Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

YAREEMA KHALEED CHAPTER 2

YAREEMA KHALEED





CHAPTER 2





sai bayan da yay ajiyar zuciya sannan ya Ι—ago daga kwancen da yake yana murza goshinsa. +

sabon envelop ya gani mai kama da irin wancan, Ι—auka yay ya zaro takardan dake ciki, wannan kuma sabon rubutu ne wanda akayisa da larabci, rubutun na faΙ—in, _kaje ka taimaki mahaifinka domin shima suna neman rayuwarsa kaman yanda suke neman taka._ abinda yafi bashi mamaki da Ι—aurin kai signg Ι—in wancan dana wannan duka iri guda ne. to mi yarinyanga ke nuhi.

ya take neman burkita masa tinani kodan tasan babu abinda yafi so sama da Abie shine zata Ι“ullo ta wurinsa… shiru yay na Ι—an lokaci kamin Ι—ayan zuciyansa tace, “ka manta da maganar datai akan Abie saboda shi bamai yiwu bane kullum kewaye yake da matakan tsaro iriri”

to taya kuma zai yarda da kalaman yarinyar da zata iya kisa ma saboda son zuciyarta? yaushema ta sami fuskar raina masa hankali irin haka? to amma taya akai tasan Angel bayan ko randa tai ganganci taΙ“a kayan Angel bai faΙ—i mata ga mamallakinsu ba bare tayi amfani da wannan hanyar.

shiru yay yana tinane tinane kamin ya tashi, jotter da biro Ι—in hannunsa yajefar yana yamutsa sumar kansa.

wai shin wanna irin so yakewa Angel haka, yarinyar da baiga fuskarta bama kawai bayanta ya gani amma ya kamu da irin wannan zunzurun ‘kauna tata haka, to idan kuma aljanace fa kaman yanda Mami ke faΙ—i.

no hakan bazai taΙ“a yiwuwa ba,mutumce kuma mallakinsa ce…harya taka zai fice a Ι—akin wani tinani da yay ya dawo dashi baya.

pix Ι—in data ajemasa ya Ι—auka ya sake kallo…akwaifa ayar tambaya akan maganarta da kuma evidence Ι—in data aje masa… pix Ι—in asali da kuma natan ya Ι—auka yana sake kallo, sam babu alamun edit ajiki , waige² yashiga yi shifa gaba Ι—aya kansa ya Ι—aure.

fita yay Ι—aga Ι—akin, yana zuwa ya haye bike Ι—insa ya fice zuwa gidan Mami.

shigarsa Parlon Mami ya ganta zaune kan kujera ta talbi fuska da hannu biyu da alamu tayi nisa cikin tinani kuma yanayinta yay kama da wadda ke tinanin hukuncin da zata yanke kan abin daya Ι“ata mata rai.

jikinsa a sanyaye ya zauna Ζ™asa da ita, Ζ™afa Ι—aya ya miΖ™e yay tagumi da Ι—ayan hannunsa, yanzu in ya zama da gaske Angel Ι—insa ce ya kenan, duk abinda ya mata a baya Angel Ι—insa ya cutar bayan irin tanadin da yay akan ko Ζ™uda bazai taΙ“a bari ya taΙ“a masa ita ba ,kai iska ma mara kyau bazai taΙ“a bari ta kusanci inda take ba.

Mami ta katse tinaninsa da yake “yaushe ka shigo?”

“tin Ι—azu” yace da ita da muryar damuwa.

“ina umarnin dana baka”? ta tambayeshi yayin data miΖ™e tana yafa lafaya.

shiru baice komi, ta kuma yanke tinaninsa, “Aayan da kai nike fa, ina takardar sakin matarka”

“ban rubuta ba Mami”

cikin tsananin Ι“acin rai da bazai misaltu ba ta hausa da faΙ—a ta inda take shiga bata nan take fita ba kamar zata dukeshi..ayanda takeji ko da Khalid zai zama gawa ne ayau sai yasaki Rahinat.

shiko baki Ι—aya ya rasa mike masa daΙ—i, moment Ι—in baya yake tariyowa da kuma letter Ι—in data aje masa dan sam baima sauraron abinda Mami ke cewa.

cikin tsawar data gama rikiΙ—a hanjin cikinsa tace, ” bazaka saketa bane ko kuma kana so kace mani kana tausayin mutumin daya tarwatsa farin cikin rayuwarka ya Ι“ata maka suna a idon duniya…ko kuma ita matar taka ka fara so? to wlh Aayan idan son yarintar nan ka fara to ka ajesa domin bazaka taΙ“a ci gaba da rayuwa da ita ba koda zaka mutu…takardar saki kuma dole ka rubuta kaje ka kai masu…Aayan duk duniya babu mutumin dana tsana sama da Rahinatu….”

ta koma ta zauna inda ta fashe da kuka.

jiki ba Ζ™wari kaman wanda yay cuta ya tashi yaje kusa da ita ya riΖ™o hannunta.

“dan Allah Ummi nah kiyi haΖ™uri ki mani afuwa….zan saketa kaman yanda kika bani umarni amma ban san mi yasa na kasa ba”

ta miΖ™e taje ta Ι—auko masa takarda da biro ta bashi, tace” idan har na isa da kai kuma ni na haifeka to ka saki rahinatu domin bata cancanci zama matarka ba”

“Mami kar mu yanke hukunci cikin fushi daga ni harke muzo gaba muna dana sani…na roΖ™eΖ™i kimin alfarma zuwa na Ι—an lokaci domin nayi wani bincike.”

