Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

TSANANI CHAPTER 16

TSANANI







CHAPTER 16




Cikin Wata irin rikicewa da d’imaucewa tare da rawar baki nake faΙ—in sunansa
“Izuddeen dina ashe baka manta da ni ba, dama ina da rabon yin tozali da kyakkyawar fuskar ka, gaskiya ka cika Ι—an halak, ka cika masoyi na gaskiya, ban taba ganin mutum irinka ba wanda ya san girman mai son shi tsakani da Allah ba”

ina maganar ina murza idanuwana don na Ζ™ara tabbatar wa da kaina shi ne ko kuma mafarki nake yi.
Idanuna ne suka fara zubar da hawaye.
Cikin Wata sassanyar murya yace
“ki Ζ™ara so mana Sa’adatuna, kin dade da xama jinin jikina soyayyar ki da kaunar ki a xuciyata take, baxa ta taΙ“a gushewa ba, kuma baxan taΙ“a mantawa da ke ba har karshen rayuwata, kin so ni tun lokacin da ba ni da komai, kinga kuwa babu abinda xai sa na guje ki har abada”

Yana faΙ—in haka ya buΙ—e min hannayen sa cikin sassarfa na Ζ™arasa wajansa hannu yasa ya rungume ni ban san lokacin da wani irin kuka ya sake ‘kwace min ba.
Cikin sigar rarrashi yace
“Sorry my life ba kuka zaki yi ba, godewa Allah ya kamata kiyi da ya sake haΙ—a fuskokin mu a matsayin masoya kuma ma’aurata nan bada dadewa ba, ban taΙ“a tsammanin xan sake ganinki ba a rayuwata duk a xatona an rabu mu, sai kuma ga shi mahalicci sarkin jin kai ya sake haΙ—a fuskokin mu”

Nan ya shiga rarrashina cikin wani irin salo mai wuyar fassarawa.

Mu’allim yana gefe wani irin tuΖ™uΖ™in baΖ™in ciki yaji ya rufe shi, nan da nan yaji garin yana jujjuya masa, baΖ™in kishi ya turnuke zuciyar sa, wai Sa’adatunsa ce wacce ya bawa dukkan kauna da soyayyah ita ce a rungume jikin wani da namiji me hakan ke nufi? wane ne wannan da har ya fi shi matsayi? me yake takama da shi da har ya janye hankalinta da wuri??

Tafin da Ruqayyah tayi ne ya fara dawo wa da su hankalin su, ita ma tayi ne sbd yadda taga masoyan sun shagala da junansu sun manta da kowa a gurin.

Cikin matsananciyar kunya Sa’adatu ta fara zamewa daga jikin izuddeen, amma shi gogan naka yaΖ™i sakinta, cikin muryan da take Ζ™ara dulmiyar da ita cikin kaunar sa taji yana cewa.

“Pls my life kada ki bari a Ζ™ara raba mu a karo na biyu, baxan iya rayuwa babu ke ba idan aka kuma raba mu mutuwa xan yi”

Cikin shagwaba
na narkar da idanu nace masa.
“Pls my man ka cika ni haka baka ganin mutane sai kallon mu suke”

Matse min hannu yayi yana cewa “Ruqayyah ce bakuwata bana jin kunyar kowa indai a kanki ne”

Cike da shagwaba na sake maimaita masa.
“baka ganin akwai bako a wajen”
Da sauri ya cika ni a dai-dai lokacin Mu’allim ya d’ago kansa, da yake masa barazanar fashewa cike da mamaki, idanunsa sun yi jawur sbd baΖ™in kishin da ya addabi zuciyarsa.

“Wai yau shi Sa’adatu take kira da baΖ™o me hakan ke nufi”

Izuddeen ne ya katse masa tunanin da yake yi, yana tuhumar Ruqayyah wane irin baΖ™o Sa’adatu tayi da zata fito a haka da wannan kayan masu kyau a jikinta.

Ɗan turo baki nayi tare da cewa
“Ni fa ba kwalliya nayi ba malamina ne yazo ya duba ni sbd ba ni da lafiya”

Ruqayyah da ke gefena kallona tayi tana rufe baki, sbd dariyar da take shirin kwace mata, saurin cewa tayi.
“Eh malamin su ne yaxo dubata”Ok” izuddeen ya faΙ—a yana mi’kawa mu’allim hannu ba don ya san muhimmancin gaisuwa a musulunci ba, da bazai miΖ™a masa hannun su gaisa ba, wani kallo ya bi Sa’adatu da shi, wata muguwar tsanarta ce ta kama shi ji yake kamar ya kashe kansa sbd baΖ™in ciki.
Neman hanyar fita daga soran ya fara yi sbd xuciyarsa baxa ta iya jure kallon abinda ta gani ba yanxu.

