WATA SHARI'A CHAPTER 2

WATA SHARI'A CHAPTER 2
WATA SHARI’A CHAPTER 2 Washe gari da sassafe Sultana ta tashi Umar suka fara shirin zuwa aiki, Bayan sun gama shiri ta yima Hafsa da Haydar wanka sannan ta shirya Hafsa cikin Uniform din School dinsu,  Sauran pepper soup din jiya tayi warming nashi sannan ta soya mata Irish da kwai ta saka a launch box d’inta.  “Wow! Kinyi kyau baby na, barin snapping naki” Hafsa uwar iyayi kuwa aka wani yi style na daukar hoto, Saida Sultana ta dauketa hoto kala biyar sannan tace “to ya isa haka, barinyi Feeding haydar shima tunda dai kinga anan zan tafi in barshi”, “0k Momy ki diba a nawa ki bashi” Hafsa ta fada cike da soyayyar kaninta, “Ahh Hafsa ai na d’ibar masa nashi daban, gashi kin gani” Sultana ta fad’a tare da nunawa Hafsa sauran Irish da kwan data ragewa Haydar.  Saida suka gama tas Umar ya fito cikin suite d’inshi black and white,  Yayi matukar yin kyau kamar a saceshi a gudu,  “Yadai Madam? Hope kun gama saboda inada aiki da yawa a Office yau, kuma kema din nasan ba zaki rasa ba”.  “I think bani…