“bincikenka Ι—in banza dana hofi, bincike ya wuce wanda ka Ι“ata shekaru 5 kanayi dan gano wanda ya Ζ™ulla maka sharri har yana neman rayuwarka a hannu…. Aryan koka manta nike auren Rahinata bakai ba saboda ni na auro maka ita, idan har baka aikata abinda na saka ba saina Ι“atamaka….in ko bakai wasa ba zaka biyani nono na daka sha, Khalass”

hannu na rawa yay saurin Ι—aukar takardar ya fara rubutu gumi duk ya keto masa.

yana rubutun yana tina kalaman Rahinat, kasoni batare daka san koni wace ba haka ka Ζ™ini batare da kasan wa nike a zuciyarka ba….karkayi shakku da kalamaina dan Allah Khalid wlh nima ina sonka kuma wlh bazan yaudareka dan ka soni ba saboda nafi son soyayyarka ta gaskia.

lokacin daya gama rubuta saki Ι—aya gaba Ι—ayansa ya jiΖ™e da gumi, haΖ™iΖ™a son yarinyar badaga shi bane ,sone da tini aka halicce shi dashi a jinin jikinsa.

ya naΙ—e takardar ya miΖ™ama Mami yace gashi, bata kalle shi ba tace yaje ya kai masu idan ya dawo ya wuce airpot domin zasu wuce saudia.

yaji daΙ—i da bata amsa takardar ba gudun karta ga cika Ι—aya saΙ“anin yanda tace mashi.

haka ya tashi ya fita har yana haΙ—a hanya sakamakon blind love Ι—in daya kanainaye jijiyoyin jikinsa.motar ma sai sai security Ι—insa ya taimaka masa ya shiga, Ζ™aΖ™Ζ™arfa ne a komi amma wck Ι—insa a so yake.sai daya kira Mami ta masu kwatance sannan ya iya zuwa gidan danshi bai san hanyar bama.

koda suka isa mai gadi ya bama takardar ya miΖ™a cikin gida daga nan kuma yace da driver ya wuce dashi gidan Khalil.

ganin a halin daya shigo Khalil ya taimaka masa da siggaret koya ji sauΖ™i, kusan kwali guda ya zuΖ™e cikin Ζ™anΖ™anen lokaci kamin ya Ι—ago da raunannun idanunsa ya kalla Khalil.

gyaΙ—a masa kai Khalil yay ya tashi ya Ι—akko giya ya bashi yasha, yana gama sha bacci kuma ya Ι—aukesa, kusan awa 7 yana bacci sannan ya farka,bayan ya farka yake sanar da Khalil halin daya ke ciki.

Khalil yace ya zauna yay nazari da duba sose , yanzu haka yarinyar wuyar data ke sha wurinsa yasata yin tinanin da zata juyar da hankalinsa, haka dai Khalil yay ta bashi shawara akan karya soma ya yarda ya tina fa itace yarinyar daya fi tsana kuma ita mace ta farko data taΙ“a nuna tsantseni akansa sannan kuma ya tina Angel fa na delhi ba wai nigeria ba.

a daddafe ya Ζ™arasa gida, shaf ya manta da batun Mami na inya dawo ya wuce airpot, sai daya diba waya yaga tarin miscalls Ι—inta tukunna ya tina.

nan yay wanka ya shirya ya fito ya wuce, acanya samesu da zuwansu jirgin nasu ya Ι—aga zuwa Ζ™asa mai tsarki.

tskanin Ι—a da mahaifa sai Allah, yanda Mami taga duk yanayinsa ya sauya sai ta shiga lallashinsa, “Aryan ka saki jikinka dan Allah kasan bana sonka cikin damuwa, ni ina mai tabbatar maka babu dana sani a hukuncin da muka yanke ko kaΙ—an”

Ι—aga mata kai kawai yay, abinda Nimrah tace ne ya juyo ya wurga mata harara sai kace ya tabbar da gaske Angel Ι—ince.

“nifa wlh Mami na tsani Rahinatu, kuma insha’Allahu barin gidan da tayi ma shine silar mutuwarta, muguwa azzaluma kawai ta Ι“atawa Khoyaa suna ta rabashi da Abie”

“kwantar da hankalinki Nimrah ai harma na shigar da Ζ™ara kuma na aikawa da Abie vedion, matsawar ina raye bazan taΙ“a bari a zaluntar mani Ι—a ba sai nabi masa hakkinsa”

ya gimtse idonsa bai buΙ—e ba har suka iso saudia, haka dai daka gansa kasan yana a damuwa.da suka isa masarautama ana yowa kansa ya dakatar da kowa ya wuce sashinsa ko fadar Abbu bai leΖ™a ba.

karo sukai da Taysir a wurin shiga, ya kaikaito da kai yace masa, “yi haΖ™uri dan Allah”. karo na farko da Tasir yaji khalid yabada haΖ™uri a rayuwarsa.

duk daya san miskili ne amma yanayin daya gansa yasan cewar akwai damuwa tare dashi damuwar ma kuwa babba.

shima bai saurareshi ba yay turakar Maamaa, bai sameta acan ba saboda sun wuce sashin kakan nasa.

ya jima acan suna gaisawa da Mami saboda tin biki rabuwarsu da haΙ—uwa, anan ya tarar da maganar da suke tattaunawa na game da yarinyar datai Ζ™azafi ga Khalid kuma yanzu harta na bayyana masa cewar zasu kasheshi.

daya dawo Ι—aki kwance ya sami Khalid kan gado yana kallon sama..taΙ“osa yay yace , “Man wai ya dai naganka yau sai a hankali duk da dama haka kake”mutumin da sai ya Ι“ata lokaci yake reply amma farat Ι—aya yace masa, “Taysir Angel, Angel Ι—ina…kasan labarin soyyta ka kuma san yanda take…syyta itace rauni na duk mazantakata…. na kasa yarda Angel Ι—ina ce na kuma kasa Ζ™in yarda da hakan saboda nasan Angel bazata taΙ“a Ζ™arya ba….gaba Ι—aya na rasa wanna irin tinani zanyi Taysir “

“Relaxx Man” Taysir ya faΙ—i yana dafa kafaΙ—arsa.
“Man believe me itace Angel Ι—inka fa”

