TSANGAYAR MATI CHAPTER 11

TSANGAYAR MATI CHAPTER 11
TSANGAYAR MATI CHAPTER 11 Abulle tayi k’asa k’asa da murya. “Makarin shine a jika wandon kwarto a shanye.” Nene ta zabura tayi zaman ‘yan bori wanda yayi daidai da sullusowar tusa mai kara. Abule ta toshe hancinta, a hankali Nene ta numfasa har da lumshe idanu don ba karamin sassauci ta samu a cikinta ba. ”Na shiga uku, yanzu ina zan ga kwar… Af! Faduwa ta zo daidai da zama ai Abule, yo bana manta ashe muna dasu a kurkusa ba? Ga Basharin Shafa?” Abule wacce itama shaff ta mance da batun Jikan Lamidon ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin zuciyarta wasai, babban abinda ya sanyamata damuwa da lamarin ba komai bane sai na tsoron kada ya kasance Nene bata warke ba ta tonamata asiri mutan gari su zageta. Ta daki cinyarta tana mai washe rinannun hakoranta. “Kai Allah mungode maka. ai ni dinma kaf tunanina bai je nan ba. Kojiya da daddare ya haurawa Kulu Gurguwa.” Suka saki shewa don Nene har ta hango warakarta a saukake. “Kai Allah Ya karowa Bashari ilimin kwartanci, wannan ai gaba ta kaini. A…