NAYI GUDUN GARA CHAPTER 25

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 25
NAYI GUDUN GARA  CHAPTER 25 Yana zaune akan kujera su kuma kowacce na gefe ta Ciki na Clki. Kallonsu ya yi d’aya bayan d’aya daga bisani yaja numfashi yace. “Ladifa.”  Ta amsa, ya kalli laila itama ta amsa. “Ina son ku fahimceni sosai da kunnen basira, na tara ku ne akan abunuwan da suke wakana a gidan nan, ba naso, ba sai mini dad’i, yanzu ku dan Allah ba abin kunya bane a taradda ku kuna fada kamaryara?.”  Kallonsu ya kuma yi, ya kalli lad’ifa kanta a sunkuye, laila kuma na girgiza k’afa.  “Wallahi karna kara ganin wata taimin fada agidan nan, ba ruwan wata da wata,ku zauna lafiya a mutunta kuma, na sanki laila kece ummul aba’isin komai, saboda kowa na san halinsa, to ki shiga hankalinki, dan zan sabar muku duk ranan dana kara ganin anyi fada  da wani makamin.”  Tabe baki laila tai ta ce “ai daman nasan ni ba kaunata kake ba, shi,isa za ka ce nice silar komai.” ‘  “Shut up!bana son irin halin nan. Duk wacce kiga gani to dan ina sonta na aurota, dan haka maganar ma wani so ki ajje shi gefe, …