Khalid ya Ι—ago yana masa duban ????, Taysir ya Ι—aga masa kai yace “Ζ™warai kuwa sai dai in karka yarda…kasan ni lauyer ne right? ka kuma san yanda nake zurfafa bincike akan abu ko…to a Ι—azu kamin ku iso Mami duk ta aiko mani da recrd na CC Ι—in gidanka….am sorry 2say a Ι—azu na kalla inda bai kamata na gani ba amma ya kama dole ne tinda ta hanyar bincike ne…Man yarinyar dake mugun tsoronka da shakkarka bazata taΙ“a wasa da hankalinka irin haka ba…sannan shaidar Ζ™arshe da zan baka wadda akanta na tsaya itace wannan”

ya miΖ™amasa vedion daya kunna, time Ι—in data shigo Ι—akinsa gyara, ta Ι—auka bangle Ι—in ta saitashi ne da ring Ι—in dake Ζ™aramin yatsanta wanda ya bada tabbacin wannan ring Ι—in na bangle Ι—inne shine har take cewan wannan ai kaman bangle Ι—ina daya Ι“ata tin a delhi saboda jan zaren data gani ajiki wanda Ammi ta Ι—aura mata gashi kuma ajikin zoben nata again, sai ta aje kawai ta Ι—au haramar aikinta sai kuma can ta tsaya tana tina wani abu shine tazo ta Ι—auka ribom Ι—in tai tsaye shiru kamin ta fara tina maganar Nimrah….

rigar baccin da take sanye da ita a time Ι—in show ne ce, cikin tsananin ruΙ—u da tashin hanΖ™ali Khalid dake kallon Vedion ya miΖ™e tsaye sakamakon ganin lafceciyar tawadar Allahn daya gani a bayanta wadda tai circle, babu shakku Angel ce wannan sai ayanzu ya Ζ™arama tabbatarwa saboda side view Ι—in wuyanta ma daya sake gani mai Ι—auke da tabon Ζ™una.

yatsansa na rawa yakema Taysir nuni yana murmushi, ” wlh itane ,wlh Allah itane, waΙ—ann sune proof Ι—in da nike faΙ—in ko a filin arfa zan fiddo da Angel Ι—ina, abu guda yanzu ya rage the extra digit finger(postaxial polydactyly) dana ganta dashi amma ita anyi surgery Ι—insa”

maganar yake murna duk ta gama cika shi dama zai sake ganinta Ι—in da gaske kaman yanda yake drmng kullum.

vedion yay rewrding baya, fuskarta yake kalla sose baki washe Ζ™ayataccen murmushin fuskarsa kuma ya gaza Ι—aukewa, a hankali ya lumshe ido ya buΙ—e ya Ι—an cije lips ya furta, “Cute face queen of king”
fuskar tata tai masa azabar kyau kaman ta lovely tah Ummu Nabil.

can kuma ya dakata jiki a matuΖ™ar sanyaye da fuskar nuna damuwa yace,
” yanzu kana nufin Taysir duk abinda na aikata a baya Angel nayima shi”

“tabbas”

kamar zai kuka ya shiga girgiza kansa,

” i will neva forgive my self har saina dawo da Angel gareni kuma na nemi afuwan abinda na aikata mata sannan ta yanke kowanne irin hukunci taga dama akaina”

ragon namiji a fannin so kenan wato Yarima Khalid??, idonsa ya matse sose ya dafe kai saboda ya daina ganin abubuwan da duk suka faru a baya.

Taysir ya dafasa yace, “kace ta yanke maka ko wanne irin hukunci ko, koda na rabuwa da kaine”…..

ai bai Ζ™arasa ba Khalid ya kaishi bango, “karka sake cewan zata rabu dani, Heenat will neva leave me saboda tana sona”

“soyayyar da take maka a bayana ne Man amma banda yanzu, ko ka yarda ko karka yarda soyayyarka a zuciyarta a baya ne yanzu babu ita….ko ka manta da maganganun data faΙ—a maka ne a baya ,koka mance cewan ita ta nemi saki da kanta daga hannunka tin kamin ka furta mata, ko ka mance tace bazata Ζ™ara dawo garekeka ba kuma bazaka Ζ™ara ganin……”

naushin daya bashi a baki ne yasanya shi haΙ—iye sauran jawabansa.huci kawai Khalid ke akansa ya kasa magana,Taysir da zafin nama ya Ι“arar da hannayensa daga shaΖ™ar kwalarsa da yay.

“mtswww ni nace ka aikata abinda zai sanyaka dana sanin da zaka zo ka juye fushinka akaina ko kuma ni na Ι“ata maka….kai nama faΙ—a Ι—in na kuma na faΙ—a yarinyar nan bazata taΙ“a zama mallakinka ba a karo na biyu….ai ita ba jaka bace duk wuyar daka bata a baya sannna ta kuma dawo ma maka” +

Khalid ya haΙ—iye wani yawu mai zafi sannan ya Ι—ago da jajayen idanunsa ya kalla Taysir yana nunasa da yatsa.

da muryan Ι“acin rai yace masa , “kar dai ka kuskura ka faΙ—i wata kalma mara daΙ—i akanta in ba haka ba yanzu ka baΖ™unci lahira”

Taysir yay shiru bai kulasa ba dan yasan kaΙ—an daga cikin aikinsa, komawa yay ya zauna yaci gabada binciken da yake akan wani issue na yarinyar da akama fyaΙ—e aka kasheta.

shikam Khalid ficewa yay Ι—aga Ι—akin, fadawa na ganinsa suka bi bayansa dan take masa amma duk ya dakatar dasu.

motar da Abbu ke fita acikinta Ζ™irar rolls royce ya nufa, da sauri dogarai suka zo dan buΙ—e masa ya Ι—aga masu hannu, hannu ya miΖ™a ya amsa key Ι—in,zai shiga muryan Mami ta dakatar dashi.

bai juyo ba ya tsaya yana jiran cewarta.
“ina zaka haka?”

“neman Angel Mami”

Ζ™arasowa tayi ta juyo dashi suna facing juna, kallonsa take kallo na kamar bai hayyacinsane ko kuma ya haukace.ita fa tsoron wannan aljanar data shigo rayuwarsa take karta zautar mata da yaro,shekaru nawa yau yaΖ™i mancewa da ita.

“to yanzu da zaka tafi nemanta ina zakaje bayan bakasan taΖ™ameman inda take rayuwa ba…Aayan….”

“Mami Angel ba kowa bace face Heenat”

ta tambayesa , “wace kuma Heenat”?

