NAYI GUDUN GARA CHAPTER 30

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 30
NAYI GUDUN GARA  CHAPTER 30 Wani hamdala tai a zuayarta a yayinda taga sun faka a harabar filin gidan nasu,juyawa tayi ta kalleshi wanda shi hankalinsa naga kokarin kashe motar, fita tai ta shiga takawa a  hankali ta shiga falon. Kamshi ne ya doketa sai tai murmushi tana son gidanta.  Babu kowa afalon sai fanka da ke aiki. zama tai akan kujera alokacin ramadan ya shigo da jakun-kunanta ya ajje, sai ta mike za taja, yace “tsaya shiga kawai na shigo dasu, kina da karamin Clkin zaki d’au wannan babbar jakar. sai tai murmushi ta bude shashinta ta shiga ganin yayi dan kura ya sanya ta ajje mayafinta a gefe, ta shiga kokarin gyara wajen bayan  ramadan ya gama kai mata jakar.  Ladifa bata san da dawowarsu ba har saida ramadan ya hau saman ya gansu suna shakar bacci ita da fuad,juyawa yayi zai fita, sai karar kofa ta tada ladifa, da sauri ta bude ido  “zauji” ta ambata sai ya tsaya ya juyo yace “ashe ba bacci kike ba?!’ Sai tai murmushi ta ce “wallahi shi nake yi, karar buga kofar da kai ce ta tashe…