WATA SHARI’A CHAPTER 18 Tunda suka bar kotun su Brr. Sa’eed ke cuku cukun yanda zasuyi su buga takardar da zata tabbatarwa kotu cewa asibnin Dr. Khalid ce shi kad’ai, Da sa‘a kuwa suka samu aka bugata yanda babu wanda zaiga takardar yace ta k‘arya ce, ni kaima nayi,matuk’ar mamakin wannan takardar, saboda tamafi ta kirkin tsaruwa, babu wanda zai ganta yace ta k’arya ce sai ni da nasan kan zancen. Ana sauran kwana uku su koma kotu ne Sultana suka fita ita da Ummimah da Umar zasu koma police station maganar batar Safiyya, Sun ‘tsaya a daidai roundabout suna jiran traffic light ya basu hanya, wani irin hold up ne sosai wanda basuyi mamakinshi ba saboda duk ranar Friday ana samun irin hold up aduk fad’in garin Katsina. Wasu matasa ne su biyu akan mashin sunabtukinsu cike da natsuwa har suka kutso ta daidai inda su Sultana suke, Kallon mamaki ta bisu dashi kam tace “Wai nikam honey ka gane wancan masu mashin d’in?”, D’aga kanshi yayi tare da sauke gilashi ya kashe AC, ya kallesu sosai yace “…