TSANANI CHAPTER 8

TSANANI CHAPTER 8
TSANANI CHAPTER 8 Bayan tafiyar su Baba da kaɗan, ‘ya’yan Malam Jibo suka riƙa shigowa dakina sahu-sahu suna tsokanata, haka na kasance a daki babu damar na fita tsakar gida sai uwar gidan ta riƙa yada min da magana, ko nayi niyyar ramawa sai na fasa sbd duk abinda aka min mahaifina ne ya fara zubar min da mutunci don haka ko me suka faɗa bana ganin laifinsu. + Bayan na dawo ɗaki komawa nayi na kwanta sbd jirin da ke dibana, ina kwanciya na tashi sbd kwanciyar naji ba daɗi, duk na takura ina ta fama ciwon da ke jikina, don haka na fara ƙoƙarin tashi zaune amma na kasa, duba jikina na shiga yi sai naga duk jini ya bata min kayana, ina so na tashi na canja wani amma na kasa, kukana ne ya ƙara tsananta, addu’ar Allah ya duba halin da nake ciki ya kawo min mafita na riƙa yi A ranar wuni nayi ban fito ba ko alwala a daki na riƙa yi sbd bana son na fita a faɗa min abinda zai sosa min raina, a zaune na riƙa sallah sbd zazzaɓi mai tsanani da ya kamani, shi kuwa malam Jibo tunda ya fita ban sake…