NAYI GUDUN GARA CHAPTER 20
NAYI GUDUN GARA CHAPTER 20 Yana zaune gefen adaidaita sahunsa, ya zuro kafafuwansa waje. Ta daya bangaren ga abokinsa kamilu suna hira. Kamllu ya kalleshi “Wai ni kuwa Murabus ina labarin laila kuwa?!‘ “Hmmm’ yace wallahi Ina nan ina kirga kwanakin aurenta, na shirya tsaf Wallahi idan ban kashe auren nan ba. to sai na dagula mata zaman auren nan, akanta sai da nai sati daya a bayan kanta, ai yarinyar nan ta yaudareni wallahi,yau da ina dayayan banki, babu abinda zai sanya na damu dan tayi aure ko taci kudina, amma kaga kullum hajiya zancenta kenan Allah ya kara da aka yaudarenka tace min tunda ban sharar masallaci ba, ai ga shi nayi ta kasuwa. Daniya kamilu ya iasa “ho ho ho, wallahi ina gaya maka kai hakuri, nuhu duk ya gayan komai, kawai Allah ne ya tsara hakan, ni dai shawarata kai hakuri, shi hakuri arayuwa yana da rana, ka barshi, baka san gaba wacce irin mata Allah zai baka ba. Inaji maka tsoron ka sanya kanka a matsala” “Kai billahil azim! sai na nuna mata cewar nima dan zamani …