NAYI GUDUN GARA CHAPTER 29

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 29
NAYI GUDUN GARA  CHAPTER 29 Abban laila na dawowa da daddare, babu bata lokaci umma taje ta sanar mai da batun cikin laila, ta kara da cewar yaje ya sanar da mijinta. Sai daya gama jinta, ya ce “lkon Allah Allah ya sauketa lafiya, amma ba zanje ba, har sai sanda yaron yazo da kansa dan ya maida ta  “Haba alhaji ya za a ce hakan? ai hannunka bai rubewa ka yanke ka yar, saboda Allah haka zaka zuba ido, muna kallon yarinya baka ganin dukyanda ta koma, dan Allah kai hakuri ka neme shi.”  “Zancen kike so saratu kome ya faru da yarinyar nan itace sila, ba wai ban damu da komawarta bane, so nake sai taji zaman gidan nan ya daMeta arai.”  “To Alhaji na nawa? kowacce mace indai an daura mata aure ai tafi san ta ganta agidanta.”  Bai kara cewa komai ba,ya karkade riga ya mike, cikin takaici umma tace “to anjima zamu asibiti a duba ta.”Yace “Sai kun dawo.”  Fuska atamke umma ta fito ta zauna adakinta tai tagumi, lamarin ya fara isarta gashi har an fara yadawa a unguwa ai auren laila ya mutu. Wasu ma ha…