saboda yanda aka ga ran mai martaba yayi mugun Ι“aci ,tinda yake cikin wannna masarauta ba’a taΙ“a kawo masa wasa da rainin hankali irin haka ba.

duk da Mami bata so ba amma taΖ™i magana tanaji tana gani aka tasa Ζ™eyar Ι—anta gaba aka wuce dasu prison.

bayan fitarsu Papa yasa aka masa magana da Raihan dake tsaye a waje.

gaban Kakan nasa ya zube gwiwoyinsa ya kwashi gaisuwa tukunna Papa yasa masa albarka.

kallon saurinyin yake da kamanni na sani kuma har yana jin wani Ι—an abu game dashi acikin jikinsa.

Papa yace dashi, ” daga ina kake kuma miya kawo cikin wannan masarauta tamu sannan aina ka samo waccen yarinyar?

Raihan ya gyara tankwashewar Ζ™afarsa yace, “Allah ya taimaki mai martaba sarki,a salina ni Ι—an wannan garin ne sai dai tin ina shekara Ι—aya a zane mahaifiyata suka sami matsala da mahaifina wannan dalili yasa suka rabu ta koma Ζ™asarta ta nigeria, inda acan na Ζ™arasa girmana bayan na gama karatuna a india na dawo kuma nai aure yanzu haka har ina da Ζ΄a Ζ΄ar shekara 4 mai sunan mahaifiyata”

Papa ya kaΙ—a kai yace, “Allah sarki…to yanzu ina shi mahaifin naka?”

“ehhh kaman yanda nace maka mun rabu dashi ne tin ina a zane to sai ayau Allah yasa na fito nemansa domin mu sami ganawa dashi nima naga mahaifina sannan na basa haΖ™uri ya maida mahaifiyata daga nan mu dawo Ζ™asarmu da zama, to akan hanyata ne na zuwa Allah ya haΙ—ani da waccen baiwar Allahn acikin wani irin mawuyacin hali na atausaya mata shine na tsaya taimka mata”

maga isar da saΖ™on maganar Papa dake gefe yace da Raihan, “to duk munji zantukanka, yanzu wanna taimako kake da buΖ™ata wannan masarauta tai maka?”

sai da Raihan ya sauke doguwar ajiyar zuciya sannan ya Ι—ago ya kalla kakansa sannan ya maida kai Ζ™asa yace,

“taimako biyu nake so wannan masarauta tayi mani wanda in har tai hakan shine zai tabbatr min kuma ya tabbatarwa da al’ummar datake mulka cewar adalar masarauta ce, na farko ta haΙ—ani da mahaifina sannan kuma ta hukuntasa akan laifin dani Ι—ansa nake zarginsa dashi na ha’intar wannan masarauta a Ι“oye…sannan abu na biyu ta tsaya tayi bincike mai zurfi akan wannan baiwar Allahn dake ta shiga tsaka mai wuya akan laifin da banata ba kamin ta yanke hukunci”

kamin Papa yay magana adalin sarki mai sauΖ™in zuciya na Ζ™asar saudiya wato Shaik Walid Ma’aruf yace,

“karka damu insha’Allahu wannan masarauta mai adalici mai albarka zatayi kaman yanda ka roΖ™a daga gareta….yanzu wane mahaifin naka kuma ya sunansa”?”Sunan mahaifina Dhameer Suhail Albannah……..”
+

ai bai Ζ™arasa ba Papa ya dakatar dashi da cewan, “kana nufin kai jikana ne Raihan Ι—an gidan Hamida?”

Raihan na murmushi ya Ι—aga masa kai yace, “ehhh nine Kaka na”

cike da jin daΙ—i da farin ciki Papa ya buΙ—a hannunsa yana faΙ—in, “

“ΨͺΨΉΨ§Ω„ Ω‡Ω†Ψ§ يا Ψ¨Ω†ΩŠ ، ΨͺΨΉΨ§Ω„”

tamkar mai sunbatu haka Papa yake maganar duk murna ta cika shi, rabonsa da samun murmushi kaman haka a fuskarsa tin alokacin da Khaleed yay fyaΙ—e ga baiwar gidan.

