NAYI GUDUN GARA CHAPTER 23
NAYI GUDUN GARA CHAPTER 23 Abubuwa goma da ashirin ne suka taru suka cakudewa laila, ta damu iya damuwa. Ba irin hanyar da ba tabi ba wajen ta shawo kan ramadan amma kamar dad’a ingiza shi take.Ga damuwar da ta sanya aranta dan ramadan yace zai kara aure. Misalin karfe sha-biyu na rana, tana kwance ad’akinta idonta biyu, amma ba bacci ta ke ba, wayarta ta dauka ta kalla wacce ta sanyawa password saboda tsaro, sai ta ajje ta gefe ta runtse ido. Ta d’au karamar wayarta wacce ta maida layinta cikinta ta bugawa ramadan, lokacin yana tsaka da aiki,Yana d’auka sai ta sanya mishi kuka .Cike da mamaki cikin dakakkiyar murya ya ce “ke meye ne?.” “Haba ramadan,yanzu dan nai maka lefi kalilan kake hukuntani, karka manta fa, murmushinka yakan sanya zuciyata tai sanyi, amma kayi dif da shi ko alamarsa na daina gani a fuskarka dan Allah kai hakuri.” “Kinga laila, idan ke awajenki abinda kikai karami ne to ni awajena babban lefi ne.” Ya fada tare da kashe wayar. Bin wayar tai da kallo. Sai ta bi gado…