NAYI GUDUN GARA CHAPTER 24

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 24
NAYI GUDUN GARA  CHAPTER 24 Gun mahaifiyarta kawai take son zuwa don ta dade ba taje ba, dan sai tace tafi wata uku, ga al’amuran dake wakana sun cunkushe mata arai, har yanzu abinda ramadan yayi mata bai dusashe ba, don har yanzu taki sakar mai fuska duk raragefen da yake.  Karfe goman dare tayi dakinsa, dan ta tambayeshi zuwa gida gobe, ta shiga yana ganinta ya danyi murmushi dan aganinsa ko hakuri tazo ba shi.  Hijabinta ta cire ta kwanta agefensa, sai ta dan juyo da kanta tace “baban baby dama ina son gaya maka gobe ina son zuwa gidan mu.” “Me za kije kiyi?.” “Dan zanje gidanmu har sai an tambayeni abinda zanyi?.” “Ba zaki ba.” Wani irin tashi tai da sauri wanda har saida taji cikinta ya amsa tace “akanme ?.” “Ra’ayina ne ki bari next week kyaje?!‘  Tafarfasa taji zuciyarta nayi,dan haka kawai takejin haushinsa adan kwana biyun nan, tun abinda ya faru wanda sukai mata shi da laila. Haryau abinna damunta.. “Amma zauji….” Sai ya dago ya kalleta “ladifa ban sanki da musu ba.” Tsam! Ta tas…