TSANANI CHAPTER 16 TSANANI CHAPTER 16 Cikin Wata irin rikicewa da d’imaucewa tare da rawar baki nake faɗin sunansa “Izuddeen dina ashe baka manta da ni ba, dama ina da rabon yin tozali da kyakkyawar fuskar ka, gaskiya ka cika ɗan halak, ka cika masoyi na gaskiya, ban taba ganin mutum irinka ba wanda ya san girman mai son shi tsakani da Allah ba” ina maganar ina murza idanuwana don na ƙara tabbatar wa da kaina shi ne ko kuma mafarki nake yi. Idanuna ne suka fara zubar da hawaye. Cikin Wata sassanyar murya yace “ki ƙara so mana Sa’adatuna, kin dade da xama jinin jikina soyayyar ki da kaunar ki a xuciyata take, baxa ta taɓa gushewa ba, kuma baxan taɓa mantawa da ke ba har karshen rayuwata, kin so ni tun lokacin da ba ni da komai, kinga kuwa babu abinda xai sa na guje ki har abada” Yana faɗin haka ya buɗe min hannayen sa cikin sassarfa na ƙarasa wajansa hannu yasa ya rungume ni ban san lokacin da wani irin kuka ya sake ‘kwace min ba. Cikin sigar rarrashi yace “Sorry my life ba kuka zaki yi ba, godewa Allah ya kamata…