WATA SHARI'A CHAPTER 19

WATA SHARI'A CHAPTER 19
WATA SHARI’A CHAPTER 19 Lambar wayar dake jiki Umar ya danna a wayarsa, ya latsa kira yayi take kuwa ta fara k’ara, Har ta tsinke ba’a d’aga ba hakan yasa ya sake kira, Saida ya kira sau uku sannan aka d’auka, “Hello-salamun alaikum” Umar ya furya a hankali bayan ya saka wayara hands free. Daga can d’aya b’angaren aka amsa da “Wa‘alaikumussalam, sunana Sarki Manu, how may I help you?”, “Alhamdulillah, Sulaiman Usman Saraki, is that your real name?“, “of course thats my real name” ya bashi amsa. “Sunana Barr. Umar Mohd Bashir, cikakken lawyer mai zaman kanshi, idan ba zaka damu ba akwai wata magana da nake so muyi da kai Dafe gaba Sarki Manu yayi bayan ya sauke ajiyar zuciya, “Wace irin magana ce?” Ya tambayeshi. ” so idan babu damuwa mu had’u dakai face-to-face muyi maganar”. Shiru yayi kafin yace “Babu damuwa ina zamu had’u d’in?”, “Ina kake ganin yafl? Wurinka ko kuma zakazo gidana?”, “Ka bani address d’inka ni zanzo ko zuwa anjima ne insha Allahu”, “Nagode kuwa abokina, yanzu zan text…