WATA SHARI'A CHAPTER 21

WATA SHARI'A CHAPTER 21
WATA SHARI’A CHAPTER 21 Hayaniya kotun ta d’auka baki d’aya sai cece_kuce akeyi, Alhaji Abu Abu kuwa mutuwar zaune yayi ji yake tamkar a mafarki ne, Barr. Sa’eed kuwa sai k’arema Gentle kallo yake yana mai tsananin jin haushinta, inda ace batayi maganar ba da yasan ta hanyar da zaibi dan lalata waccan maganar, amma kuma duka ta b’ata zancen. Bubbuga guduma alk’ali yayi da k’arfi sannan kowa yayi shiru, ‘Salmah Abubakar kinsan ko me kike fad’i kuwa?”. Cikin hawaye Gentle ta d’aga kanta tace ‘Tabbas a duk bayanan da YB yayi babu k’ari ko kad’an a ciki, Da gaske ni nasa ayiwa Ummimah fyad’e, ni nasa aka satomin k’annenta ‘yan biyu duk dan in guma mata, Ganin kamar hakan bai dameta ba yasa da nasa aka kashe k’anwarta d’aya daga cikin wanda aka sato, Na samu labarin halin da suke ciki kuma na had’a baki da wanda yakeda gidan hayarsu na maka masa kud’i yaje ya koresu, A dalilin haka babanta ya had’iyi zuciya ya rasu, Naso insa a saki Amrah amma kuma koda na samu labarin cewa wasu Indiyawa zas…