” Ψ±Ψ­ΩŠΩ†Ψ© زوجΨͺي “

ta kifeshi da mari, “wai hankalinka Ι—aya kuwa, wacce iriyar maganar banza kake yi, shekara nawa ka Ι—auka kana neman yarinyar data Ι“ata ka sannan kuma gano ka barta tasha, ko ka mance ata dalilinta kai zaman prison ka kusa Ι“ata kyakykyawan tarbiyarka ka sauya Ι—abi’unka masu kyau…… oak kana nufin idan itane Ι—in zakaje ka nemeta ne”

“ehhh Mami saboda soyayyarta tarin jayi Ζ™iyayyarta….da ace tin farko nasan itane to dana manta da komi na mance da faruwar komi, zaman prison dama can rubuce yake sai nayi rayuwan ciki…Mami abinda tayi fa b ayin kanta bane kuskure ne kowa na aikatawa, ki barni naje nemanta dan Allah, rayuwata zata cika ne idan har kawai da ita”

“Mami ga kiran Abie ,yace karku wahalar da kanku domin yarinyar yanzu haka tana wurinsu a tsare kuma tana gab da fuskantar hukunci dai² da abinda ta aikata daga masarautar Abu Mourad Albannah , sannan kotu bazata bar fushi da ita ba har sai lokacin data faΙ—i waΙ—anda suka sanyata suma an hukuntasu, yanzu haka Sarki yasa a jefeta idan har bata faΙ—i b a gobe saboda wannan shine mafi girman laifi da aka taΙ“a aikatawa acikin masarautar dan ta tozarta sarki gobe mai jiran gado….”

“a jefe wa? u mean zasu jefe mani Angel, to kayi gaggawar sanar dasu kar wanda ya sake ya taΙ“ata har lokacin da zan isa idan ba haka ba kowane sai ya kuka da kansa”

ya faΙ—i yana zazzarewa Taysir ido ga wata uwar shaΖ™a daya bawa wuyansa kuma yaΖ™i sakinsa, Taysir ko sai kakari yake saboda maΖ™urar daya sha banda Ι—ishi² ba abinda yake gani.

ya shiga girgiza sa da Ζ™arfi yana faΙ—in, “ka kirasu ka faΙ—a masu kar wanda yay yunΖ™urin aikata mummunan abu akan Angel, su dakatar da shirin abinda suke aikatawa,laifi ne ni akamawa ba wani ba, kar wanda yay gangancin taΙ“an mata”

kowa Ζ™oΖ™arin Ζ™watar Taysir yake amma ya kasa , daka kawo hannu zai mangareka, Mami kam gefe ta koma tana kuka saboda kisan da Khalid ke shirin yi gashi yaΖ™i ji yaΖ™i gani.

hargitsatstsen marin da Abbu ya saukar masa a kunci ne yasasa sakinsa batare daya shirya ba nan Taysir ya koma gefe yana maida numfashi.

“dama baka da hankali Aayan, Ι—an uwan naka zaka kashe da hannunka”

“Abbu bakaji abinda yake faΙ—i bane akan matata”

“toni na faΙ—a, ba aikoni akai ba”
Taysir yay maganar shima yana huci cike da jin haushin Ι—an uwan nasa.

“shikenan kar Allah ya baka ikon yin shiru Ι—ora daga inda ka tsaya”

sanin hauka irin na Khalid akaja Taysir baya saboda yanda ya nufosa a fusace yana muzurai.

“ahaka zaka mulki wasu, to bari kaji mai saurin zuciya baya iya zama shugaba… shikenan kaje ka aikata son ranka Aayan tinda kai babu wanda ya isa ya faΙ—a maka kaji”cikin ransa yake faΙ—in shifa baya son yana abu tsohonnan ya shiga ciki, Ζ™wafa yay banda Abbu a wurin da sai ya dagargaza bakin Taysir, yana huci yay motar ya buΙ—e , zai shiga ya jiyo yana korawa Taysir kashedin, +

“kuma ka sanar masu matsawar aka cutar min da matata koda Ζ™warzane saina tashi Ζ™asar Libya baki Ι—ayanta.”

yama manta da idanun su wane a wurin ya shige ya banke Ζ™ofarsa yabama motar wuta zuciyarsa cike da zullumin son ganin halin da Angel ke ciki yana kuma tamin Ι—in irin hukuncin dazai wanda duk ya taΙ“ata.

yana isa airpot ya wani fito yashige jirgi ya tashi dashi zuwa Ζ™asar Libya.
kansa bisa kujera daya kwantar yake tina lokatan baya, babu abind aketa faΙ—o masa sai abu biyun nan ,lokacin datai gudun mage ta shige jikinsa da lokacin fito a toilet da gudu tana ihu kumfa duk jikinta.

wani dadΙ—an numfashi ya saki sai leΙ“ensa dake motsawa, wato shiyasa yaji ya tsani magensa alokacin har yay sadaΖ™a da ita duk da bala’in son da yake mata…. murmushi mai kama da dariya yay a hankali ya furta “My Agel fear fear”

ji yay baki Ι—aya ya Ζ™osa ya dira a Ζ™asar.

ita kam Mami bayan fitarsa kuka ta saka saboda tsoro da fargabar abinda ka iya zuwa ya dawo.

****

ba sakin Rahinat ya Ι—agawa Hajia hankali ba, babban tashin hankalinta kalaman Ζ™arshe daya rubuta watanni bakwai kenan da guduwar Ι—iyarsu suje su nemeta.

koda ta kira Abbi ta sanar masa yace shi ba ruwansa ai dama ya faΙ—a mata duk matsalar data biyo baya to kar asoma nemansa.

