NAYI GUDUN GARA CHAPTER 19NA
NAYI GUDUN GARA CHAPTER 19 Bayan gama gage man leban, sai ta daga kai ahankali ta kalli mudubin, tai ido hud’u da shi sai yayi murmushi, yajijina kai alamar yayi. Sai ta jingina da bayan kujerar, tana masa wani irin kallo da manyan idonta. Wanda ya kejin wani irin feelings nata na tashi a hankali. Adaidai lokacin laila ta waigo za tai mai magana, tai arba da yanda idonsa ke kallon titi yana kuma kallon mudubi, yana sakin murmushi. Juyawa bayan tai taga ladifa kanta jingine da kujerar tana dan wasa da mayafinta abaki, tana lullumshe mai ido. Anan ta fahimci komai. Cikin fushi ta waigo, karar awarwaronta ya sanya ramadan ya kalleta. Sai ta yasine fuska. “Yanzu abinda kai ya dace kenan ramadan?, dan wulakanci ina gaban mota kai idonka na kan wancen yarinyar, nina zama dodo-rudo kenan ko?.” Afuskance ya kalleta fuska atamke, sai ta danyi tsaki kasa-kasa tace “wallahi ba zan yarda da wannan cin amanar ba, a gaba na! Wallahi dole ta fito daga bayan motar nan, dan bazan Iamunta ba.” Ta fada t…