Yana tafiya yana haΙ—a hanya sbd takaici, ji yake ya tsani duniya gaba Ι—aya da kyar yake jan kafa a haka har yaje gida.

Cikin soron muka koma muka fara hirar mu ta masoya cike da farin ciki sai a lokacin na lura da mu’allim baya nan, ban wani damu zuciyata ba sbd na san dama ya xama dole yaji haushi, nima tasirin da soyyyar izuddeen tayi min ne yasa ni mantawa da kowa.

Har cikin gida ya shiga ya gaida Adda ita tayi mamakin ganinsa a wajena duk da arxiki mai yawa da ya samu bai sa ya manta da soyayyata ba, wrapper din yan dari biyar ya miΖ™a mata, sannan ya Ζ™ara jaddada mata soyyyar da yake min ya faΙ—a mata nan bada dadewa ba yake sa ran aurena.

Sai da muka yi sallar magariba muka yi sallama, tare da Rukayya suka tafi ya sauketa a gidansu shi kuma ya wuce wajen Innah.

A soro suka ci karo da salim, cikin sakin fuska ya miΖ™a masa hannu suka gaisa, sa shi yayi ya kira masa innah, ba tare da bata lokaci ba ta fito.

Ita ma tayi matuΖ™ar mamakin ganin izuddeen, da yadda Allah yayi masa arziki dare Ι—aya, nan ma ya Ζ™ara jaddada mata cewar yana son Sa’adatunsa kuma baxai dade ba xai aureta, kuΙ—aΙ—e masu yawa ya dakko ya bata.

A Hanyar fitar shi kofar gida ya haΙ—u da Baba cike da ladabi ya tsugunna ya gaida shi, da farko bai gane shi ba sai da ya sake haska shi da touch light, sai a nan yaga izuddeen ne, cikin sakin fuska yace.

“Tashi tashi Ι—an nan, kaine yau a gidan namu”

Mamaki izuddeen yayi sbd irin karΙ“ar da mahaifin Sa’adatu yayi masa.
Jan hannunsa yayi zuwa soro na biyu

“Ai bai kamata ka tsaya a nan ba ka shigo daga ciki kai ai Ι—an gida ne, dakin Innah Salamatu yaje ya dakko masa shimfida tare da xaunar da shi a kanta”

Cike da ladabi ya sake gaida shi, a lokacin ya sake faΙ—a masa shi fa yana nan a kan bakansa na kaunar Sa’adatu.

Cikin sakin fuska mahaifin Sa’adatu ya dube shi.

“Ya za a yi kace kana son baxawara izuddeen ga yan mata nan kala-kala a gidan nan sai ka zaba ka darje, ka kyale wannan yarinyar ba yarinyar kirki bace yanzu haka ma na koreta daga gidana”

Shafa fuskarsa yayi
“Na riga na san komai Baba, Yanxu ma daga wajenta nake, duk na san ,wannan labarin idan da hali ni dai ina sonta a haka”

Ransa bai masa daΙ—i ba haka dai ya amsa masa da “shikenan tunda ka kafe a kan abinda kake so na kyale ka, amma Hausawa sun ce wanda yaΖ™i ji ba yaΖ™i gani ba”

Shi ma dubu Ι—ari ya bashi, nan da nan ya sake gigicewa kamar xai goya izuddeen sbd murna har bakin motar shi ya raka shi sannan ya dawo.

Jikinsa na rawa ya shiga dakin Innah Salamatu ya faΙ—a mata zuwan izuddeen da irin abin arzikin da yayi masa, nan fa baΖ™in cikinta ya motsa taji kamar ta mutu sbd haushi.

