TSANANI CHAPTER 10

TSANANI CHAPTER 10
TSANANI CHAPTER 10 A hankali ta xare sakatar kafin ta bude har sun ‘kagu sun hankado kyauran saura kaɗan ta fadi a kasa, cikin kasalalliyar murya take tambayar innah salamatu “Haba Hajiya ya xaki turo min kofa da karfi haka, idan kin yi hakuri xan bude miki, yanxu da ina da rabon wahala karya ni xa kiyi saura kiris na fadi” Wani kallon wulakanci ta watsa mata “to menene dan kin karye, ai da xaki karye din ma haka nafi so, da xamu fi samun sassauci a kan masifar da kike kokarin jefa mu a ciki” Cike da mamaki ta dube su “Ban fahimci abinda kike son faɗa ba wani abin ne ya faru, ni dai na san ban yiwa kowa komai ba?” Matsowa tayi kusa da ita “Au tambayata ma kike?? Ki fada mana inda malam yake kafin mu fara canja miki halittarki, don na fahimci sai mun fara gyara miki xama a gidan nan xaki daga mana kafa Da jin wannan kalaman nata sai taji ta warware daga dukkan kasalar da take ji, murmushi tayi gami da kallonta ido cikin ido. “wannan ne kuma baki isa ba, ba ki da wannan ikon, dakata kiji sala…