MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 38

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 38
MUSAYAR ZUCIYA  CHAPTER 38 Tunda Sadeeq ya koma gida be sanar da kowa zancen da suka yi da lNdo ba kasan cewar baya son duk wani abinda zaija ayi mata gori akai ba. Gidan kanwarsa Hauwa yaje suka yi magana hakan yasa duk abinda ya siyo ita yake kaiwa ga shirin gidan da ake yi mata wanda zata koma.  Cikin kwana biyu ya gama had’awa washe gari ana sauran kwana biyu lNdo ta dawo yasa aka kai hawwa gidan su INdon takai kayan. Sosai aka dinga murna ana yiwa INdo barkar cewar mijinta ya fitar da ita kunya da kayan da babu wacce aka taba yiwa kowacce mace irinsa a kauyan. Shiri tayi sosai ciki da waje Rukayya ta kawo mata kayan INdo ta sake yin wani sassanyan kyau sam bata bari a sauya mata akidar da take da ita dan yanzu a kauyan akwai ‘yan matan da suke kwaikwayar shigarta da kwalliyarta har yafa mayafi ma.  “Gaskiya Fateema kina da hakuri, ki duba ki gani a cikin shekara d’aya da auranku kishiyarki tayi zaman gidaje gashi yanzu mijinku d’aya amma zata koma wannan uban gidan na alfarma ke kina…