“Yanxu shi Wannan mayen sai da ya Ζ™ara dawowa dole ne yana saurayi sai ya auri baxawara ga yan mata nan kala-kala yaxo ya zaba amma ya nacewa wannan guxumar, yarinyar nan ba haka ta kyale shi ba wlh asiri tayi masa, ya xama dole naje gidan su yaron nan na Ζ™ara ankarar da su”

Da sauri mahaifin Sa’adatu ya dakatar da ita.
“Bana son mugun hali da sharri, kinga Allah xai rufawa yarinya asiri shi ne xaki je ki kashe mata aure, to wlh idan kika je a bakin naki auren”

Yana gama faΙ—a ya fita ya kyale ta.

Banda ciwo babu abinda zuciyarta ke yi sbd takaicin za a saketa.Kwance nake kan cinyar Adda tana min tsifa, ta lura da ni yau ina cikin farin ciki sosai, don gaba Ι—aya bakina yaΖ™i rufuwa ina tuna yadda na kasance da izuddeen dina, da irin farin cikin da ya bani, Ι—aga kaina nayi ina kallonta
“Adda kin san kuwa abinda nake tunani?”
Kallona tayi tare da bayar da hankalinta gare ni
“Sai kin faΙ—a Sa’adatu”

Gyara kwanciya nayi, cike da damuwa nace.
“Ban san ta inda xan fara miki ba Adda, xuciyata tana cikin damuwa sosai, kaina ya kulle na rasa me xan ce miki ki fahimci irin yadda nake ji a xuciyata, tunanin abinda xan faΙ—awa doctor nake yi, kin ga yana sona ya gama bani amanar xuciyarsa da soyyyar sa gare ni, yanxu da wane ido xan dube shi na faΙ—a masa cewa izuddeen ya dawo”

Mayar da numfashi tayi tare da ajiye kibiyar da ke hannunta.
“Wlh nima tunanin da nake yi kenan Sa’adatu tunda nake ban taΙ“a tunanin izuddeen xai dawo gare ki ba, duk a tunanina yayi miki nisa tunda Allah ya arxuta shi ya kai ga babban mataki ya xama wani a rayuwa, amma sai ya bani mamaki ya dawo, da na san haka xata faru da ban bari doctor yayi xurfi a sonki ba, ina tausayin ki Sa’adatu domin kin haΙ—awa kanki kulli mai wuyar warwarewa, ina fatan dai tun farkon haΙ—uwar ku kin bashi labarin rayuwar ki gaba Ι—aya, don a nan ne kaΙ—ai xai san da xaman izuddeen?”

Tashi nayi daga kwanciyar da nake
“Iya labarin malam Jibo kawai ya sani Adda”

Girgiza kai tayi
“Kin yi kuskure da kin sani kin faΙ—a masa, amma nasan baxa ki samu matsala da shi ba insha Allah, sbd doctor mutum ne mai fahimta da zurfin hankali, sai dai babu daΙ—i mutum ya rabu da abinda yake so”

Wayana naji yana Ζ™ara, Adda ta sakar min kaina na shiga daki don amsa kiran, Ι—an halak yaΖ™i ambato na faΙ—a tare da daga wayar, number doctor na gani.

Cikin siririyar murya nayi masa sallama.

Marairaice wa yayi
“Babyna shi ne yau ko ki kira mijinki ki ji ya ya kwana, kin san xuciyata bata iya jure rashin ki amma yau gaba Ι—aya kin manta da ni”

Ajiyar xuciya na saki cike da marairaice wa nace
“Kayi hakuri doctorna, ba mantawa nayi da kai ba kuma kana raina nima tun daxu nake tunaninka, tunda naji shiru na san ka wuce asibiti, tunda jiya ka faΙ—a min kana da tarin aiyuka, bana so na kiraka ne na hana ka yin aikinka, amma xuciyata ta faΙ—a min kana cikin koshin lafiya”

Shafa fuskarsa yayi gami da mirgina kanshi gefe guda har ga Allah yana jin daΙ—in kalamanta, zuciyar shi tana faΙ—a masa yadda zai samu kulawa matuΖ™ar ya mallake ta.

Cikin rikitacciyar muryar shi yace
“To babyna na gode kuma na gamsu da kalaman ki, idan shirya ki fito gani nan a kofar gida ina jiranki”

To nace tare da mi’kewa, daure gashina nayi na shiga gyara fuskata, hijabina na sanya sannan na fita.

Ina sako kaina kofar gida da fuskarsa na fara yin tozali, yana sakar min wani kasalallen murmushi, a da idan yayi min wannan murmushin ba Ζ™aramin narkar min da xuciyata yake yi ba, amma yau sai ban ji komai ba, a sanyaye na Ζ™arasa wajen shi.

