NAYI GUDUN GARA CHAPTER 26
NAYI GUDUN GARA CHAPTER 26 Da safe, a darare laila ta tsaya gefen ramadan tana zuba mai abinci, cikin sauri ta ke komai, saboda azalzalarta da ya shiga yi, saboda za su je wani meeting da shugabansu ya wakilta suje abuja, sabuwar lamba ke ta kiranshi amma bai da lokacin d’auka, dan ba kasafai ya ke d’aukar lambar da bai sani ba. K’arfe goma ya kammala yayi musu sallama ya tafi, sai alokacin laila tai hamdala sabida ganin yanda ya ke cikin yanayi na fada. Ga kuma mafarkin da tai daren jiya wanda ke damalmala zuciyarta. Dan tai mafarki wai ramadan ya saketa. Shi’isa tunda ta tashi ta keyin dari -d’ari. A sanyaye ta koma shashinta. Shida abokin aikinsa suna tafiya suna hira. Inda suke ta kwararar gudu amota. Wayarsace ta shiga kuka, alamartana bukatar a kawo mata dauki. lambar dake faman damunsa da kira ne ya gani, tsaki ramadan yayi ya yace “wallahi bana son damuwa,” sai ya d’aga kan yayi magana ta katse .Sai ga sakon text msg nan ya shiga wayarsa da sauri ya duba aka ce; “ka kunna data …