TUN KAFIN AURE COMPLETE TUN KAFIN AURE?1 Motsi kadan sai ta daga labule ko zata ga shigowarsa amma shiru. Dawowa tayi falo ta shimfida abin sallah don tana gudun kada ya dawo ya shige daki bata sani ba. Tayi raka’a takwas duk biyu tayi sallama ta sake tashi ta daga leka wajen, wannan karon ruwa akeyi kamar da bakin kwarya tayi ajiyar zuciya…daya daga cikin lokutan amsar addua kenan sai ta koma kan abin sallar ta fara addua. Tana yi tana kuka bukatar tata bata wuce Allah Ya shirya mata Junaid ba. Jin alamar shigowar mota gidan yasa tayi saurin kashe fitilar falon ta koma gefe ta tsaya. Bata dade ba taji ya bude kofar a hankali ya shigo da sanda kamar wani barawo. Mamaki ne ya kamata yadda yake da key din kofar bayan ta rufe ta sannan ta kwashe duka keys din. Yana kokarin hawa sama ne yaji ta haske masa fuska da touch light din wayarta….wane dan kut….maganar ce ta makale a bakinsa ganinta a tsaye fuskar nan kamar bata taba dariya ba. Duk da a buge yake amma sai da gabansa ya fadi. Saukowa yayi yace Mommy ina wun…