Sannu da zuwa na masa d’ago fuskata yayi yana kallona, “

“Sa’adah ya nake ganin damuwa a cikin idanuwanki?? Ko yau ma nayi laifi ne na tsugunna na kama kunne na batawa sarauniya ranta”

” uhmm” nace ina gyara tsayuwata

“Ba komai ai kai autan maza ne baka laifi” na Ζ™arasa maganar ina kawar da fuskata.Nuna min hanya yayi
“Bisimillah mu shiga daga ciki babyna”
A hankali na ja kafa nayi gaba shi kuma ya biyo ni a baya.

Gaisawa muka Ζ™ara yi, zaulayata ya fara yi.

“Ni fa kwanan nan wani kyau kike yi, tun kafin a fara maganar auren mu har kin fara kyallin amarci ko dai kin kosa ne?”

Narai-Narai nayi da ido kamar xan yi kuka. Ban iya bashi amsa ba sbd abinda ya tsaya min a wuyana.

Cike da tashin hankali ya sake dubana tare da sakkowa daga shimfidar da nayi masa.
“Me yake damun ki Sa’adatu ko wani abin aka yi miki, ki faΙ—a min damuwar ki ni mijinki ne, ni nafi cancanta nayi miki maganin matsalar ki”

Idanuwana ne suka Ζ™ara ciccikowa na fara magana a hankali.
“Daman daman wata magana nake so mu yi ni da kai, amma ina so ka yiwa maganar kyakkyawar fahimta, dan Allah kada ta xama sanadin samun matsala ta da kai”

Cike da kulawa ta dube ni
“Ina jin ki Sa’adatu ki fadi komai ni naki ne Insha Allah baxa ki samu matsala da ni ba”

Saita nutsuwata nayi tare da sunkuyar da kaina sbd baxan iya hada ido da shi ba.

“Allah ya sani ina Kaunar ka kuma ina kwadayin kyawawan halayenka masu kyau, amma duk abinda zan faΙ—a maka ina so kai min kyakkyawar fahimta, kai mutum ne mai hakuri da kawaici tare Ι—aukan kaddara mai kyau da mara kyau” nan na dora masa da tarihin rayuwar mu da izuddeen tun daga daga farko haΙ—uwar mu har Ζ™arshe.

Sake kallon shi nayi
“Dan Allah kayi hakuri ka bar masa ni ya aure ni, ya faΙ—a min idan ya rasa ni mutuwa xai yi”

Na Ζ™arasa maganar tare da zamowa daga kan kujerar da nake zaune, zuba gwiwoyina nayi a Ζ™asa ina d’aga masa hannu.

Kayi hakuri kada ka rika min kallon wacce ta yaudare ka, wlh ban yaudare ka ba doctorna, na ceci ran izuddeen ne sbd bak’ar wuyar da ya sha a kaina har kulle shi Babana yayi, idan ya rasa ni xai iya rasa rayuwarsa”

Kafin na karasa maganar kuka mai tsanani ya kama ni, duk maganar nan da nake idanunsa na kaina yana min kallo mai cike da tausayawa, sai da na samu nutsuwa na sake kallon sa.

“Ina neman alfarma a gurin ka dan Allah ka auri yar uwata Ruqayyah, zata xama sanyin idaniyarka, xata riΖ™e maka yayanka amana, zata baka kulawa fiye da ni, kayi min wannan alfarmar dan Allah
doctor, bana son mu yi asararka a cikin dangin mu don kai mutum ne na gari”

Hannayen sa ya saka ya d’ago ni daga durkusan da nayi, ya matso daf da ni numfashin sa na dukan fuskata, cikin wani salo ya fara min magana.