Raihan ya tafi garesa ya shiga jikin kakan nasa Papa na faΙ—in,

“ΩƒΩŠΩ Ψ­Ψ§Ω„Ωƒ ΩƒΩŠΩ Ψ­Ψ§Ω„ Ψ§Ω…Ωƒ Ψ§ΩŠΩ† Ψ§Ω…Ωƒ؟”

dama ni Ι—an gata ne haka mahaifina ya rabu da mahaifiyata, zancen da Raihan keyi cikin zuciyarsa kenan.

har yanzu shafa sumar kansa Papa yake, ya Ι—ago da fuskarsa yay masa sumba ta kulawa a goshi.

yana kuma shafa fuskarsa yace,

” Ψ§ΩŠΩ† زوجΨͺΩƒ?Ψ§ΩŠΩ† ΨΉΨ§Ψ¦Ω„ΨͺΩƒ؟”،

“Ψ¨Ψ§Ψ±Ωƒ Ψ§Ω„Ω„Ω‡ ΩΩŠΩƒ ،و Ψ¨Ψ§Ψ±Ωƒ Ψ§Ω„Ω„Ω‡ في حياΨͺΩƒ Ψ±ΩŠΨ­Ψ§Ω†”

sai a sannan aka shigo da Asma’u tare da Ι—iyarta dake waje.

Ummi yarinya ce mai wayo tana hangensa ta Ζ™wace a hannun Mominta ta tafi wurin Dad Ι—inta.

Raihan ya nuna mata Papa yace, “to yau ga Granny Ummi”

ta Ι—an juya masa idanu kamin tace, “rilly Dad?”

ya Ι—aga mata kai alamun tabbas, Ζ™wacewa tayi a hannunsa ta nufa Papa tare da Ι—anewa jikinsa tana, “My Granny”

Papa yana Ι—auke da ita yake sa mata albarka yana ta mata sumba.

Asma’u ma ta Ζ™araso ta zube tana kwasar gaisuwa, itama nan Papa da Papi suka shiga sanya masu albarka baki Ι—ayansu.

shiko Papa tsabagen daΙ—i yama kasa sakin hannun Raihan, faΙ—i yake yau ga jikan albarka ya dawo, ga magajin kujerata, ga adalin shugaba mai jiran gado.

cike da Ζ™asaita da kuma izza Sultana Dhameer yake shigowa cikin fadar, dan tin alokacin da labari ya riske shi kan cewar Ι—ansa ya shigo masarauta kuma Papa nata faΙ—in cewar shine sarkin gobe yake wani jinsa a sama, sarautar ta motsa.

bayan ya durΖ™usa ya miΖ™a gaisuwa ga mahaifin nasa ya nemi kujera ya zauna yanata annushuwa.

Raihan ya karkato ya matso ga mahaifin nasa, cike da girmamawa ya gaidashi sukai musabaha.

shima albarka yake sanya masu baki Ι—ayansu sannan yace da Ummi ta tazo taΖ™i tace ita sai Granny.

darawa sukai baki Ι—ayansu sannan Papa yace a sanarma da kowa yana son ganinsa a fada cikin Ζ™an-Ζ™anen lokaci domin yana so ya gabatar masu da jikansa kuma sarki mai jiran gado.

Kamal,Toufiq da Yusuf suna gefe suma suna jin daΙ—i, dan yanda suka fuskanci baΖ™on Ι—an’uwan nasu lusari ne so koda an bashi sarautar sai yanda sukai dashi shiyasa ma bazasu wani Ι—aga hankalinsu ba kaman yanda suka Ι—aga lokacin Aayan.

to batare da Ι“ata lokaci ba Papa ya gama gabar dasu acikin wannan masarauta sannan ya faΙ—i sashe mai lamba 03 da sarki ke hutawa na cikin masarauta aciki ya zama na *SULTAN RAIHAN* ,nan fa aka Ι—au tafi ana rairo waΖ™a cikin yaren larabci cikin farin ciki.Nadiya kaman ta kurma ihu a wurin ganin abinda ke faruwa, shin wannan tsohon wannan irin tsoho ne mara yafiya da mantuwa da kafiya.

yanzu kenan da gaske ya cire Aayan cikin sahun jikokinsa kuma ya bar batun sarauta atare dashi.

to wallahi koda zatai kisan rai saita Ζ™wato masu sarautarsu dan ba wanda ya dace da zama sarki sai mijinta Aayan.

har da kyautar gwal-gwal Sarki Suhail yasa akama duk wani da yake cikin fadar, banda bayi 20 dayasa aka Ζ΄anta atake alokacin duk na farin cikin zuwan Sultan Raihan.

