WANENE SHI CHAPTER 1 WANENE SHI CHAPTER 1 Nanne! nanne! nanne!!…ki tashi nace koh?” Yarinyar da aka kira da nanne ta motsa sannan ta cigaba da baccinta, “Zaki bude ido ko sai na tashe ki da ruwa…” Inna ta fada tana dad’a girgizata, jin haka yasa ta zumb’ura baki sannan ta mike tana murza ido ta cikin dogon gashin kanta daya hargitse ya rufe fuskarta. “Ki tashi ki wanke ido ki fita tun kan salisun ya tafi, kin san tun jiya muka yi haka dake.” Nanne ta dago ta kalli agogon dake kafe a dakin, k’arfe takwas da kwata na safe, gabadaya baccin da tayi bayan sallar asuba ma bai kai fi na awa biyu ba. Kwata-kwata ta manta sunyi da inna cewar yau zata je da safe ta gayawa salisu irin audugar da zai d’ebo mata a gonar baffansu wajen daza’a fitar da auduga yau kafin masu siyen kamfani su d’ebe masu kyan ciki, wai da ita zata yi sak’ar mayafan da amare zasu yafa ranar wankan amarya (Hakan wata al’adarsu ce ta wata kabila daga nijer) “Allah inna da kin san gajiyar da na kwanta da ita da kin hakura wani daga cikin su yaya umar …