“Naji dukkan abinda kika fada min sa’ar mata, na kuma yarda da ke na san baxa ki yaudare ni ba, baxa ki cuce ni ba, kuma baxa kiyi abinda xaki wulakanta soyayyar da nayi miki ba, kin nuna min kauna kin so ni iya so, kin so abinda na haifa, yanzu ma na san lalura da kaddara ke neman raba ni da ke, amma ki sani har abada baxan iya cire soyayyar ki a xuciyata ba, sai dai xan yi hakuri na barki ki auri wanda kike so sbd ina sonki, soyayyar ki tasa ni son duk abinda kike so, ni mai ceton rai ne ba mai kashe rai ba, don haka na amince na yarda ki so izuddeen ko don mu ceto rayuwar shi daga halaka, sbd shi masoyinki ne na gaskiya ya can-canci ki so shi har karshen rayuwar ki, sbd ya nuna miki kauna tun lokacin da baki san kanki ba har zuwa yanxu bai manta da ke ba, na yarda har ga Allah ki aure shi”Ban san lokacin da wani farin ciki ya lullube ni ba, dubansa nayi ina murmushin farin ciki
“Na gode doctor gaskiya ka cika masoyi na gaskiya ka cika Ι—an halak, ka amsa sunanka na namijin duniya, yadda ka tseratar da zuciyar wani daga halaka kaima Allah ya kula da kai, Allah ya duba bayanka”

Amsa min yayi da ameen, sake jefo min tambaya yayi.

“Amma kina nufin ita Rukayyan, ba tada wata matsala xata so ni, kuma ba tada wanda take so, sbd bana so na shiga tsakanin masoya?”

Ya faΙ—a tare da marairaicewa cikin wani salo mai ban tausayi.

A sanyaye nace
“Rukayya ba tada matsala yadda halina yake haka nata yake, shi yasa abotar mu tayi ‘karko har muka kawo wannan lokacin, sannan iyayenta sun fi nawa hali ta fini kyau ta fini ilimi, ina tabbatar da cewa ba tada kowa a halin yanzu don haka ka tsarkake xuciyarka ka faΙ—a son Rukayya Ina tabbatar maka da cewa baxa ka samu matsala ba”

Daga min hannu yayi tare da dakatar da ni
“Wannan ni duk ba damuwata bace Sa’adatu nafi buΖ™atar kyan hali fiye da kyan fuska, amma na san baxa ki min xaben tumun dare ba, Allah ya tabbatar mana da alkhairi”

Amsawa nayi da ameen

Sake duba na yayi
“Kin faΙ—awa Rukayya wannan tunani da kika yi?”

A sanyaye nace
“Ban faΙ—a mata ba ina so dama naji ta bakinka ne kafin nayi mata magana, na san baxa tayi min musu ba”

Murmushin Ζ™arfin hali yayi
“To shikenan bani numberta yau xamu yi magana kuma baxan baki kunya ba Sa’adatu”

A hankali na fara laluben number Rukayya na bashi, cike da girmamawa muka yi sallama ya tafi.

A hankali ya yi wa motar shi key ya bar kofar gidansu. Jikinsa na rawa yake driving din ya rasa me ke yi masa daΙ—i a duniya, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un kawai yake nanata wa a fili, tare da addu’ar Allah ya bashi nutsuwa da juriya a kan wannan babbar jarrabawar da ya shiga.
Yana xuwa gidansa yayi parking fitowa yayi, masu yi masa hidima sai sannu da zuwa suke masa amma ya share su sbd baya cikin hayyacinsa. BanΙ—aki ya shiga ya sakarwa kansa ruwa sai da ya fara dai-daita nutsuwar sa sannan ya daura alwala ya fito.

Sallah yayi raka’a biyu ta neman zabin Allah tare da addu’ar Allah yasa zabin da Sa’adatunsa tayi masa ya xama alkhairi a rayuwarsa, don yasan baxa ta bashi abu mara kyau ba.

Tabbas yaji xafi da ciwon rabuwa da ita, amma babu yadda zai yi izuddeen ya fi shi cancanta da ya auri Sa’adatu, kuma a yadda alamu suka nuna xai riketa tsakani da Allah, tunda gashi ya yi kuΙ—i amma bai manta da ita ba, kuma shi ne wanda ya fara sonta tun farko, idan har ya raba su bai yi musu adalci ba.

Tashi yayi ya kwanta a kan gado yana ta juyi yana tuna irin madarar soyayyar da ya kwasa a wajen Sa’adatu, amma yau mai rabawa ta raba su, rintse idonsa yayi tare da matse pillow a kirjinsa. Yana ta ambaton Allah.Ko da na koma gida sai da na faΙ—awa Adda yadda muka yi da doctor, tayi farin ciki sosai da karΙ“ar Rukayya da yayi, ita kanta sai da ta jinina masa sbd namijin Ζ™oΖ™arin da yayi wajen karΙ“ar Ζ™addara, komawa daki nayi na cire hijabin da ke jikina, mayar da kallona nayi ga Hanan da ke faman sharar bacci bisa katifata, tausayin yarinyar ne ya kama ni, na so a ce ni xan maye mata gurbin mahaifiyarta amma Ζ™addara ta riga fata, matsawa nayi ina cigaba da kallonta tare da sumbatar goshinta, har cikin zuciyata ina jin kaunar Hanan naso a ce a kafaduna xata cigaba da kasancewa.