Ι“angaren Ammi kam kuka ta sanya a lokacin, tana zubar hawaye take ceda Abbi yanzu itama ka yarda mu rasata kamar yanda muka rasa Raihana.

duk da Abbi ma cikin tashin hanΖ™ali yake amma sai ya dake yace , “ai ita Raihana ba bijire mana tayi ba tabi son zuciyarta kamar yarda Ζ΄ar uwarta tayi ba ,ita mutuwa tayi, wataΖ™ila da tana nan data kore min baΖ™in cikin da Rahina ta sanyani ciki, Allah yafimu sonta shi yasa ya amsa abarsa tin tana jaririya”

“duk da haka Abbi, kar fushi yas aka manta matsayin da zuciyarka ta bama Rahinat”

saboda karta sa zuciyarsa ta tsinke ta raunana Abbi ya tashi ya fice a gidan, office ya wuce idan ya Ζ™ulla kansa, hular kansa ya cire cikin zuciyarsa yana adu’ar Allah ya kiyaye masa Ι—iyarsa a duk inda take..

*****

Nawwara ke zaune kusa da Anty, dafata tayi tace, “Anty wai lafiya tin Ι—azu na ganki cikin damuwa”

Anty Asma’u da duk tabi ta ruΙ—e ta kalleta tace, “ba komai, kinga sake kira min numbar Hajia Saddiqa”

“wacce Anty”

cikin tsawa tace, “Hajia Saddiqa shugar gidan marayun pataskum mana wanda Engnr Faruq Adam Modibbo ya buΙ—e”

“O na tinata amma kaman ta sauya numba bari na duba a whatsapp Ι—ina”

“ke dalla malama kiyi min da jiki ko kuma ranki yay mugun Ι“aci wlh…kin san meke shirin faruwa dani ne”

jiki na rawa Nawwara ta Ι—au wayarta ta shiga laluban numban Hajia Saddiqa babu tace Anty nifa banda tata saita matarsa Ζ™awar matarsa Hajia Hidaya.

“dan uwarki wai ni su nake maki magana, ki duba wayata mana akwai numbar ki sake kira kiji, ni na kira bata shiga ba”

nan Anty taci gaba da safa da marwa a tsakiyar parlon, tana jin sallaman Uncle Badamasi ta kuma ruΙ—ewa dan sai taji kaman ta Abbi.

****
tsaye su Sultana Yasmeen suke cirkocirko cikin asibitin Tripoli Central hospital Libya kowa da abinda yake saΖ™awa cikin zuciyarsa.

tinda labarin Ζ™ullinsu yaje kunnen Sarki Suhail suka shiga tashin hankali, fargabar da suke ciki idan yasan su suka aikata, lalle matakin da zai Ι—auka akansu mummuna ne kaman yanda yasha alwashin jefe ko wane.

Sultan Dameer ya katse tinaninsu da faΙ—in, “nifa bana jin komai, ruΙ—anin da nake ciki kawai nake so na fita daga ciki”

Sultan Salaman yace, “nima shi kawai nake so a fitar dani saboda dashine kawai zamu tsira…shin wacce yarinyar ce ta asali ,tamu ko kuma tasu?”

Sultan Baheer yace, “tamu itace feck tasu kuma original zasu raina mana hankali ne kawai”

Sultan Abid dake da zurfin tinani yace, “tamu itane bata asali ba tasu kuma ta asali….mafita Ι—aya mu kashe wannan ta wurinmu”

Sultana Yasmeen tai caraf tace, “dai dai kenan, muna kasheta kasheta mu yaudaresu da gawarta domin nima nafi tinanin ta wurinsu itane ta gaskian tinda har suka Ζ™i tsaurara bincike bayan mun Ι—auke wadda suka sauyawa kamanni” +

“to yanzu ya za’ayi kenan?”
Dameer daya fi kowa Ζ™wallafa rai akan sarautar ya fadi.

Sultana Yasmeen ta daki dariya sannan ta zaro wata allura daga jikinta tace, “wannna itace allurar gubar dana daΙ—e ina ajiya dan kashe Mourad ko kuma Ι—ansa amma yau zan kashe baiwa da ita saboda bana so asirinmu ya tonu dan daga lokacin da Maimartaba yasan dasa hannunmu to tabbas ranar na lahira zaifi mu jin daΙ—i”

tana murmushin mugunta tai room Ι—in da Rahinat ke kan gado kwance drip na shiga jikinta.

****
Abie da Papi ne zaune kan kujera gaban gadon Raihana dake kwance itama.

gefe kuma police ne tsare da asalin drcter Ι—in dake kula da Rahinat lokacin datake hannun Abie.

tsawa sojan ya daka masa sannan ya saita drcter Ι—in da bindiga yace masa, “zaka faΙ—i mana dalilin daya sa ka mata alluran bacci kuma ka faΙ—i wanda ya saka ko saina Ι“ula kanka”

jiki na Ι“ari yace, “wlh ban mata alluran bacci ba tin ta farko dana mata kuma ai ta farfaΙ—o, ban san wa yay mata ta yanzu ba sai dai idan a lokacin da aka kawo harin nanne”

sai yanzu Abie yay tinani yace, “Ζ™warai zai iya zama haka tinda da suka shigo basu mata komi ba kenan alluran kawai suka mata”

Ran maimartaba matuΖ™ar Ι“ace yace, “bazan taΙ“a barin wanda ya nemi ya cutar da jikan dana fi so ba….itama wannna Ι—in ku kasheta bana buΖ™atar farfaΙ—owarfa, su kuma da sannu asirinsu zai tonu suzo hannu na , mai jiran gado ya masu duk hukuncin daya ga yayi daidai dasu”

Abie ya miΖ™e yana lallashin Papi yana kwantar masa da zuciya kan karsu kashe yarinyar yanzu saboda idan sukai haka sunyi abinda waΙ—ancan suke so.

****
Khulaid yana daga tsaye tin a Ι—azun yana kallonsu Sultan Baheer saboda ya jima yana bibiyarsu tinda suka sace Rahina.

yana ganin sun wuce zuwa room Ι—in da Rahinat Ι—in ke ciki ya saurin zira labcourt tare da face mask sannan ya sanya gloves wuyansa kuma saΖ™ale da stethoscope yabi bayansu zuwa ciki dan yasha alwashin bazai taΙ“a bari wani abu ya sami Rahinat ba saboda baya son ya rasa Raihana, kamar yanda ita Raihana ke son raba Rahinat da Khalid dan Aayan ya zama mallakinta…
.

yana shiga room Ι—in ya tadda Rahinat cikin hali na ban tausayi wanda duk mai imani zai zubar mata da hawaye.

akan gadon take kwance kowanne sashi na jikinta ciwo ne ajiki duk jini ga Sultana Yasmeen ta toshe mata baki da hanci sai Ζ™oΖ™arin Ζ™watar kanta take shi kuma Sultan Dameer ya fito da allurar zai tsira mata ga Sultan Salman ya riΖ™e Ζ™afafunta.

