NAYI GUDUN GARA CHAPTER 28
NAYI GUDUN GARA CHAPTER 28 Hannuwanta ta sanya ta dafe gefen cikinta da taji ya kame, sai ta runtse ido tana salati, ta dade a yanayin, sannan ya lafa, sai ta tashi. Alokacin ramadan ya shigo gida Idonsa ya sauka a kanta. Da kewa tai tayi mai sannu da zuwa,shi kuma ya zauna a gefenta yace “na ganki ba daidai ba baby ya dai ko haihuwar ce?.” Murmushi tai tace “ba najin fa komai, kawai dai dan ciwo marata keyi.“ Da kinji dai babu dadi ki sanar min baby, dan kinga likita yace da kin fara nakuda akaiki asibiti, saboda ba a son zama agida idan ka fara jin hakan, kinji me yace dai. ” To tace mai to tana runtse ido tashi yayi ya haye sama. Ita kuma taci gaba da runtse ido, a hankali ta mike dan ta hau saman, sai taji mararta ta wani amsa cikin ya wani irin juyawa, sai ta danyi kara ta dafa kujera, gadan-gadan ta fara jin ciwo.Wanda a daidai lokacin ramadan kuma saukowa, ganin halin da ta ke ciki, ya ta karaso aguje, yace “kawai muje asibiti.” Bata musa ba, ya dauko mata hijab suka tafi. Koda …