Yau tsabar tashin hankali doctor ya mance da yar diyar tasa gaba Ι—aya, don ko tambayar lafiyata bai yi ba.

Tsakar gida na fito don na sha iska kasancewar yau ana xafi, sallamar yaro naji a hankalina na d’ago ina kallon shi.

A ladabce yace
“Wai ina Sa’adatu?”
Gaba Ι—aya na bayar da hankalina gare shi, tare da cewa “gani”

Wata takarda ya miko min
“Wani ne a kofar gida yace na kawo miki”
Gabana ne ya fadi sbd ina jin tsoro ko malam Jibo ne ya aiko shi, da har na yanke shawarar baxan karba ba, sai kuma na miΖ™a masa hannu ya bani.
Cikin kosawa da ganin abinda ke jikin takardar na shiga budewa don ganin abinda ke ciki, sunan mu’allim na gani a zane jikin takardar.

A kasalance nace
“Na gode kace ina gaida shi”
Tsintar kaina nayi cikin fargaba da tashin hankali, nasan tabbas ba abin arxiki mu’allim ya rubuta min ba, muddin na karanta wasikar ba lallai ne na iya bacci ba.

Tashi nayi na shiga daki, sai da na dai-daita a kan katifata sannan na fara buΙ—ewa.

*_Assalamu alaikum masoyiyata a da amma kuma sanadin kukana a yanxu, na shiga d’inbin damuwa tun bayan rabuwata da ke, amma ke na san ba haka abin yake ba a cikin zuciyar ki, tunda masu kuΙ—i sun hure miki kunne har sun kai ga raba ki da masoyinki na gaskiya, tun bayan da kika kyale ni kika sa na shiga zargin kaina ko ina da wani mugun hali ne da har ya sanya ki guduna. Dan Allah ki taimake ni kada ki sa zuciyata ta koma kallon so a matsayin wani abu mara daraja, abin gujewa da rashin can-canta ga rayuwa ta zahiri. linzamin farin-cikina na a hannuwanki a halin yanzu. Ina son ki, kuma xan cigaba da sonki har abada duk da cewa ke kin guje ni, amma ko kaΙ—an ban ji tsanar ki a xuciyata ba, ina miki fatan alkhairi ke da sabon mijinki Allah ya bar ku tare, nima ina so ki ci-gaba da taya ni addu’a Allah ya zaba min mace ta gari, wacce baxa ta guje ni ba a daidai lokacin da nake da tsananin bukatar ta_*

*_Bissalam_*

Ban san lokacin da na kwanta ba tausayin mu’allim ya kama ni, tabbas ina son shi amma ba kamar yadda nake son izuddeen ba shi ma kanshi ya sani, amma halin da na jefa shi ne babban abinda yake damuna a yanzu.

Haka na kwana cikin damuwa, wayar da muka kwana muna yi da izuddeen ne ya Ι—ebe min kewa.

***********

Kwance nake kan sallayata ina karatun Alkur’ani tare da addu’ar Allah ya tabbatar mana da alkhairi tare da zaman lafiya a aurena da izuddeen, ‘karar da wayata tayi ne yasa ni saurin kai hannuna wajen dakko ta, murmushi na sauke a kan wayar saboda ganin sunan masoyina a jikin screen din.

A hankali na d’aga tare da karata a kunnena.
“Barka da asuba my man”

Ɗan murmushi yayi tare da tashi daga kwanciyar da yayi.
“Barkanki mu wife, Ina fatan kin tashi lafiya kuma babu abinda yake damunki”

Kara saita wayar nayi cikin shagwaba nace.
“Babu abinda ke damuna illa rashinka”

Ɗan siririn murmushi ya saki “Indai ni ne yanzu ma sai nazo wajenki, kin san burin kowane masoyi ne ganin murmushi a fuskar wadda yake kauna, ko da a ce wani ya saka ki cikin damuwa, ni kuma zan yi iya kokarina wajen bayyanar da murmushi a saman fuskarki”

Murmushin farin ciki nayi
“Ina godia my man, wannan kalma na dade ina jinta a wajenka, kuma na amince da ita Ι—ari bisa Ι—ari”

Ƙasa yayi da murya cikin sigar rad’a yace.
“Da gaske my wife?”

