NAYI GUDUN GARA CHAPTER 31

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 31
NAYI GUDUN GARA CHAPTER 31 Yarinyar mai suna hansatu Iaila ta kalla tace to zaki ringa yi mana sharar falon nan da goge shi kullum safe da yamma, sannan bangarena zaki na min wanke -wanke da sharar falona da sauran wasu abubuwa da gaba zance ki nayi. Bansaniba ko kishiyata zata sanya ki to dai dukyana ciki.” “To,” yarinyar ta fada tana rarraba idanuwa. Karamin Dakin da ke gefen kitchen din ladifa aka shigarda ita ta ajje kayanta ta zauna tai tagumi. Ta dade a zaune tana ta kalle-kalle karshe ta tashi ta tura bandakin da taga kofa agefe tai Alwala ta fito tayi sallah. Nan bacci ya dauketa awajen. Dakin dame aikin take ladifa ta shiga ta taradda hansatun na bacci,sai ta tasheta ta tashi da sauri tana rarraba ido, ladifa tace “kinci abinci kuwa? .” Ta yi mata alamar Aa, Sai ta koma ta zubo mata ta zauna za taci ita kuma ta fita. Bata dade da cinye abincin ba ladifa ta dawo tace taje tai wanka, nan kuwa taje tayi wanda tana fitowa ta sanya kayanta ta kuma maida hijabin jikinta. Iaila ce ta …