WATA SHARI'A CHAPTER 16 WATA SHARI’A CHAPTER 16 Washe gari. Tunda sassafe Haydar ya tashi daga barci, ido ya bud’e bayan ya lalaubi Safiyya bai jita ba, Daga can gefe ya hangi Hafsa tanata sharar bacci abunda cikin kwanciyar hankali. Zaune ya tashijikinshi zafi rau yana fad’in “Aunt Shifiyya” amma shiru baijita ba dan a tunaninshi k0 tana toilet ne, Sauka yayi daga kan gadon ya fara knocking toilet amma har yanzu baiji alamarta ba. Kuka ya fasa da k’arfl tare da barin d’akin ya doshi kitchen ko tana can amma Ina,a b’uruntun Sultana ta jiyo tana had’a break fast saboda sammako zasuyi a kotu. K’arar kukanshi data jiyo yasa tayi saurin fitowa ta tareshi dan dama a tsarinta bata barin yaro ya shiga kitchen saboda tana amfani da gas da electric, “Haydar wats your problem?” Ta tambayeshi bayan ta rungumeshi. “Momy banga Aunty shafiyya ba tunda na tashi” ya fad’a cikin kuka. “Kajika Haydar da wata magana, yo ina zataje kuwa? May be ko ta shiga toilet ne yasa baka ganta ba, kayi shiru ka daina kukan nan ba nisa tayi ba…