“ku dakata” shine abinda Khulakd yace dasu yana Ζ™arasawa wurin nasu da sauri.

sakinta sukai suka jajja da baya shi kuma ya ruΖ™o Rahinat dake miΖ™o masa hannu.
idonta duk ya firfito waje hawaye na bibiyar kuncinta bakinta sai rawa yake, shi kansa bai san lokacin da hawayen suka zubo masa ba ,ji yayi dama basu bata maganin da suka bata ba na hana magana tsawon lokaci.

hannuΙ“ta dake ta rawa ya riΖ™e gam yana , “kwantar da hankalinki babu abinda zai sameki kinji tinda har nazo gareki”

taji duk mai yace sai dai babu bakin mayarwa sai kallo data bisa dashi, Sultana Yasmeen taja dogon tsaki tace da Khulaid, “ka matsa a gunnan ko kuma yanzu nasa dogarai suyi min waje dakai

Sultan Abid yace da ita, “a’a ba haka za’ai ba Yasmeen ai tinda ya ganmu asirinmu ya tonu , yanzu mafita Ι—aya mu sayeshi shima”

nan gaba Ι—ayansu suka masa alΖ™awarin billion ashirin tare da mallaka masa tarin kadarori.

tsaye yayi yana nazari da tinani kamin ya juya ya kalla Rahinat data cikwikwiye a bayansa sai ajiyar zuciya take fitarwa.

tausayinta ya kamasa sose bazai iya bari su kashe baiwar Allahn da bata da laifin komi ba sannan kuma bai iya jin zai sadaukar da soyayyarsa saboda kuΙ—i ba.ganin yana neman Ι“ata masu lokaci da banzan tinaninsa suka makeshi ya zube Ζ™asa, ita kuma Rahinat Sultana Yasmeen ta shaΖ™i wuyanta. +

****
kamar baΖ™o yake kallon Ζ™asar tasa tinda ya fito daga cikin jirgi, ji yay iskar duniyar ta sauya masa gaba Ι—aya.

tsaye yay yana kalle kalle, bugun zuciyarsa ne ya Ζ™aru a lokaci guda fat fat, tinawa da Angel yay saurin nufa mota aka jashi.zaune Raihan yake cikin wani haΙ—aΙ—Ι—en parlo na alfarma kansa jingine da kujera idanunsa a rufe.
wata Ζ΄ar Ζ™aramar yarinya ce tazo wurinsa tare da kiran sunansa, “Dad” +

Ι—agowa yay tare da sauke idonsa kanta yana mata murmushi, hannayensa ya buΙ—a mata ta shige jikinsa tana dariya.

kiss ya mata a kumatu sannan yace, “Ummi nah ya akai

Tana masa shagwaΙ“a tace, “Dad muje park ka jima baka kaini ba”

“angama Ζ΄ar gidan Dad, maza jeki ce da Momi ta shiryaki mu tafi”

“Dad harda Momi zamu tafi?”
“ehh harda ita, kice mata itama tayi kwalliya mai kyau”

da gudu ta tafi tana “tom Dad kaima kaje ka shirya”

ajiyar zuciya ya sauke gami da shafa goshinsa,shin har sai yaushe zai bar tinanin wannan yarinyar ne,wannan shi ake kira da ƘADDARAR SO,haΖ™iΖ™a sonta ya masa wani mugun kamu mai wuyar fassaruwa wanda shi kansa bazai iya misaltawa ba, babban tashin hankalin daya ke ciki a yanzu na rasa taΖ™amaime a inda zai sameta, ya koma ruga yafi sau goma amma kullum labarin da Baba Hardo yake bashi basu sami labarinta ba.

yana tsaka da tinani Asma’u ta taΙ“osa dan tin Ι—azu take wurin amma bai san tazo ba.

kan cinyarsa ta zauna a shagwaΙ“e tace, “Handsome nah wai dan Allah mike damunka da kake Ι“oye mani, ka diba fa yanda duk kabi ka rame saboda yawan tinani, ko wani abin ya faru a office ne?”

ya kaΙ—a mata kai Ι—auke da damuwa yace, “babu komi Swthrt Ι—ina, karki damu kinji”
yay maganar yana shafo kumatunta.

fuska ta yamutse tana shirin kuka cikin shagwaΙ“a tace, “ni dai Allah na gaji da faΙ—in ba komi, ina fa lissafe 7month kenan da sauyawar walwalarka”

kauda zancen yay da Ι—aukanta yana, “mutum shidai yafiya shagwaΙ“a”

ta saΖ™alo da hannayenta wuyansa tana dariya tace, “to idan ban maka ba wazanma handsome Ι—ina
tai maganar tana bashi light kiss a lips Ι—insa.

murmushi yay tare da mayar mata nasa a kumatu, a tsakiyan Ι—akinsa ya ajeta ya kamo weast Ι—inta yace, “Swthrt kin san mine”?

tace dashi “a’a saika faΙ—i”

Ι—an matse ido yayi yace da ita, “swthrt ina son ganin mahaifina, rabona dashi tin ina Ι—aure a tsumma, yanzu lokaci yayi da zanje innemesa”

