WATA SHARI'A CHAPTER 17 WATA SHARI’A CHAPTER 17 Mamaki fal a fuskar Umar yake kallon mutanen dake cikin matrix d’in, A hankali mutumin ya fito bayan ya kashe motar, Murmushi yayi tare da mik’a masa hannu yace “Assalamu alaikum”, Shima hannun ya mik’a masa amma kuma bai amsa sallamar ba saidai kallo kawai da yake binsa dashi. “Ka daina mamaki Barr. Umar, nine d’in dai Dr. Rafiq wanda kukayi dashi zaije kotu ya bayar da shaida sai kuma wani dalili ya hana, amma yau a shirye yake daya bayarda shaidar duk abunda ya sani kuma tsakaninshi da Allah”. Murmushi Umar yayi yace “ina ka shiga Dr. Rafiq? Aimu munyi zaton ko kaima sun siyeka da kud’i ne, tuni aka yanke hukunci amma mun d’aukaka k’ara, yanzu haka shirin tafiya kotun muke saboda yaune zamu fara zama”. Muryar mace yajiyo tace “Ba za’a tab‘a siye Rafiqu da kud’i ba d’an nan, shari’ar nan tana ransa kawai dai an nuna anfl k’arfinsa ne…” Umman Raftq ta kwashe duk abunda ya faru ta fad’awa Umar, Sultana ma tana tsaye tana saurarensu wani irin dad’i taji a ranta, l…