YAREEMA KHALEED CHAPTER 2 YAREEMA KHALEED CHAPTER 2 sai bayan da yay ajiyar zuciya sannan ya ɗago daga kwancen da yake yana murza goshinsa. + sabon envelop ya gani mai kama da irin wancan, ɗauka yay ya zaro takardan dake ciki, wannan kuma sabon rubutu ne wanda akayisa da larabci, rubutun na faɗin, _kaje ka taimaki mahaifinka domin shima suna neman rayuwarsa kaman yanda suke neman taka._ abinda yafi bashi mamaki da ɗaurin kai signg ɗin wancan dana wannan duka iri guda ne. to mi yarinyanga ke nuhi. ya take neman burkita masa tinani kodan tasan babu abinda yafi so sama da Abie shine zata ɓullo ta wurinsa… shiru yay na ɗan lokaci kamin ɗayan zuciyansa tace, “ka manta da maganar datai akan Abie saboda shi bamai yiwu bane kullum kewaye yake da matakan tsaro iriri” to taya kuma zai yarda da kalaman yarinyar da zata iya kisa ma saboda son zuciyarta? yaushema ta sami fuskar raina masa hankali irin haka? to amma taya akai tasan Angel bayan ko randa tai ganganci taɓa kayan Angel bai faɗi mata ga mamallakinsu ba bare tayi amf…