SAWUN BARAWO CHAPTER 11 KARSHEE

SAWUN BARAWO CHAPTER 11 KARSHEE
SAWUN BARAWO CHAPTER 11 THEND KARSHE “Ramlah! Keh Ramlah bude idonki ki kalleni nan” muryar Hajiya ta doki kunnuwan ta, a hankali ta rika bude idanuwan nata da hawaye yakasa daina fitowa daga cikin su, har yanzu kunnuwanta basu daina jiyo mata muryar Safwan ba lokacin da yake datse igiyar aurenta dake kanshi. + “Ya salam!Hajiya,Innah, Nabilah, ku taimakeni, meyasa Ya Safwan zai mani haka? Meyasa zasu rik’a wasa da rayuwata kamar wata yar tsana? Uhmm Hajiya ki gaya mani, menene yasa mutanen nan biyu bazasu bar zuciyata ta huta haka nan ba? Sabida Allah Innah menai masu har haka da bazasu barni inyi farin ciki ba? Ki duba kigani Nabila daga wannan sai wannan, dame suke so inji? Nagaji, nagaji, Hajia, wallahi nagaji da yawa.” 2 Ta ida zancen da wani irn matsanancin kuka, ba shakka duk mai sauraren ta a lokacin dole ne ma tabashi tausayi, dole neh ka tausaya mata, hakika rayuwa nakan yin tangal tangal da ita, amma sai dai? Hakuri d yanda rayuwa tazo wa bawa shine kawai mafita. 1 Cikin lallashi…