Sarki da kansa yay ma Sultan Raihan irin shigarsu aka naΙ—a masa

bayan ko an idar da sallar isha’i aka gabatar da wata Ζ΄ar Ζ™aramar walima ta farinciki, ansha anyi Ι—a’ami kowa na jin daΙ—i, Ι“angaren su Sultana Yasmeen ma zuciyoyinsu wasai domin yanzu sun san Papa zai watsar da sha’anin bincikensa tinda har yana ambaton sati mai zuwa za’a naΙ—a Raihan a matsayin sarkin Ζ™asar Libya.

su kansu su Sultan Salman ko zuciyarsa wasai take domin kuwa tinda ragamar sarauta ta dawo hannun Ι—ansu asirinsu ya zamana a rufe, dan zasu san yanda zasu sa Ι—ansu koda asiri ne ya yanke hukunci kisa ga Khalid tinda dai har yayi fyaΙ—e..

da daddare Sultan Raihan ya fito fadawa na take masa baya zuwa cikin kurkun dake bayan gidan.

koda yaje kasa gane wace Rahina yayi ganin dukansu sun koma iri guda har sabon raunin dukan da aka masu a Ι—azu.

sai da Rahina ta Ζ™uresa da ido tukunna ya iya ganeta yace a buΙ—e masa Ζ™ofarta ya shiga.

yana shiga ta kama Ι—aga masa hannu tana tari, da sauri ya Ζ™arasa gareta, nunin da take masa ya fahimci na buΖ™atar ruwan sha ne.

take ya bada izinin a kawo mata ruwa mai sanyi a gora haΙ—e da zuma da kubza.

agaba yasa mata yace taci, ce masa tayi bazata iyaci ba dan bata da buΖ™atar komi na sawa a bakinta.

da Ζ™yar ya lallamata taci kusan rabi sannan ya umarci mutanen wurin dasu bashi wuri.

kallonta yake wadda kanta ke sunkuye Ζ™asa tana zubda hawaye.

muryarsa a sanyaye ya ambaci sunanta data faΙ—i masa a Ι—azu yace, “Rahinatu”

ta Ι—ago da Ζ™wala-Ζ™walan idanuwanta da suka koma tamkar na mujiya tsabar mayuwacin halin da take ciki na rashin nutsu.

kallonsa take tana jiran cewarsa sai taga yayi murmushi.

runtse ido tayi wasu zafafan hawayen suka kuma sakkowa.

“albishirnki?”
yace da ita.

kaΙ—a kai tayi wanda ta basa amsa da hakan na goro.

yace, “yauwa ko kefa, to smile lemme see”

ta wuya ta Ζ™aΖ™aro murmushin da bai mata kyau a yanzu tayi, duk da tana tausayin kanta amma sai taji tafi tausayin Raihan daya damu akanta da yawa yake ta neman hanyar da zai kawar mata da damuwa.

hannu tasa ta karkaΙ—a a idons aganin yayi zurfi a tinani, juyowa yayi ya kalleta yace, “what happen”?

ta kaΙ—a masa kai alamun ba komi.

hannu yasa a aljihu ya ciro wayarsa, record Ι—in da yay a Ι—azu shi ya kunna mata ta kas akunne tana ji.

tsabagen daΙ—i bata san lokacin data kusa rungumesa ba, baki kawai take buΙ—ewa tana son tayi magana amma babu daman hakan sai sabbin hawaye dake kwaranyo mata.”is ok”

yace da ita ya kuma miΖ™a mata hansky yace ta goge hawayen.

ta amsa ta goge baki Ι—aya murmushin fuskarta ya gaza Ι—aukewa.

