RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 3

RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 3
RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 3 Aishalle ta saki ihun wahala, Musbahu ya chapko karime ya hadata da bango, yaja hannun Aishalle yayi waje da ita. karime na kwance kasa amma bakinta be daina furta zagih da batanci ga Musbahu ba, Wurin Hajjo ya kaita, tayi saurin lullube jlkinta da zani. yace hajjo ga yarinya nan dan Allah aba ta abinci kuma tayi wanka a bata kaya, Hajjo tace toh Yaya, Yace Aishalle ki saki jikin ki, ba abunda xai sameki anan, ga qanwata nan zata kula dake kinjl? Aishalle ta gyada fuska,musbahu ya saketa ya fice,Hajjo tace zonan kinji qanwata? Aishalle ta matsa kusa da hajjo tana dari Dari don ta tsorata da alamarin karime, Jan hannunta tayi ta kaita har daki, ta zubo mata faten doya ta bata, sosai taci abincm nan. Sannan ta bata kaya ta sata tai wanka. Kwanan Aishalle 5, ta sake da hajjo da yaranta, ita ke kula da Hafiz auta, wanka da wanki, haka kuma zata tasa su Hassan gaba tayi ta basu tatsunniya, kullum Musbahu Sai ya shigo yaga ya take, Duk zaton karime Aishalle bata gi…