“to kana ganin Hubbi zata bari”
“swthrt idan na daka ta Hubbi bazata taΙ“a yarda ba, kuma har abada bazata sakko daga fushin da take dashi ba duk da cewan shine da laifi tinda ya Ι—auki SON ZUCIYA(sanaz deeyah) ya Ι—aurawa kansa bayan ya san cewan mulki da saurata duka na Allah ne, wayonsa ko dabararsa bazasu taΙ“a bashi ba, koya manta idan ya kashe shima kasheshi za’ayi, ni Ι—in dayake taΖ™aman ya haifa sam bana sha’awan saurauta ko an bani bazan amsa ba, ina son ganinsa koda sau Ι—ayane Swthrt, ki bani Ζ™warin gwiwa kinji matata”

tace dashi, “ina goyon bayanka Handsome Ι—ina, ya kamata ace kaje ka gana da mahaifinka, kai rayuwa dashi kaman yanda sauran Ζ΄aΖ΄a ke rayuwa dana su mahaifan suji daΙ—i…. to amma ni tinanina abinda zamuce da Hubbi”

yace da ita, “kawai na yanke shawaran zance mata zamuje london, duk da ban san inane ba amma nasan Ζ™asar libya ne kuma cikin masarauta”

“hakane kayi tinani mai kyau, yanzu yaushe zamu tafi”?

yay murmushi sannan yace da ita, “baki buΖ™atan haΙ—a mana komi kin san mu dama already visa Ι—inmu koda yaushe a shirya take, zadai muje ne yanzu muyima Hubbi sallama nasan zamu sha faΙ—an bamu sanar mata da wuri ba”

tai murmushi itama tace, “Allah yasa dai kar tace tare zamu tafi dan kasan bata son muyi nesa da ita”miΖ™ewa tayi taje ta shirya cikin Ζ™anΖ™amen lokaci, data dawo Ι—akinsa shima harya shirya cikin haΙ—aΙ—Ι—en farin boyel mai kyau wand aya amsa farar fatar jikinsa. +

Ummi ce ta Ζ™arasa wurinsa da Ι—an gudunta tana “Dad mun shirya kazo mu tafi”

itama Asma’u da kwaikwayon Ζ΄ar tata ta Ζ™arasa garesa tana “Dad kaifa muke jira”

yay dariyar farin ciki ya rungumeta jikinsa yana shafa Ζ™aramin cikin data ke Ι—auke dashi yace, “Swthrt kiyi min adu’a Allah yasa na sami abinda zuciyata take nema domin ina jin ajikina tafiyar nan da zanyi alkhairi ne agaren, dmauwar da nake ciki zata yaye”

da rashin fahimtar zancen nasa ta Ι—ago ta dubesa kana tace, “kaman ya abinda zuciyanka ke so da kuma damuwan da kake ciki?”

sam ya manta yay wanan katoΙ“arar, cicks Ι—inta ya kama yace, “kewar mahaifina na mana”

nan ya kama hannunta dana Ζ΄ar suka fita dgaa sashensu zuwa na Hubbi wato mahaifiyar Raihan.. suna mata bayani ta gamsu musamman ma da Raihan yace mata ai zasuje duban lafiyan Unborn ne dna 2dayz yana takurama Mamansa.

adu’an Allah ya kiyaye hanya tai masu duk da tafiyan ba’a son ranta ba, sam bata Ζ™aunar abinda zai nisnata ta da Ι—anta kaman yanda mahaifinsa ya nisanta dashi saboda wata aba sarauta.

****
dakatar da driver yay dayaga sun Ι—auki hanyar masarauta yace ya juya ba can zasu ba gidansu zashi.

juya akalar motar drivern yayi zuwa president house
wata faΙ—uwar gaba Khalid yaji lokacin da suka isko bakin gidan, tangamemen gate Ι—in gidan aka wangale masu suka shiga ciki.

runtse ido Khalid yay yana mai murza karan hancinsa ,ji yake inama baizo ba saboda tinawa da korar karen da Abie yay masa, ya jingina kansa da kujera yana mai jin raΙ—aΙ—i da zugi acikin zuciyarsa.

juyi yake da kansa kamin ya yanke shawaran komawa kawai dan sam bai cancanci zama cikin mutanen da suka Ζ™isa ba akan gaskiyarsa.

haushin kowa da komi yake, umarni yabama driver daya juya ya maidasa airpot dan ayanzu zai koma saudia, Ι—ayar zuciyarsa ta tinatar dashi idan ka tafi Angel kuma fa?

ido ya buΙ—a da sauri zuciyarsa na harbawa, can kuma Ι—ayan zuciyar tasa tace masa kenan ka mance da komi ya sameka itace maΖ™usidi harta walaΖ™antar da kai a bainar jama’a.

ya dafe kansa da Ζ™irjinsa, ya rasa asalin zafin da yake ji cikin zuciyarsa, SO ko kuma ƘIYAYYA,kansa dake neman sarawa yana mai jin kaman zai faΙ—o ya dafe, a hankali murya a sanyaye yake cewan,why angel,miyasa kika aita hakan akaina bayan kin san ni mai tsananin sonki ne?

umarni ya bama driver Ι—in daya juya kawai, yay alΖ™aawarin mantawa da ita gaba Ι—aya a rayuwarsa, driver na tada motar saiga Abie da sauri ya fito domin kuwa ayanzu ya amsa kira daga Mami cewan Aayan yazo kuma tasan da wuya in yazo ya isko inda suke saboda yanayin daya taho ba kyau.

security yasa dasu dakatar masa da motar, da Ι—an gudunsa ya Ζ™arasa inda motar take, buΙ—ewa yay farinciki duk ya isheshi yau gashi ga Ι—ansa duk da komi ya faru nasa laifinne.

ciki ya shiga ya Ι—ago Khalid dake daga kishingiΙ—e wanda duk abinda ke wakana yana ji sai dai yay shiru dan baiko Ζ™aunar buΙ—e ido yaga wannan gidan.

jin daΙ—i duka ya rufe Abie, muryarsa harna rawa yace, “Aayan wuldi

kibiyar Ζ™aunar mahaifinsa ta soki zuciyarsa, yana cike da kewarsa sai dai kuma yana fushi dashi.

Abie ya kamasa suka fito a motar, tallafar fuskarsa yay yace, “Aayan ka buΙ—e idanunka ka kalleni, shekara shida bama tare yau kaga gani amma bazaka kallemi ba”

sma Ζ™in buΙ—e ido Khalid yay sai dayaji muryan Abie ya sauya kaman zai kuka sannan ya buΙ—a idanunsa ya zubesu a Ζ™asa still dai yaΖ™i kallon Abie.Abie yace dashi, “nasan har yanzu kana baΖ™in ciki da abinda ya farune shiyasa, amma karka damu asiri ya riga ya tonu domin yanzu haka ita baiwar data maka Ζ™azafi tana tsare zamu walaΖ™antata kamar yanda ta…..”