Cikin wani salo nace.
“Kwarai kuwa, shi yasa na baka sarautar xuciyata domin ka shimfida mulki a cikinta yadda kake so, a kullum burina ka zamo nawa, ta yadda zamu kasance tare tamkar jini da tsoka. kaine jarumi guda Ι—aya tilo da zuciyata ta aminta da shi. Ina son ka, fiye da yadda nake son kaina”

Cikin tsantsar farin ciki ya saki wani mutum
“Yanzu wannan matsayin duk ni kaΙ—ai Sa’adatu?”

Kamar yana ganina na girgixa kai alamar eh.

Cikin sigar rarrashi ya fara min Magana.
“Kiyi hakuri Sa’adatu yau baxan samu zuwa ba kamar yadda nayi miki alΖ™awari, sbd xan je na gano ginin gidan mu inda xamu shimfida rayuwa da soyayya mai kyau tare da ke da yayanmu”

A shagwabe nace
“Ni Allah nafi buΖ™atar ganinka, kawai kaxo idan ba haka ba kuma nayi fushi da kai”

Rarrashina ya shiga yi har sai da na hakura ya tafi ganin ginin namu.

Da misalin Ζ™arfe hudu na yamma na shirya tare da tambayar Adda don xuwa waje Rukayya, kama hanyar tafiya gidan su nayi, hannuna janye da Hanan.

Sallama nayi muka shiga cikin dakin su cikin farin ciki ta karΙ“e mu tambayarta nayi ina ummansu sanar min da tayi bata nan taje unguwa.

Abinci ta zubo mana muna cikin ci ta dube ni.
“Tunda izuddeen ya dawo wani kyau kike yi wato hankali ya kwanta ko?”
Ta Ζ™arasa maganar tana murmushi tare da ajiye cokalin abincin.

Cike da zaulaya nace
“Ke kuwa ba dole na canja ba mai bani farin ciki ya dawo”

Miko min hannu tayi muka tafa, sai a lokacin idanunta suka kai kan Hanan.

“Wannan babyn kuma a ina kika samo ta na dai san ba yar Adda bace, don ba tada yarinya kamar wannan”

Rausayar da kaina nayi
“Yar ki ce fa, ina fatan ma rainon yarinyar nan da kulawarta su dawo hannunki idan kika auri mahaifinta”

Cikin rashin fahimtar abinda nake nufi ta dube ni.
“Ban fahimce ki ba Sa’adatu, me kike nufi da hakan?

Nan na bata labarin nagartar doctor, da kyawun halinsa da irin yadda ya kula da ni tun xuwana asibitinsa.

Mayar da ajiyar zuciya tayi.
“Na gode Sa’adatu na san baxa ki haΙ—a ni da mutumin da kika san ba shi da nagarta ba, amma kina ganin zai karbi soyayyata?”

Girgiza kai nayi
“Kwarai kuwa don shi ne ma ya nemi na samo masa macen aure da kaina, na faΙ—a masa nagartar ki kuma ya yaba da komai naki, kada ki damu ke dai kiyi addu’a kawai kawata, Allah ya tabbatar da alkhairi”

Da ameen ta amsa min, hira muka cigaba da yi muna maganar ne doctor ya kirata, da zaulayarta ya fara har sai da ta saki jiki da shi suka fara sabawa, ita kanta ta yaba da halin shi da yadda yake da saukin kai da barkwanci, a lokacin take fada masa muna tare, karbar wayar yayi muka yi magana inda ya faΙ—a min yau da daddare xai xo ya dauki Hanan.Da ummansu ta dawo muka faΙ—a mata halin da ake ciki, ita ma tayi farin ciki sosai tare da addu’ar Allah ya dai-daita su.

Sai wajen isha muka koma gida, a kofar gida naci karo da shi har yaxo yana jirana, gaisawa muka yi sannan na shiga gida na dakko masa kayanta, da abubuwan da Adda ta bata.

Da kyar muka rabu da yarinyar muna ta kukan shakuwa.

Post a Comment for "TSANANI CHAPTER 16"