“kinji duk yanda mukai da Abbi, bayan kin bani numbarsa na kirasa munyi magana dashi, na faΙ—a masu duk abinda yake faruwa kuma ya shaida mani gobe da yardar Allah zasu dira a Ζ™asar nan dan a daren yau zaiyi booking Ι—in komi na tahowarsu” ,

ya numfasa kan yaci gaba da cewa, “haΖ™iΖ™a Raihana ke Ζ΄ar gata ce, yanda naji muryar mahaifanki ya bani tabbacin suna cikin tashin hankali…yanzu haka ma Kakarki tin barowarki can take kwance a asibiti,ita ba araye ba ita ba’a mace ba, dan haka ki kwantar da hankalinki gobe Ζ΄an’uwanki zasu kuma zasu tafi dake dan mahaifinki zaiyi komi dan ganin ya fitar dake daga wannan hali”

tsaye Rahinat ta miΖ™e duk da jirin dake Ι—ibarta sannan ta durΖ™uso Ζ™asa, hannaye biyu ta haΙ—e tana ta wangale baki tana zubawa Raihan godiya.

girgiza mata kai yayi yace, “ba godiyarki nake buΖ™ata ba, kwamciyar hankalinki nake so daga daren yau zuwa gobe”

ta Ι—aga masa kai alamun ya gama samu, takarda ta rubuta masa ya kuma bata wayarsa taji voice Ι—in Abbinta.

kunna mata yay tana taji, sai daya tabbata ya Ι—auke mata kewa tukunna ya miΖ™e ya fita a Ι—akin.

*****

misalin Ζ™arfe 2 na dare Khalid ne kishingiΙ—e akan kujera riΖ™e da siggaret hannunsa yana zuΖ™a.

Ι—ago da kansa yayi a hankali kuma ya ware idanuwansa da sukai jawur wanda kana kallo zaka hango zallar Ι“acin rai acikinsu sai fuskarsa dake shimfiΙ—e da tsan-tsar damuwa.

ranΖ™wafa yayi yaci gaba da zuΖ™ar abarsa har sai daya zuΖ™eta tas tukunna ya yarda.

hannunsa ya aza saman sumarsa yana murzawa gami d fuszagar da zazzafar iska daga bakinsa, Angel Ι—insa kawai zuciyarsa ke ambato a duk lokacin data harba.

runtse idonsa yay na Ι—an wani lokaci kamin ya buΙ—esu a firgice kaman mayunwacin zakin daya jiyo Ζ™amshin nama.

tashi yay yana faman huci ya nufa Ζ™ofa, da sauri dakarun dake tsaron Ζ™ofa suka buΙ—e masa inda securities nasa kuma suka biyo bayansa har zuwa cikin prison.

tsit masarautar take sai masu tsaro dake kai komo, duk wanda ya jiyo motsi ya taho in yaga Khaleed ne sai ya koma ya cigaba da aikinsa.

tsakiyar Ζ™ofa biyun cell Ι—in da 2wins ke rufe ya tsaya, kowaccensu kwance take cikin uniform Ι—in prison akan gadon Ζ™arfe ta takure daga dukkan alamu ba jin daΙ—in kwanciyar sukai ba dole ne kawai ya sanya.

Ι—akunan daban-dabanne amma kuma a haΙ—e suke, ya kalla wannan ya kalla wannan haka ya dingayi har kusan mitina biyar kamin ya tsaida idonsa kan Ι—akin da Rahinat take.

umarni ya bada na abuΙ—e masa Ι—akin, suna shiga ya sanya aka malala wani tattausan carpet a dai² wurin da yake tsaye.

cikin lokaci kaΙ—an aka kimtsa wurin harda standing fan, aka kuma feshe Ι—akin da tirare baki Ι—ayansa ya hautsine da shegen Ζ™amshi.

hannu yasa ya cicciΙ“i Rahinat dake baccin wahala ya sauko da ita Ζ™asa, zama yay ya miΖ™e Ζ™afafunsa ya Ι—ora kanta akan cinyarsa.

sam Rahinat bata san anayi ba dan a wahalace take duk dake madai ta kwanta da farincikin zuwan mahaifanta a gobe, hular uniform Ι—in ya zame daga kanta wanda duk ya gama burkicewa sakamakon rashin kulawa daya daina samu.

shafa kan yake a hankali yana lumshe ido, sunkuyo da kansa yay ya juyo da fuskarta ya saita leΙ“ansa da nata ya haΙ—e.kusan miti biyu tukunna ya Ι—ago daga kiss Ι—in da yay mata tare da sauke doguwar ajiyar zuciya.

