NAYI GUDUN GARA CHAPTER 27

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 27
NAYI GUDUN GARA  CHAPTER 27 Har karfe uku laila na daki tana kuka, wanda har saida taji kanta na ciwo, umma kuwa k0  ajikinta, saida taga abin ya wuce munsherin, sannan ta leka dakin tace “Aduk lokacin da  mutum ba zai ji maganar manyansa ba yana tare da wahala, tun dazu nake miki maganar  sallah da abinci, amma kinyi burus ko, irin wannan gaddamar ne fa yajanyo miki halin da  kike ciki. To wannan ne maganar k’arshe tsakanina da ke, kar Allah ya sanya ki tashi kuka babu wata tsiyar da zai miki.”  Tana gama maganarta Fice. Sai alokacin laila ta mike tana tafiya a hankali, dan jinta take yi wata iri, ga zuciyarta data kasa sukuni da abubuwan da suka faru, wanda ramadan yayi mata, alwala ta je tayi ta koma tai sallah taci abinci, wanda bata tashi daga wurin ba, ta dau wayarta ta kuma latsa wayar ramadan, lokacin yana farfajiyar gidansa ta baya yana karanta jarida, wayar tana ta ring ya duba ya gani ya tabbatar laila ce sai yajuyar da kai.  Alokacin kuma ladifa ta tawo da turtstsen cikinta dauke …