Abie bai Ζ™arasa ba Khalid ya damΖ™i kafaΙ—arsa cikin tsawa yace, “tana inaaaa”?

shiru Abie yay yana dubansa da mamaki saboda abinda ya masa.
cikin wata tsawar Khalid ya sake ce masa “ina tambayarka tana inaaa”

“Aayan ni kake ma tsawa, koba komi fa ni mahaifinka ne”

sai a sannan ya saisaita fushinsa ya Ι—ago ya duba Abie, Allah sarki rayuwa harya Ζ™ara tsufa dan furfura sose ta fito masa, wani sabon tausayi da Ζ™aunar mahaifin nasa ne ya shigeshi, fashewa yay da kuka ya kaima Abie runguma yana roΖ™on yafiyarsa.

“nizan roΖ™i yafiyarka bakai ba Aayan, haΖ™iΖ™a duk girman sharri gaskia sai tayi halinta wataran, yanzu gashi nida kakanka muna danasanin abinda muka aikata na yanke hukunci acikin fushi”

hannu yasa ya sharema Abie hawayen daya zubo masa yace, “ya mahaifina ina so ka manta komi domin duk abinda ya faru a baya ya wuce, bakuyi laifi ba domin irin wannan hukuncin ya cancanceni sai dai laifin ku Ι—aya da kuka yanke hukunci batare da bincike ba”

“hakane Aayan amma duk da hakan ka yafe mani kaji masoyina… insha’Allahu kaman yanda mai martaba yace yau za’a yankema yarinyar hukuncin don yanzu haka ana fada an taru gaba Ι—aya ,jiran farkawarta kawai ake wanda nan da minti 30 allurar dake tasiri ajikinta zata barta”

ya zaro ido yana kallon Abbie kamin ya maida idonsa kan diamond wristwatch Ι—in dake hannunsa.

saura mintina 28 ya rage,Abie ya matsar daga kusa dashi ya ture driver ya shiga ya tada mota. datse haΖ™oransa kawai yake yana mai jin kaman ya tashi sama saboda nisan dake tsakani zuwa masarauta.

yankar motoci kawai yake, banda securities Ι—in dake biye dashi da Ζ΄an sanda zasu iya kamashi saboda ya saΙ“a Ζ™a’idan tuΖ™i.

tabbas wani abu ya sami Angel bazai Ζ™yale kowa ba, mugun gudun da yake a minti ashirin ya iso Ζ™ofar masarautar, bai jira da an wangame masa Ζ™ofa ba ya fito da sauri ya faΙ—a gidan da gudu.
kasancewar Abie yayo waya ya sanar tini dogarai suka bi bayansa, kai tsaye fada ya faΙ—a, wata supa yaja ya tsaya lokacin daya shiga ciki, numfarfashin dake fita daga jikinsa kowa na iyaji.

hango Raihana dake kwance kan carpet dake shimfiΙ—e Ζ™asa yasanya ya Ζ™arasa wurin da sauri, zaro ido yayi duba da yanda ya ganta da uban tabbuna ajiki da dukkan alamu ta jibgu da duka.

Ι—agowa yay ya dubi dubban al’ummar dake cikin fadar, tini jijiyoyin jikinsa suka bayyana tamkar zasu fito waje idonsa ko launin daya sauya baza’a kirashi da ja ko kore ba sai buΙ—a hanci yake yana fitar da zazzafan numfashi.

leΙ“ensa ya cije ya daki Ζ™asa wanda saida wurin ya amsa gaba Ι—aya…cikin Ι“acin rai mai martaba ya miΖ™e tsaye yace, “kaiii”

kansa na Ζ™asa bai Ι—ago ba dan bin tabbunayen jikin Raihana yake da kallo yana Ζ™irgesu, tabbas babu wanda zai hanashi yima wanda yay ma Angel Ι“alliΙ“alli a duk sassan jikinsa.

“Khaleed Bin Mourad”
Mai martaba ya kira sunan nasa muryarsa Ι—auke da Ι“acin rai.

bai amsa ba kum abai Ι—ago ba yasa hannu ya sunkuci Raihana, miΖ™ewa yay da ita yaΖ™i Ι—ago ya kalla inda mai martaba ma yake.

cike da jin haushin kowa na wurin ya juya yay hanyar fita ,yasa Ζ™afa a Ζ™ofa ya dkaata da fitar tare da faΙ—in, “idan har wani abu ya sameta ,to bazan bar kowa ba, zan tada ta’addancin da aka sami salamarsa shekaru biyar da suka wuce”

dagama faΙ—in haka ya fice, bai bari an tuΖ™asa ba dan yana ganin Ι“ata masa lokaci za’ayi.

yana tuΖ™i yana dubanta yana kiran sunanta ,”Angel open your eyes plsss, dan Allah karki ce mani wani abin ya sameki ,ki farka gani gareki, wlh na maki alΖ™awarin babu wanda zan bari acikinsu “cikin ruΙ—ewa da tashin hankali yake maganar yana faman girgiza fuskarta, Ζ™iris ya rage yay accident saboda sakin stearing da yay ya taΙ“a artery Ι—inta yaji ko tana motsawa amma sai yaji shiru. +

Ζ™ara ya Ζ™wala tare da Ζ™ara kiran sunan nata, “Angellll ” ya fashe da kuka yana damΖ™e da hannunta

duk nisan Alkhalil hospital amma cikin kaΙ—an Ι—in lokaci ya isa, ragaraga yay da motarsa saboda bai tsaya jiran an wani buΙ—e masa gate ba banka motar kawai yay kaman a film.

ko kashe motan baiba ya fito ya Ι—auketa yay cikin asibitin da ita sai kiran sunanta yake ba Ζ™aΖ™Ζ™autawa.





Post a Comment for "YAREEMA KHALEED CHAPTER 2"