ya bada umarnin ai maza a kira masa likitan cikin gida, ba Ι“ata lokaci likita ya iso, Khalid yace dashi yay mata allurar Ι—auke zugi tukunna kamin ya fara aikinsa.

kaman shi za aima allurar haka yaji dan saida ya runtsu ido ya kwantar da kanta kan Ζ™irjinsa yasa hannu ya toshe mata kunne sannan yace da likitan yay mata.

zafin data ji kaΙ—an dan tana motsawa ta kuma lafar da kanta saman faffaΙ—an Ζ™irjinsa a dalilin daΙ—in baccin data keji da iskar fanka ke shiganta ta ko’ina.

kamar za’ai dressing Ι—in ciwon kamar baza’ai ba, dan da likitan ya Ι—auko kayan aiki Khalid zai dakatar dashi yace wai yayi a hankali karta farka.

da Ζ™yar dai ya bari aka samu akai dressing ciwukan dake jikinta.

hannunsa da nata ya haΙ—e ya damΖ™e inda Ι—umin tafin hannunta ke ratsa shi sai faman lumshe ido yake banda zuciyarsa kuma dake mugun zafi.

Ι—ayan hannunsa yake yawo dashi a saman fuskarta yana bin duk wani tabo dake ajikin fuskarta yana shafawa, tinanin irin azabben hukuncin da zaima Raihana data sanya Angel Ι—insa acikin wannan hali yake.

“soon jin daΙ—inki zai dawo my Angel, ba zan kuma barinki shiga wani halin ba tinda har na gane cewar kece ainihin Ruhina….kimin afuwa dana barki har tsawon wannan lokaci acikin wannan hali ,nayi hakanne duk dan na gane wace Raihana da dalilinta kuma nayin basaja a mtsayin ke”

shi Ι—aya yake maganarsa can kuma ya Ι—auka wayarsa ya kira wani D.P.O dayasa suyi masa Ζ™waΖ™wΖ™waran bincike.

anan D.P.O ke shaida masa cewarma ai Raihan bai mutu ba yana raye, ya sami wani ne ya maye gurbinsa matsayin shine har aka kashe shi.

amma yanzu haka yana tare dasu zuwa gobe zai fayyace masu dukkan komi kamar yanda ya shaida masu.

suna gama wayar yay ma Rahinat sabon light kiss a laΙ“Ι“anta tare da sakar sabon murmushi sannan ya shimfiΙ—ar da ita kan carpet Ι—in ya tashi ya fita yana mai waigenta.

da komawarsa Ι—akin Ζ™ullensa ya kirayi Tayseer yace ya shirya masa Visa zuwa London.

yana daga kishingiΙ—e kan kujera yake Ζ™wafar yana lissafo mugwayen iyayensa cikin ransa.

Dhameer,Baheer,Salman,Abid,Yasmeen amd photocopy of my Angel duk zaku Ι—an-Ι—ana kuwarku, duk sai kun Ζ™wammaci ina ma ba’a haifeku ba.

da na yanke shawaran Angel da kanta zata yanke maku hukunci amma nasan halin Ruhina da tausayi hakan yasa zan Ι—auketa nayi nesa da ita sai dai ta kalla azabar da zan ganawa kowannenku a vedio.

kasa jurema zaman yay ya tashi ya koma Ζ™ofan cell Ι—in da Rahinat take, kujera aka sanya masa ya zauna yanata kallon abarsa, har subhi bai runtsa ba,anata kirayen sallah yanaji amma yaΖ™i tashi sai daya ga ta motsa tukunna ya miΖ™e da sauri ya laΙ“e.

ta gefe yake kallon yanda take miΖ™ar wahala kan ta maida hankalinta kan lafiyayyen carpet Ι—in data kwana akai ga wata haΙ—aΙ—Ι—iyar standing fan na bayar da iska.

wani Ζ™ayataccen murmushi ta saki cikin zuciyarta ta ambaci, “tanku Brother Raihan”

daga nan ta miΖ™e tana Ι—ingisa Ζ™afa ta shiga toilet.shi kuma dake laΙ“e sanyayyan murmushin data yi yasa shi suman tsaye harta fito a toilet tukunna shima ya wuce zuwa masallaci.

Post a Comment for "YAREEMA KHALEED CHAPTER 4"