TSANANI CHAPTER 6

TSANANI CHAPTER 6
TSANANI CHAPTER 6 Tun bayan fitowar Izuddeen daga police station bai sake samun sukuni ba, kullum cikin damuwa da tunanin halin da Sa’adatunsa take ciki yake yi, yana ji a ransa baxai taɓa barinta ba har abada ko ana muzuru ana shaho, gaba ɗaya ya daina fita harkokinsa komai nasa ya tsaya cak saboda tunani, kullum cikin kuka yake duk ya rame yayi baƙi, ko abinci baya ci sai idan mama ta bashi shi ma sai ta rarrashe shi sannan zai ci. + Yau ma kamar kullum kwanon abincin yasa a gabansa, hannunsa rike yake da wayarsa ya kurawa wayar ido yana hawaye, hoton Sa’adatu yake kallo zuciyarsa sai radadi take masa, ji yake kamar yaje ya shaqi Baban Sa’adatu ya fito masa da ita, saboda idan akwai abinda yake da muradin gani yanzu bai wuce Sa’adatunsa ba. Sallamar mama ce ta katse masa dogon tunanin da ya tafi, tare take da abokinsa Kabir karasowa daf da shi tayi fuskarta a bayyane da damuwa. “Wato har yanzu dai kana nan kana wannan tunanin naka ko Izuddeen, yaushe xaka cire yarinyar nan a ranka ne, …