NAYI GUDUN GARA CHAPTER 22

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 22
NAYI GUDUN GARA  CHAPTER22 Hankalinta kwance tai ficewarta, sam! ba ta gano cewar gatse ramadan yayi mata ba. Musamman da taje ta hadu da ‘yan uwa da abokan arzik’i. Wata mata mai saida k’ananan kayan mata kala -kala, ta bajewa laila tana ta siya, hakan ma ya dada sata shan takewa. Ta yiwa matar nan ciniki sosai, ba ita ta tashi komawa gida ba sai wajen shida. Faka motarsa yayi ya shiga gidan, shiru falon babu kowa.Direct saman ya yi dan bai tunanin cewa laila ta fita ba, saboda shi ya san gatse ya yi mata. Dakinsa ya shige, wanka yayo saboda zafin da yakeji. Sannan ya fito ya shiga wajen ladifa baby. Tana zaune da kofi a hannunta tana shan kwalaba da nono, sanye take da riga da siket mai siririn hannu. Mikewa tai tace “sannu da zuwa zauji na, ban san ka shigo ba.“  Hadata yayi da jikinsa ya ce “ke da ba lafiya ba maman baby, acici kullum bakinki na motsi.” Dariya ta sanya “wallahi nima bansan mai ya sa nake yawan ci ba, tunda  babynka ya fara girma, nama d’anji dama-dama fa.”  Cikin jin d…