TSANANI. CHAPTER 7 TSANANI CHAPTER 7 Bayan na gama karatun Alkur’ani kishingida nayi sbd ina so na ɗan huta amma duk da haka bakina bai bar ambaton Allah ba, tashi nayi na karkade katifata na shimfida zanin gadon da innah ta aiko min da shi. Sallama malam Jibo yayi tare da dage labulen dakina, ina ganin shi na tashi zaune tare da amsa masa sallamar, tsaye yake a bakin kofa bai karaso inda nake ba ya fara min magana “Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida” haɗe fuska nayi ban amsa masa ba, murmushi yayi “wai sai yaushe xaki daina fushi da ni Sa’adatu na zaci komai ya wuce a tsakanin mu, dan Allah ki saki ranki ki min murmushi ko zan ji daɗi, wai kin ci abinci ma kuwa naga tsakanin jiya da yau kin ɗan rame, ko sai naxo na dura miki ne” duk maganar da yake min idanuna na ƙasa ban dago na kalle shi ba ballantana na bashi amsa. Sako kafarsa yayi cikin dakin ya cigaba da yi min magana. “Sa’adatu ina so ki dafa min ruwan wanka xan ɗan watsa a jikina ko xan ji dadi, yau kin san a dakinki xan kwana ina so na…